Abin da ya sa muka kafa APC akida a Jihar Katsina – Kabir Murja
Alhaji Kabir Abdullahi wanda aka fi sani da Kabir Murja na daya daga cikin ’yan siyasar da suka yi gwagwarmayar adawa da jam’iyyar PDP wadda ta yi shekara 16 tana mulki. A zantawarsa da Aminiya, ya baiyana dalilan da suka sa har suka kafa APC akida a Jihar Katsina. Ka gabatar da kanka ga […]
Alhaji Kabir Abdullahi wanda aka fi sani da Kabir Murja na daya daga cikin ’yan siyasar da suka yi gwagwarmayar adawa da jam’iyyar PDP wadda ta yi shekara 16 tana mulki. A zantawarsa da Aminiya, ya baiyana dalilan da suka sa har suka kafa APC akida a Jihar Katsina.
Ka gabatar da kanka ga masu karatu?
Sunana Kabir Abdullahi wanda aka fi sani da Kabir Murja. Sunan Murja ya samo asali ne daga wajen ’yar uwata wadda ta rike ni kamar uwa a garin Dutsinma. To masu suna Kabir a lokacin muna da yawa a inda nake aiki, amma domin a bambanta mu sai aka rika hadawa da sunanta ana cewa ‘Kabir na wajen Murja’, a haka na zama Kabir Murja.
Me ya sa kake shiga bangare adawa a siyasance?
To abin da ya sa nake shiga jam’iyar adawa shi ne mutun a kullum in ya ga ana tafiya wanda yake ganin ba daidai ba, to zai so ganin cewa an canja wannan al’amari yayin da har zai iya neman abokan da za su taya shi. Shekara 16 ina yin wannan tafiya ta adawa wadda kowa ya san haka. Hatta shi mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taradda ni da adawa a lokacin ina jam’iyar APP a 2003 inda ya zo ya same mu. Koda ya shigo ya same mu muna da tsari tun daga mazabu har zuwa kananan Hukumomi. Ko a yankinsa na Daura ya taras da wadannan tsare-tsare namu a cikin mazabu 11. To a haka muka yi ta tafiya har Allah Ya bamu dama muka kafa gwamnati a Jihar Katsina. Muke da dukan wadannan ’yan majalisu tun daga na jiha har zuwa tarayya. Kazalika muke da sanatoci 3 na jihar sannan kuma ga Shugaban kasa.
Me ka samu a baya a wajen yin adawar?
To duk da cewa a can baya ne na yi adawa, domin yanzu ai jam’iyata ce ke mulki, ka ga ko wannan wani abu ne a gare ni na alfahari.
Amma adawar ta dawo cikin gida kuma?
Ai ita maganar gaskiya daya ce. Matsala ko a gidanka ka ganta za ka fada. Abin da kuma ya sa muka koma gefe daya suna da yawa. Ai a da da jam’iyar PDP muke fada, to amma a yanzu sai ya zamo mun bullo da APC AkIDA wadda take kungiya ce ba jam’iyar siyasa ba a nan Jihar Katsina, amma har gobe muna nan a cikin APC. Amma abin da muke nufi da APC AkIDA shi ne matukar aka yi alkawurra aka kuma saba to an sabawa ita jami’ar APC, sannan kuma yadda ake tafiyar da jam’iyyar muka ga ba daidai bane saboda an ajiye kundin tsarin mulkin ana amfani da hauragiya. To mu abin da muke so shi ne a koma akidar APC ta gaskiya, sannan kuma a koma akidar Buhari wadda yake son taimakon al’umma. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka kafa APC AkIDA a Katsina. Ai ko addininmu na musulunci ya ce idan har muka ga barna to mu gyara ta a aikace ko da baki ko kuma mafi rauni shi ne a yi shiru amma a kyamaci abin. To shi ya sa muke magana da babbar murya muna cewa abi nda ake yi bai yi daidai ba kuma ba shi ne a ka yi alkawari ba.
Me ya sa ba ku dauki matakin sulhu ba?
Idan ka ga ana rigima watakila sulhun cikin gidan ne ya gagara. Lalacewar abu ke sawa a fito har waje ana rigima domin kawo gyara. Bai yiwuwa a ce wadanda aka sha wahalar jam’iya da su a ce ba da su ake hidima ba sai ’yan PDP da muka kayar bayan sun yi shekara 16 suna mulki mu kuma muka yi hakuri a cikin adawa har na tsawon wannan lokaci. Ya kamata a ce an yi adalci, wato a ajiye abu bisa muhallinsa, da zarar ba a yi haka ba, to an samu matsala. To ka ga ashe ba zai yiwu a yi hakuri da wannan ba. Sannan kuma ba mu ga an dauki hanyar cika alkawurran da aka dauka ba. Wadannan su ne dalilanmu na jayayya. Saboda haka mu gyara muka zo domin ganin an cika alkawurran da muka daukar wa jama’a.
