Abin da ya sa muka rusa Hukumar Alhazan Jihar Katsina – Gwamna Masari
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya rusa sashen gudanarwa da na aiwatarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai sakamakon gazawar da bangarorin biyu suka yi na sauke nauyin da aka dora musu na tafiyar da harkokin hukumar. Gwamna Masari ya fadi a jawabinsa bayan ya karbi rahoton Hajjin bana daga hannun Amirul Hajji na […]
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya rusa sashen gudanarwa da na aiwatarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai sakamakon gazawar da bangarorin biyu suka yi na sauke nauyin da aka dora musu na tafiyar da harkokin hukumar.
Gwamna Masari ya fadi a jawabinsa bayan ya karbi rahoton Hajjin bana daga hannun Amirul Hajji na Jihar, Alhaji Muntari Lawal a makon jiya a gidan gwamnati cewa, zamba da yaudara ne abin da suka rika faruwa da mutanen da aka danka wa amanar tafiyar da wannan aiki.
Gwamnan ya ce daga cikin masu yin zamba ko ha’incin a lokacin aikin Hajjin har da wadansu daga cikin ma’aikata ko shugabannin hukumar da ma’aikatan gwamnati da ake turawa da ’yan siyasa da kuma wadansu malaman addini.
Gwamna Masari ya nuna bacin ransa kan abubuwan da suka faru a aikin Hajjin bana, sannan ya jinjina wa Amirul Hajjin bisa jajircewarsa.
A jawabin Amirul Hajjin, Alhaji Muntari Lawal wanda ya nuna takaici kan yadda ake yaudarar gwamnati a wannan fanni sama da shekara 20. Ya ce duk lokacin da jami’an hukumar suka zo suka ce sun kama masaukai masu kyau kuma kusa da Harami a Makka ba gaskiya ba ce, yaudara da cuta suke yi.
Ya ce suna kama gidaje ne a wurare masu nisa da Harami, wasu gidajen ma an dade ba a amfani da su, amma sai su hada baki da wadansu jami’an da ake kama gidajen a Makka domin kama irin wadannan gidaje marasa kyau, bayan an karbi makudan kudi daga gwamnati da sunan an kama gidaje masu kyau.
“Misali shi ne, gidan da aka kai mata, gidan ya yi shekara 15 ba a zauna ba, bayan nisan da yake da shi da Harami. Akalla sai an yi tafiyar minti 50 daga gidan kafin a je Harami. Wani gidan ma daga cikin na maza tafiyar awa daya ce zuwa Haramin. Wani abin takaicin shi ne yadda mahajjata 150 da suka biya kudinsu a hukumance suka rasa masauki a Makka har sai da aka sake tuntubar Mai girma Gwamna ya bayar da wasu kudi aka kama musu masauki,” inji shi.
Da ya juya kan matsalar rashin lafiya, Alhaji Muntari ya ce, a aikin Hajjin bana, an samu wadanda suka samu matsalolin rashin lafiya na mutum 854. “Sai alhazanmu 4 da muka rasa a can, biyu maza biyu mata,” inji shi.
Ya ce, “Duk abin da na yi, Allah ne Ya yi mini jagora a kai domin na dauki wannan aiki a matsayin amana da Allah zai tambaye ni a kai fiye da komai saboda aikin addininSa ne.”