Abin da ya sa muka ladabtar da alkalai a Jihar Bauchi – Hukumar Shari’a
Wadanne irin ayyuka ne wannan hukumar ke yi? Ita Hukumar Kula da Harkokin Shari’a (Judicial Serbice Commission -JSC), hukuma ce da take lura da ladabtar da ma’aikatan kotuna da suka hada da kananan alkalai wato majistarori da alkalan kotunan shari’a na larduna da kotunan shari’a. Sannan wannan hukuma a kowane lokaci Babban Akalin Jiha shi […]
Wadanne irin ayyuka ne wannan hukumar ke yi?
Ita Hukumar Kula da Harkokin Shari’a (Judicial Serbice Commission -JSC), hukuma ce da take lura da ladabtar da ma’aikatan kotuna da suka hada da kananan alkalai wato majistarori da alkalan kotunan shari’a na larduna da kotunan shari’a. Sannan wannan hukuma a kowane lokaci Babban Akalin Jiha shi ne ke shugabantarta. Kuma a cikin mambobin hukumar akwai Alkalin-Alkalai akwai kuma Kwamishinan Shari’a da kuma wadansu da ake nadawa kamar lauyan da ya kai shekara goma da zama lauya. Sukan zauna a kan karin girma ko ladabtarwa ko kuma duk wani abu da ya shafi wani ma’aikaci ko kuma alkali domin daukar mataki a kai.
Kwanan baya kun yi wani hukunci a kan wadansu alkalai ko me ya jawo haka?
Abin da muka yi mun yi shi ne a bisa doka, dama dai dokokin suna nan; korafe-korafe ne muka samu daga wajen jama’ar gari wadannda kuma hukumar nan ta zauna ta yi bincike sosai aka tabbatar suna da laifi sai aka yi musu hukunci gwargwadon laifuffukan da suka aikata, kuma cikin adalci bisa yadda dokar wannan hukumar ta shimfida.
Wadanne irin laifuffuka kuka same su da su kuma wane irin hukunci kuka yi musu?
To, daga cikinsu akwai wadanda hukuma ta same su da laifin sun karbi kudade a hannun mutane a kan wai za su samar musu da aikin gwamnati; don haka ne mutanen suka yi korafi a kai, bayan kaddamar da bincike da hukuma ta yi aka samu akwai tabbaci a cikin korafin, aka sanya su suka biya mutanen kudadensu sannan aka dauki matakin hukunta su. Wadansu kuma daga cikin alkalan sun yi laifuffuka ne da suka shafi shari’a, kamar yin ayyukan da ba su dace ba, ba kuma ya yi kuskure ba, a’a ya yi ganganci ne, ko kuma gwada halin ko-in-kula a kan aikinsa, bayan gudanar da kwakkwaran bincike aka kira su aka ba kowa damar kare kansa daga bisani aka yi musu hukunci. Bari in ba ka misali, akwai alkalin da aka zartar da hukunci a kan idonsa, bayan an yi hukunci kuma aka rushe wannan wajen duka a kan idonsa, bayan kuma suna da masaniya kan cewa an daukaka karar, an kuma shigar da takardar dakatar da hukuncin. Ka ga kamar alkali bai da hurumin zuwa wajen zartar da hukunci, muna da kwararan hujjoji na cewa ba ma da ’yan sanda aka je ba; an je ne da jami’ai na ma’akatan gidan yari aka zartar da wannan hukuncin, to tunda ya yi abin da bai kamata ba dole ne a yi masa hukunci, domin ya zama darasi ga sauran wadanda ba su aikata laifi irin wannan ba don su ji tsoron aikatawa, su kuma mutane su sani duk da alkali na da dama a hanunsa amma idan ya yi ba daidai ba za a ladabtar da shi gwargwadon yadda doka ta tanada.
Shi wannan alkali da ya je wajen zartar da hukunci da wadanda suka karbi kudin jama’a wane irin hukunci kuka yi musu?