To Ai gamayyar jam’iyu ce ta kawo APC?
Haka ne, amma kuma jam’iyun CPC da ACN da kuma ANPP. To a Katsina ina tabbatar maka da cewa babu wani wanda ya yi ANPP yake da wani mukami a gwamnati ko wanda ya yi ACN, mutanan CPC ma babu. ’Yan kadan ne suka biyo Gwamna Masari daga cikinsu ne aka ba wasu mukami. Amma daga ACN ko ANPP ban san wanda aka ba wani mukami ba. Amma a matakin kasa za ka ga duk wadannan jam’iyu sun samu wani kaso. Yanzu ba ma ta mu ake magana ba, a’a magana ake ina dan PDP?. Idan ka lura a yanzu ga wasu manyan ’yan PDP nan ana ta dauka, idan ka lura da kyau ana so ne jam’iyar ta koma ta ’yan PDP gaba daya. To wannan manufar da muka gano shi ya sa muka ce ba za mu tsaya muna kallo ba.
Tun daga CPC kuna tare da shi Gwamna, ba ka ganin a dinke barakar cikin ruwan sanyi yafi ganin cewa Jihar Shugaban kasa ce kuma zabe na karatowa?
Duk fa inda ka ga ana ja-in-ja ba haka aka so ba, za ka tarar akwai inda daya ya nuna taurin kai. Wasu ne suka zagaye gwamna suka hana ruwa gudu, idan kuwa har akwai hakan to ka ga babu yadda za ka yi da shi dole sai ka yi hakuri ku zo a yi fadan a gane cewa abin da ake yi a gwamnatin ba daidai bane, wannan shi ne dalilinmu. Ai kungiya ce muka kafa, ka ga idan ana so a shirya sai a nemi kungiyar baki daya ba wai a rika zarar wani daga ciki ba a ce ya fito a yi da shi. Kuma ai shekara hudu za a yi a gwamnatin, to yanzu har an yi wasu shekarun daga ciki kuma a cikin barna, to yaya za ka yi ka gyara a cikin wannan lokacin kafin zabe?
Amma kuma gwamnati na cewa tana gudanar da ayyuka tare da biyan hakokin ma’aikata, wannan ba abin yabo bane?
Ai ita jam’iyar PDP da muka kalubalanta ba ta bar wani bashi na ma’aikacin gwamnati ba. To kuwa in har haka ne, idan mun yi haka ai ba laifi bane, munyi daidai. Amma inda akwai matsala shi ne a rika fadin abin da ba a gama ba. Su kansu ‘yan fansho da ake magana har yanzu wasunsu ba a basu kudin ba, amma magana ya riga badawa. To a wannan bangaren ka ji yadda abin yake.
Ba ka ganin jam’iyar PDP za ta iya amfani da wannan damar ta karbe mulki?
Ina? Ai a lokacin da shi Gwamna yake zare wasu daga cikinmu, a hannu daya mu kuma ‘yan APC AkIDA mutanan PDP suna biyo mu, saboda haka ba na tsammani za mu yi wata jayayya a Jihar Katsina da PDP. Kuma ina so ka sani cewa daga cikin wadanda suka yi takarar Gwamna da shi mai ci a yanzu, muna tare da hudu. Akwai Abubakar Sama’ila da Sadik ’Yar’aduwa da Sada Ilu da kuma Bugaje. Ina jin Audu Soja ne kadai yake tare da Gwamna a yanzu.
Ina uwar jam’iya ta jihar wadda ya kamata ta sa baki a kan matsalar?
Yo ina uwar jam’iyar take? Abin da ke akwai shi ne mu uku muka yi takarar shugabancin jam’iyar tun farko, ni da Dokta Mustafa Inuwa da Dokta Abdul aziz. Sai muka ce idan an zabi shugaba to a zo a debo abin da wannan sashe ya tsara da na wancan sashe ta yadda kowa na da hannunsa a ciki. To da aka gama zabe sai suka kauce, hatta da takardar da muka sanyawa hannu, sai suka zabi mutumin da suka ga dama suka bar mu a waje mu da mutanenmu. Amma saboda Jihar Buhari ce sai muka hakura don kada a ce mun kawo matsala. Ka ga tun da ba al’umma suka zabi mutum ba saboda shi wanda aka zabar, ya kauce zuwa wani mukamin a gwamnatance sai kawai wani ya ce wancan ya kawo yaronsa,wancan ma ya kawo na shi aka taru aka hada, ina kake tsammanin za a yi abu mai kyau a nan?. Duk kuwa wanda aka nada a jam’iyar siyasa ka ga bai san darajar jam’iya ba ballantana ta mutane saboda ba mutanan bane suka zabe shi.
