‘Abin da ya sa muka kirkiri bikin Ranar Hausa’
An fara gudanar da bikin ne a 2015 a shafukan sada zumunta na zamani.
An fara gudanar da bikin ranar Hausa ne a shekarar 2015 a shafukan sada zumunta na zamani.
A lokacin dai, ana alakanta wani ma’aikacin Sashen Hausa na BBC, Abdulbaki Jari da cewa shi ne da wasu abokansa suka fara bikin ranar don su bunkasa harshen don ganin ya yi kafada da kafada da sauran yarukan duniya.
- An rada wa jaririn Aghanistan da aka haifa a jirgin Amurka sunan jirgin
- ‘Dalilai 7 da za su sa Majalisar Dinkin Duniya ta amince da Ranar Hausa a hukumance’
A wata tattaunarsa da Aminiya, Abdulbaqi ya ce babban dalilin da ya sa suka kirkiri ranar shi ne ganin yadda dukkan kasashen suka ci gaba sun bunkasa ne ta hanyar amfani da harsunansu na gida, inda ya ce ya zama wajibi harshen Hausa ma ya sami irin wannan tagomashin.
Ya ce, “Da yawan masu amfani da Turanci a kafafan sada zumunta suna yin haka ne don su nuna cewa sun fi sauran wadanda basu yi Boko ba wayewa. Kai kusan duk kasashe masu farcen susa sun yi amfani da harsunansu na gida ne don kaiwa gaci.
“Sannan kuma mun lura cewa cikin daukacin harsunan da ake amfani da su a Afirka ta Yamma, babu wani harshe da ya kai Hausa yawan masu magana da shi.”
Da yake bayani a kan abin da ake gudanarwa a ranar, Abdulbaki ya bayyana cewa a na tattauna duk wani abu da ya shafi Hausawa, kama daga harshensu da al’adunsu da adabinsu.
Ya ce an zabi ranar 26 ga watan Agusta ne saboda alakarta da harshen Hausa, domin a ranar ne aka fara amfani da wasu bakake na daidaitaccen rubutun Hausa ta hanyar amfani da haruffan Boko da na Larabci (Ajami).
Abdulbaki ya kara da cewa a shekarar 2020, an gudanar da shagalin bikin ranar a kasashen duniya fiye da 15 , ciki har da Faransa da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Sudan da kuma Burtaniya.
‘So muke mu ga Hausa ta taka matsakin da ya dace da ita’
Da Aminiya ta tambaye shi ko meye burinsu a kan bukukuwan a nan gaba sai ya ce, “Muna fatan ci gaba da gwagwarmaya har sai duniya ta ba Hausa matsayin da ya kamaceta.
“So muke Hausa ta zama daya daga cikin manyan harsunan duniya, alal misali yanzu ana magana da harshen Hausa a Afirka ta Yamma fiye da harsunan Larabci da Turancin Ingilishi da na Faranshi, wannan kuma shi ya karfafa mana gwiwa muka nemi a ayyana Hausa daya daga cikin harsunan da a hukumance ake amfani da su a Kungiyar Cinkikayyar Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da Tarayyar Afirka (AU) da kuma Majalisar Dinkin Duniya, kuma tuni mun aika wannan bukata a rubuce.”
Daga karshe ya ce, “A yanzu harshen Hausa ne na 11 a jerin harsunan da aka fi amfani da su a duniya, sannan akwai harsashen masana da yake cewa nan da shekara ta 2050 matsayin zai cilla sama zuwa na biyar a duniya.”