Abin da ya sa muka kafa jam’iyyar matasa – Shugaban Jam’iyya
Aminiya ta zanta da shugaban riko na Jam’iyyar Matasa wato Youth Party (LP) na kasa, inda ya bayyana dalilan da ya sa suka kafa jam’iyyar da kuma manufofinsu: Ko za ka gabatar da kanka a takaice? Da farko dai sunana Suleiman Usman Yusuf, Shugaban Riko na kasa na Jam’iyyar Matasa, wadda a Turance ake kira […]
Aminiya ta zanta da shugaban riko na Jam’iyyar Matasa wato Youth Party (LP) na kasa, inda ya bayyana dalilan da ya sa suka kafa jam’iyyar da kuma manufofinsu:
Ko za ka gabatar da kanka a takaice?
Da farko dai sunana Suleiman Usman Yusuf, Shugaban Riko na kasa na Jam’iyyar Matasa, wadda a Turance ake kira da Youth Party (YP), mai taken kyautata gobe (shape the future).Jam’iyyar Matasa jami’iyya ce wadda aka assasa don fadada damar siyasa ga kowa, ba tare da nuna bambanci da kyama da son rai da izgilanci ba. Jam’iyya ce wadda za ta ba da dama ga duk wani mai niyyar yin takara don kawo cigaban al’ummarmu da kuma kasarmu Najeriya.
Mene ne dalilin kafa wannan jam’iyyar?
Mun yi la’akari da irin siyasar da jam’iyyu masu ci ke gudanarwa, wanda ke cike da son kai ba cigaban al’umma baki daya ba, siyasar wariya da amfani da kudi da rashawa da siyasar ubangida ke tauye hakki da tashin hankali da dai sauran su. Ko kuma yin amfani da matasa a cim ma buri, daga bisani a watsar da su. Har ila yau, matasa (‘yan tsakanin shekaru 18 zuwa 45) sun kasance su ne kashi 75 na masu kada kuri’a. Wadannan al’amura ya sa muka ga ya dace mu kafa jam’iyyar da za ta kawo sauyi na kwarai ga al’umma.
Mene ne manufofinku?
A Jam’iyyar Matasa mun rungumi siyasa a bayyane, wadda za ta kore siyasar zamba da cin hanci da rashawa da rikici da rashin tsari da kunci da takura. Muhimman manufofinmu sun hada da;
i. Samar da dama ga kowa, ta hanyar inganta ilimi da kiwon lafiya da muhalli mai rahusa.
ii. Samar da tsarin kasuwanci da bunkasa tattalin arziki na kashin kai ba tare da shisshigi ko katsalandan ba.
iii. Kasa daya ( Samar da jituwar addinai da kabilu).
ib. Inganta damar siyasa ta hanyar bunkasa tsarin cikin gida da fid da gwani a bayyane.
b. Canji na bai-daya a mulkin siyasa.
Mun yi amanna da siyasa ingantacciya da kawo gyara.
Ya kuke ganin za ku fafata da manyan jam’iyyu irin su PDP da Atiku ?
Daga manufofin za a iya ganin bambancin mu da sauran jam’iyyu. Ko daga tsarin zaben fid da gwani muna da bambanci da su. A Jam’iyyar Matasa duk dan jam’iyya yana da hakkin kada kuri’a a zaben fid da gwani ba wai a bar wa wasu tsirarun mutane ba, kamar yadda yake faruwa a wasu jam’iyyun.
Ya maganar kudi fa, kasancewar siyasa sai da kudi a wannan zamani?
Babban tsarinmu na samun kudin gudanar da harkokin jam’iyya shi ne ne ta hanyar membobinmu. Kowane memba na jam’iyya a kowane karshen wata zai rika ba da kudin da bai gaza naira N200 biyu ba. Idan a misali jam’iyya a ce tana da membobi miliyan daya da suke ba da Naira 200, a kowane wata zai zama jam’iyya tana da Naira Miliyan dari biyu. Ka ga ko da wadannan kudade jam’iyya za ta iya kashe duk matsalolinta ba tare da matsi ba. Wannan tsari da ma wasu tsarurruka na samun kudaden shiga su ne muke kai. A duk lokacin da jam’iyya ta ce wai daga wani mutum daya ko kuma daga wasu tsirarrun mutane ne za ta rika samun kudin kula da kanta, to fa jam’iyya ta zama ba ta al’umma ba. Jam’iyyar Matasa za ta tabbatar da bayyana wannan tsari kan harkokin shiga da fice na kudade.
Me ya sa kake ganin za ku yi tasiri a zaben 2019?
Mu ne kadai kuma jam’iyya ta farko wadda ta fara ba ‘yan takaranta horarwa na musamman a kan yadda za su tafiyar da harkar shugabancin al’umma, da kuma yadda za su tafiyar da mutane daban-daban, tare da yadda za su gudanar da tsare-tsaren kawo cigaba ga al’umma.
Bugu da kari, kasancewar jam’iyyar sabuwa ce, ba mu da dan’ takarar shugaban kasa, da gwamnoni. ‘Yan takaran majilisar jiha da na tarayya kawai muke da su. Dalilin hakan kuwa shi ne muna son jama’a su ga kamun ludayinmu a kan kananan matakan shugabanci tukunna, kafin mu kai ga neman manyan mukamai.
Mene ne kiranka ga matasa?
Ya kamata matasa su daina yarda a yi ta amfani da su ta hanyoyin da ba su dace ba. Dole kuma mu mike tsaye mu nemi ilimi ingantacce, domin shi mulki da ma duk wani lamari na duniya sai da ilimi. Da ilimi ne kadai za mu iya kwatar gurabenmu daga hannun azzalumai da kuma duk wasu wadanda suka jefa mu a halin da muke ciki a yau. Ya zama dole a gare mu, mu shirya wa gobe tun a yau.
Ko kana da kira zuwa ga gwamnati da INEC?
Ina mai kira ga gwamnati da ta tabbatar an yi zaben adalci a 2019. Ta tabbatar da an bar mutane sun zabi abin da suke so ba tare da tsangwama ko wata barazana ba. Ta haka ne kadai za a samu cigaba da kauce wa rigima da tashin hankali a kasarmu da kuma tabbatar da wanzuwar dimokuradiyya ingantatta. Ita kuma Hukumar INEC ta kasance ta gudanar da aikinta bisa amana da tsoran Allah. Domin kuwa ita kasa tana cigaba ne idan duk wani wanda aka dora wa alhakin gudanar da hakkin al’umma ya gudanar yadda ya kamata ba tare da tsoro ko nuna bambanci ba.
A karshe me za ka ce game da Gwamnatin APC?
Su san cewa duniya juyi juyi ce. Saboda haka su yi amfani da damar da ke hannunsu yanzu wajen kawo ci gaba da kyautata wa al’umma baki daya.