An ce an kore ka daga jam’iyar kuma ka yi shiru ba ka ce uffan ba?
A nan zan ce ina ba al’ummar Jihar Katsina hakuri domin tun da aka ce an kore ni daga jam’iyya ba a ji na ce komai ba. To abin da ya sa ban ce komai ba takardar da aka rubuto wa Kabir Murja aka ce an kore shi, da takardar tsiren naman da aka ci aka jefar duk daya suke a wajena. Kuma ai batun mai rike da mulki daban maganar jam’iya daban. Ni memba ne na jam’iya kuma ana kirana taron masu ruwa da tsaki, kuma har yanzu ba a yi wani ba balle ince ba a kira ni ba. Shi korar mutun kamar yadda tsarin mulkin jam’iya ya ce yana da ka’idoji da dama wanda sai an cika su abin ke tabbata. Farko dai akwai bayar da damar jin ta bakin wanda ake zargi wanda ni ba a yi haka ba. Kuma bani kadai aka yi wa haka ba a cikin shugabannin, da zarar an ce mutun yana Akida sai a ce an kore shi. Idan kuwa haka za a rika yi sai an kori mutanen baki daya. Kuma ai shi tsarin mulkin Najeriya ya bada damar mutum ya fadi albarkacin bakinsa a kowane irin al’amari.
Akwai wasu mukamai da aka baku, amma maimakon ku ba ’yan siyasar da kuke tare da su sai kuka ba ’ya’yanku?
Shi al’amari na siyasa mutane na wasa da shi. Maganar an ba ’ya’yan masu yin APC Akida ai ’ya’yan nan har yanzu Kwamishinoni ne. Bari mu yi magana ta Alhaji Sada Ilu, ai dan nashi na nan Kwamishina. To wai da ma cin hanci aka basu don in sunga barna su yi shiru? Ko me ake nufi da wannan? ’Ya’yan suna cikin gwamnati, shi kuma yanzu siyasa yake yi, idan ya ga barna don anba dansa kwamishina sai ya yi shiru saboda an bashi cin hanci? Yanzu shi dan da ke kwamishina me zai ba Sada Ilu mutumin da ya kai kololuwa a wajen aikinsa? Sannan wurin da dan yake me yake samu balle ya ba wani? Saboda haka ba wata hujja ba ce za a kawo ace an ba ’ya’yansu wasu Kwamishinoni.
Sauran shugabannin jam’iyar sun yarda da abin da kuke yi?
Alhamdulillahi. Kusan kashi 80 cikin 100 sun yarda da abin da muke yi saboda su ma me suka gani? Da su aka yi gwagwarmaya har aka tsaida Masari ya ci zaben fidda gwani, sune kuma suka yi zabe na gama gari, amma ina so ka sani akwai ’yan Akida a cikinsu amma tsoro ya hana su motsawa. Ai taron da muka yi na Kaduna wasu sun zo amma wannan dalilin zuwan yasa aka kore su daga jam’iyar saboda basu da ’yancin kansu.
Shin in son samu ne kamar me kuke so gwamna ya yi?
Zan iya dauko abu daya zuwa uku. Da farko dai sakamakon bayan taron da muka yi a Katsina muna cewa ya gaggauta ba jihar nan bayanin kudaden kananan Hukumomi da ya amsa daga shigowarsa ofis zuwa yanzu, wato abin da aka samu da kuma yadda ya yi alkawali cewa zai kasa bisa faifai a lokacin da muke yakin neman zabe.
To yanzu wace fata gare ku ga gwamnatin?
Fatar da za mu yi ga al’umma da ita kanta jam’iyar shi ne kiyaye doka. Muna bin shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda bin doka da oda ne,to bai kamata mu daga Jihar Katsina muna karya doka da yin yadda muke so ba saboda mun raina Buharin. Kuma ba tare suke da Buharin ba. Sun yi amfani da wannan damar sun ci zabe kuma sun jefar da shi.
Mene ne abin yi?
Mu dake son Buharin shi ne muka dauko wannan salon na Akida, Akidar gaskiya kuma Akidar Buhari.
Amma kamar da wuya tunda baku da gwamnati?
Ai PDP shekara 16 ta yi,amma da jama’a suka ga ba su sonta basu canza ba? To haka jama’a za su canza gwamnatin da ba ta yi adalci ba.