Abin da ya sa muka ki zaben Ikimi shugaban APC – Tinubu
Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jigo a Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu ya ce sun ki zaben tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya Cif Tom Ikimi a matsayin shugaban jam’iyyar ce saboda mutum ne marar gaskiya.Bola Tinubu yana mayar da martini ne kan zargin da Ikimi ya yi masa na dakile shi daga shugabancin jam’iyyar da […]
Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jigo a Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu ya ce sun ki zaben tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya Cif Tom Ikimi a matsayin shugaban jam’iyyar ce saboda mutum ne marar gaskiya.
Bola Tinubu yana mayar da martini ne kan zargin da Ikimi ya yi masa na dakile shi daga shugabancin jam’iyyar da dora wa jama’a shugabannin tilas, lamarin da ya jawo ya fice daga jam’iyyar a makon jiya.
Bola Tinubu wanda ya mayar da martanin ta ofishin watsa labaransa, ya ce Ikimi wanda jigo ne a Jam’iyyar APC, jam’iyyar ba ta amince ya zama shugabanta ba ne, saboda miyagun halayensa na baya, domin in ta zabe shi, zai zamo ba za ta iya kwanciya ta yi barci ba, gudu kada ya sayar da ita kafin gari yaw aye.
Ya ce, “A fili yake duk wanda yake son jam’iyyar a zuciyarsa ba zai lamunci masu hali irin na Ikimi su shugabance ta ba. Wane mai hankalin ne zai hada mutane masu gaskiya da rikon amana wato Bisi Akande da Cif Oyegun da wani wai shi Tom Ikimi? Mutanen biyu an san su da tsayawa kan kafafunsu, ko sau daya ba ku ji an ce sun ci amana ko sun zama Karen farautar wani ba.”
Tinubu ya ce, Ikimi bai sadaukar da kansa ga APC, kullum yana yi wa PDP aiki ne a cikinta. Ya kara da cewa, Ikimi ya bukaci zama shugaban jam’iyyar ce kawai domin neman na bagas, kuma ficewarsa daga jam’iyyar ba zai yi mata wata illa ba.
“Na san zai koma wurin masu daukar nauyinsa. Ya koma kamfanin da ya fito, kuma APC ta ji dadin haka,” inji Tinubu.