Abin da ya sa muka fara garkuwa da mutane —Yara

Wadansu kananan yara ’yan kasa da shekara 20 su hudu sun bayyana yadda suka hada wani gungun garkuwa da mutane inda suka sace wani yaro dan shekara shida suka nemi fansar Naira miliyan biyu da rabi. Lamarin yaran ya jefa jama’a a cikin damuwa kwarai da gaske, ganin ba wanda ya kai shekara 20 a […]

Abin da ya sa muka fara garkuwa da mutane —Yara

Wadansu kananan yara ’yan kasa da shekara 20 su hudu sun bayyana yadda suka hada wani gungun garkuwa da mutane inda suka sace wani yaro dan shekara shida suka nemi fansar Naira miliyan biyu da rabi.

Lamarin yaran ya jefa jama’a a cikin damuwa kwarai da gaske, ganin ba wanda ya kai shekara 20 a cikin yaran.

Yaran da suka hada da wani wani saurayi mai shekara 19 da ke zaune a Unguwar Borno kuma dalibi a Kwalejin Shari’a ta AD Rufa’i da ke Misau.

Akwai kuma wani mai shekara 18 shi ma da ke Unguwar Borno da abokinsu mai shekara 19 da ke Unguwar Madina Kwatas sai na karshen mai shekara da ke Unguwar Borno.

Wakilinmu ya ce matasan sun amince da aikata laifin a lokacin da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta gabatar da su ga ‘’yan jarida a farkon wannan mako.

Daya daga cikin samarin ya ce sun saci yaron ne domin su samu kudin da za su bude harkokin kasuwanci ko sana’a, inda ya ce shi burinsa ya bude shagon dinki.

Su ma abokansa uku sun ce burinsu shi ne idan suka samu kudin za su fara yin sana’o’i ne.

Abdulgafar ya ce ya iya dinki kuma ya roki mahaifinsa ya ba shi kudi ko rance ne, amma ya ce ba shi da su.

Saboda haka ne ya shawarci abokansa kan su sace dan makwanbicinsu ko za su samu kudin don su yi jari.

Ya ce, “Mun shirya komai har da inda za mu ajiye yaron,” kuma wanda suka ajiye yaron a gidansu ya yi karya ga mahaifiyarsa cewa yaron, kanen abokinsa ne da aka kwantar da mahaifiyarsa a asibiti.

Amma washegari sai mahaifiyar da hankalinta bai kwanta ba ta sanar da makwabta.

Ya ce ba su samu kudin ba, domin bayan sun daidaita a kan Naira miliyan daya, a ranar da suka yi za su karbi kudin ne aka kama su.

Ya ce sun yi da-na-sanin aikata wannan mugun aiki kuma idan har aka sake ba su dama za su yi rayuwa mai kyau.