Shi wanda ya je wajen zartar da hukunci an cire shi ne a matsayin alkali aka mai da shi magatakardan kotu, sannan aka rage masa matakin albashi daga na goma sha biyar 15 zuwa na goma sha 14, shi kuma alkalin ba na karamar kotu ba ce na Lardi ne, Babban Kotu ke nan. Wadannan da suka amshi kudaden ba yanzu ba ne suka karbi kudaden nan ba; sun yi wadannan laifuffukan ne shekara hudu da suka wuce wadansu kuma biyar ma; tun ni ban zo wannan hukumar ba, tun kuma Babbar Jojin Jihar nan ba ita ba ce Babbar Joji a lokacin, amma da yake korafe-korafen sun yi yawa, kuma an kawo kuka da yawa tunda dai laifi laifi ne sai hukumar ta bayar da umarni a bincika kuma aka bincika aka tabbatar aka kai gaban hukuma, duk da dai ya biya kudin da dadewa aka ce to bai cancanci zama alkali ba; daya daga ciki sai aka cires hi aka mai da shi magatakardan kotu bisa laifin amsar kudi da sunan zai samar da aikin yi, shi kuma dayan dama ba alkali ba ne magatakardan kotu ne shi ma duk da ya biya kudin da ya amsa sai aka rage masa matakin albashi daga na goma zuwa na tara, aka kuma yi musu gargadi cewa idan aka sake samun wani da laifi makamancin wannan, tunda laifin ya jima koda sun biya ne to za su iya rasa aikinsu gaba daya.
Jama’a na na ganin cewa wannan hukunci ya yi tsauri kuma tuntuni ba a dauki wani mataki na tsarkake hukumar shari’a ta jihar ba sai yanzu ko me ya sa?
Abin da zan fada a nan shi ne ka san ita Babbar Mai shari’a ta Jihar nan Hajiya Rabi Talatu Umar zuwanta ta rigaya ta yi alkawarin cewa za ta yi aikinta tsakaninta da Allah kuma duk wanda aka same shi da laifi ba za a bar shi ba, sannan dukan mambobin wannan hukumar su ma sun yi alkawarin yin ayyukansu tsakani da Allah. Idan mutum ya yi laifi a baya har ya kai shekaru, to idan sai a yanzu wannan laifin ya fita, kuma aka bincika aka tabbata, za a iya yi masa hukunci. Wannan matakin da muka dauka na gyara ne, kuma ba za mu bar wannan gyaran ba an fara ke nan.
Yanzu idan wadanda kuka yanke musu wannan hukuncin suka ga hakan bai yi musu ba, suna da damar su yi kara a kotu?
Wadanda wannan hukuncin ya shafa su ne za su yanke wa kansu wannan hukunci. Ita dai wannan hukumar ta yi nata, sannan kuma zuwa yanzu babu wanda ya yi korafi daga cikinsu kan cewa ba su yarda ba. Don haka wannan shawarar tasu ce, ba za mu ce ga abin da za su yi ko ga wanda ba za su yi ba. Sannan ina tabbatar wa jama’a cewa duk wanda ya yi korafi tabbas za mu duba, matukar kuma da gaskiya a ciki to za a yi abin da kamata. Don haka ina kira ga jama’a, idan mutum zai yi korafi ya tabbatar yana da kwakkwarar hujja.
Wadansu suna tsoron kai irin wannan korafi ga hukumarku, me za ka ce a kan wannan?
Idan alkali ba wani laifi ya yi ba, ba kudi ya amsa ba, ba kuma wani abu ya yi na ganganci ba, matukar shari’a ne ya yi maka sai ka dauka ka kai kotun gaba idan ba ka gamsu ba, ita wannan kotun za ta duba ta gani an yi maka adalci ko kuma ba a yi maka ba, amma idan wani abu ne alkali ya yi wanda ya saba wa dokar aiki, shi ne za ka yi korafi a kai. Amma idan ana magana ne kuma a kan cin hanci ko kuma take doka ko na goyon bayan wani ta yadda bai kamata ba, shi ne za ka kawo korafinka wannan hukumar.