Abin da ya sa muka buxe kungiyar masu ra’ayin Kwankwasiya – Zainab Buba

Shugabar Mata ta riko ta Kungiyar Masu ra’ayin Kwankwasiya wadda a turance ake kira Kwankwasiya ideology ta kasa reshen Jihar Kaduna Zainab Buba ta ce sun buxe kungiyar ne domin tattara jama’a masu ra’ayin Kwankwasiya a karkashin lema xaya domin cim ma burinsu tun da manufar xaya ce. Zainab Buba ta sanar da hakan ne […]

Abin da ya sa muka buxe kungiyar masu ra’ayin Kwankwasiya – Zainab Buba

Shugabar Mata ta riko ta Kungiyar Masu ra’ayin Kwankwasiya wadda a turance ake kira Kwankwasiya ideology ta kasa reshen Jihar Kaduna Zainab Buba ta ce sun buxe kungiyar ne domin tattara jama’a masu ra’ayin Kwankwasiya a karkashin lema xaya domin cim ma burinsu tun da manufar xaya ce.

Zainab Buba ta sanar da hakan ne a zantawarta da wakilin Aminiya, inda ta ce shirye-shirye sun yi nisa wajen ganin cewa kungiyar ta taimaka wajen yaxa manufar Kwankwasiya a kasa da ma duniya baki xaya.

“Mu ‘yan Kwanwasiya ne, kuma muna alfahari da Kwankwaso domin shi ne jagoran wannan tafiya. Duk wanda ya san Kwankwaso ya san cewa mutum ne mai son jama’a da adalci da son ci gaban al’umma. Kulluma burinsa shi ne ya zai taimaki al’umma da kasa baki xaya.

“Ashe ke nan, duk wani mutumin kirki zai so ya yi mu’amala da wannan bawan Allah tunda ba komai a zuciyarshi sai alheri.

“Wannan ne ya sa muka haxu a waje xaya domin mu yi koyi da shi. Kuma burinmu shi ne duk ’yan siyasar mu su zama masu hali da ra’ayi irin na Kwankwaso, shi ya sa muke kokarin ganin cewa mun faxaxa wannan kungiyar da ayyukanta.

Ta kara da cewa manufofin kungiyar sun haxa da cusa wa mutane ra’ayin taimakon al’umma da son juna, da kuma nuna wa yara masu tasowa cewa duk wanda ya taimaka, shi ma Allah zai taimake shi.

“Manufofin wannan kungiya suna da yawa, amma babban manufar mu ita ce mu cusa wa al’umma halaye na gari, wanda suka haxa da taimakon mutane  da kuma son juna ta yadda ’yan siyasa masu tasowa za su gane cewa lallai idan suna so su yi tasiri a siyasa, dole sai sun yi abun da ya kamata ta hanyar taimakon al’umma ba tare da son kai ba.

“A karshe ina kira ga sauran mutane musamman mata ’yan uwana da su shigo wannan kungiya ta masu ra’ayin Kwankwasiya domin mu amfanar da kanmu da al’ummar mu baki xaya,” inji Zainab Buba.