Abin da ya sa muka rufe tafsiri a asirce – Sheikh dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce ba su kira taron rufe tafsirin bana a bainar jama’a ba ne saboda shawarar da hukumomin tsaro suka ba su. Sheikh dahiru Bauchi ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Bauchi. Ya ce, “Hukumomin tsaro a Jihar Kaduna sun […]

Abin da ya sa muka rufe tafsiri a asirce – Sheikh dahiru Bauchi
Abin da ya sa muka rufe tafsiri a asirce – Sheikh dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce ba su kira taron rufe tafsirin bana a bainar jama’a ba ne saboda shawarar da hukumomin tsaro suka ba su.

Sheikh dahiru Bauchi ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Bauchi. Ya ce, “Hukumomin tsaro a Jihar Kaduna sun ce kada mu kira taron rufewa (tafsirin) saboda suna da bayanan sirri kan Dandalin Murtala saboda haka muka yi addu’a a masallaci muka rufe tafsirin. An samu labarin cewa akwai wasu mutane da suke yunkurin kai mana hari a Dandalin Murtala Sukwaya da ke Kaduna a ranar da za mu rufe tafsiri, don haka matsalar tsaro ta hana mu gayyatar mutane.”
Kan bayanin da Gwamnan Jihar Borno Kashim Shetitma ya yi cewa malamai suna tsoron magana a kan ’yan Boko Haram ne saboda gudun kada a kashe su, Sheik dahiru Bauchi ya ce, malamai suna magana, amma masu mulki ne ya kamata su yi maganinsu. “Saboda malamai ba su da makami kuma su ba gwamnati ba ne. Kowa ya san na sha yin magana a kan wannan batu kuma na fadi yadda ake jihadi a Musulunci na fadi a wurin taron mauludi da wurare da dama. Ba na tsoron kowa a duniya sai Allah, babu wani mutum da ya isa kai ni Lahira sai kwanana ya kare.”
Dangane da ziyarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Amurka malamin ya ce suna fata ziyarar za ta haifar da alheri, “Domin kamar yadda muka ji an tattauna batutuwa da dama har da halin da mutanen Arewa maso Gabas suke ciki na tashe-tashen hankula , yadda aka bata Najeriya muna ganin za a wanke ta cikin kankanen lokaci,” inji shi. Sai ya yi addu’ar Allah Ya ba gwamnatin Buhari damar cika alkawuran da ta dauka ga al’umma tare da ba su mashawarta nagari da za su fada musu gaskiya.
Sheikh dahiru Bauchi ya shawarci gwamnonin da suke kokarin hana bara a jihohinsu cewa su tabbatar sun samar wa miskinai abin da za su ci kafin hana su bara. Ya ce akwai wata jiha da ake kama mabarata ana tura su kurkuku, Allah ba Ya son a taba masa miskinai. “Masifar hana bara tana da muni, a kasashen Turawa an fada min cewa ana bara balle Najeriya. Ina fatar kada gwamnoni su dauki akidar hana bara kamar yadda wasu daga cikinsu suka fara a jihohinsu,” inji shi.