Abin da ya sa muka kashe Odunukwe – Likita Bob

A kwanakin baya ne ’yan sanda suka kama wani likita mai suna Daniel Bob Ibeaji da wadansu mutum uku da ake zargi da kashe attajirin nan na Legas Cif Ignatius Odunukwe domin mallake wani gidansa na Naira miliyan 900, Aminiya ta zanta da likitan wanda ya bayyana dalilin da ya sa ya yi watsi da […]

Abin da ya sa muka kashe Odunukwe – Likita Bob

A kwanakin baya ne ’yan sanda suka kama wani likita mai suna Daniel Bob Ibeaji da wadansu mutum uku da ake zargi da kashe attajirin nan na Legas Cif Ignatius Odunukwe domin mallake wani gidansa na Naira miliyan 900, Aminiya ta zanta da likitan wanda ya bayyana dalilin da ya sa ya yi watsi da aikin likitanci da yadda ya kashe attajirin:

 

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Dokta Bob: Sunana Daniel Bob Ibeaji, ni likita ne dan asalin Jihar Enugu kuma shekarata 41. Na yi firamare da sakandare a Legas a makarantar AOBSS wato makarantar sakandare ta maza zalla. Bayan na kammala sai na fita kasar waje inda na yi karatun likita. Da na kammala na dawo Najeriya na yi aikin likita na wata uku kacal a Asibitin Holy Trinity da ke Abuja. Bayan na bar aikin sai na koma kasuwanci gadan-gadan ina zuwa sayen ma’adanai a jihohin Zamfara da Osun, da suka hada da zinare da sauransu, ina sayar da su a nan Najeriya ina kuma kaiwa kasar Afirka ta Kudu.

Me ya sa ka daina aikin likita?

Dokta Bob: Ra’ayina ne kawai, ni mutum ne mai son tara dukiya, na kuma lura ba zan iya cimma burina da aikin likitanci ba, don haka na bari na kama kasuwanci. Ba ni kadai na yi irin wannan ba, za ka ga akwai likitocin da suka daina aikin suka koma fastocin coci suka gina manyan majami’u suna samun kudi wadansu ma ba likitoci ba ne, masu tukin jirgin sama ne, wadansu kuma manyan hafsosin soji ne amma suka bar aikin suka kama wanda suke gani za su tara dukiya da shi.

Yaya aka yi ka samu kanka alamarin kisan attajiri Ignatius Odunukwe?

Dokta Bob: Kamar yadda na fada maka a garin Abuja nake zaune, na ga sanarwar tallar katafaren gidansa ne a Unguwar Katampe a garin Abuja a wani waje da ake sanya tallar kadarori da suka hada da manyan gidaje da filaye. Sai na nuna sha’awa na tambayi jami’in da ke kula da tallar ya hada ni da mai kayan wato Cif Ignatius Odunukwe, mamallakin Kamfanin Janareta na Firearm. Nan da nan sai dattijon ya umarci jami’in da ya ba ni lambar wayar salularsa, bayan ya ba ni sai muka fara waya da shi kai-tsaye daga bisani na shirya na tafi Legas na same shi muka hadu ido-da-ido.

Yaya aka yi kuka yi cinikin gidan har ya san hannu a takardun gidan?

Dokta Bob:  A ’yar mu’amalar da na yi da shi ya saki jikinsa da ni sosai, ya kuma sakankance cewa, da gaske nake zan sayi gidan, in ba shi kudinsa. Na hadu da shi mun zauna sau uku, na ziyarce shi a ofishinsa ya zo ya same ni a otel dina. Wannan ’yar mu’amalar da muka yi ita ce ta sanya ya sakankance ya yarda da ni. Ranar da ya zo da takardun cikin sauki na ce ya sanya hannu, nan take ya sanya hannu cewa ya sayar min da gidan a kan Naira miliyan 900. Mun yi haka ne a harabar otel din Artican Beach da ke Ajah a zauren da ake shan barasa. Bayan ya sanya hannun sai na nemi ya bi ni cikin dakina na otel din domin ya karbi kudinsa inda a nan muka kashe shi.

Yaya kuka kashe shi?

Dokta Bob: Dama na riga na shirya da abokan ta’asata kan yadda za mu kashe shi, suna cikin dakin a labe koda na shiga da shi na nuna masa buhun kudi, a daidai lokacin da hankalinsa ya tafi wajen sai na yi alama, nan take daya daga cikin wadanda suka taya ni aikin mai suna Solomon Cletus, ya fito da adda ya daba masa a kai, daga nan ragowar biyun suka fito suka rike shi na yi masa allurar kashe jiki. Na yi masa allurar ce domin in kashe masa jiki kada ya yi kururuwa ya fallasa mu. Amma ba ta yi aiki yadda na so ba, ba allurar ce ta kashe shi ba, bugun da aka yi masa da adda ne ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Ta YAya kuka fita da gawarsa daga otel ba tare da asirinku ya tonu ba?

Dokta Bob: Na kama daki a otel din tsawon kwana hudu, a cikin wadanda suka taya ni aikin, akwai Arinze Uzor wanda tsohon ma’aikacin otel din ne da ya daina aiki da su. Ya san otel din ciki da bayansa, shi ne ya nuna mana kofar baya ta nan muka fita da gawarsa a cikin jakar leda daga nan muka kai ta daji muka zubar, na yi wa abokan aikin nawa alkawarin zan ba su Naira miliyan biyu kowanensu, su uku. Dama na riga na kira su ta waya na shaida musu abin da nake so mun yi lokacin da na shiga Legas.

Ban kai ga ba su kasonsu ba ’yan sanda suka kama ni a Abuja, domin an kama ni ne kimanin mako biyu da kashe attajirin. Mun kashe shi a ranar 1 ga Disamban bara. Ayarin ’yan sanda na musamman na ZIP ne ya kama ni bayan sun bibiyi lambar wayata. Sun kama ni ne a lokacin da nake kan hanyar zuwa gidan wata ’yar uwata a Abuja. Daga nan ne suka kawo ni Legas bayan an kai ni wani ofishin ’yan sanda a Abuja. Lokacin da suka kama ni sun samu takardun gidan  attajirin a hannuna, ban kai ga sayar da gidan ba kamar yadda wadansu ke fada. Na kira direban tasi na kamfanin urba na ce ya tafi da motar attajirin gidansa ya aje min. Amma ban nuna masa cewa ba motata ba ce, shi ma direban yanzu haka yana tare da mu an kama shi.

Ko ka yi nadamar abin da ka aikata?

Dokta Bob: Tabbas na yi nadama kasancewar na kashe wannan dattijo, idan na tuna abin yana kona min rai. Domin ni ma a baya ina da tsoho ya yi rayuwarsa ya gama ya mutu, ba a irin wannan hali ba, ba wani ne ya kashe shi ba. Don haka in na tuna wannan abin na damuna lura da yadda na kashe dattijon.