Abin da ya sa muka soke daukar nauyin alhazai da masu ziyara – Gwamnatin Kaduna

Aminiya ta tuntubi Mai bai wa Gwamnan Jihar Kaduna Shawara kan harkokin Adinin Musulunci da Kiristanci, Injiniya Muhammad Namadi Musa, inda ya bayyana dalilan Gwamna Malam Nasir El-Rufa’i na soke daukar nauyin mutane domin zuwa aikin hajji da kuma ziyara a kasar  Isira’ila. Ya ce matakin ya yi daidai, don haka sai ya nemi jama’a […]

Abin da ya sa muka soke daukar nauyin alhazai da masu ziyara – Gwamnatin Kaduna

Aminiya ta tuntubi Mai bai wa Gwamnan Jihar Kaduna Shawara kan harkokin Adinin Musulunci da Kiristanci, Injiniya Muhammad Namadi Musa, inda ya bayyana dalilan Gwamna Malam Nasir El-Rufa’i na soke daukar nauyin mutane domin zuwa aikin hajji da kuma ziyara a kasar  Isira’ila. Ya ce matakin ya yi daidai, don haka sai ya nemi jama’a su yi hakuri.

Aminiya: Me za ka ce game da matakin gwamna na dakatar da daukar nauyin mutane zuwa aikin Hajji da kuma ziyara Jerusalem?
Injiniya Muhammad Namadi: Duk wanda ya san abin da ake yi ya san hakan ya yi daidai. Misali a bara abin da kiristoci suka biya da kudinsu mutum 10, amma gwamnati ta biya wa mutum 800, Musulmi kuma aka biya wa mutum 2000. Ka je kauyaka ka gani, shin kujeruna  nan sun isa Ikara ko Sanga ko Samaru?  a cikin kananan hukumomin Kaduna ta Arewa da Kudu da sabon Gari suke karewa. ‘’Yan siyasa ne da manyan jami’an gwamnati ake bai wa. Yau a ba wannan, gobe a bai wa wancan. Sai ka ji mutum na cewa shekaru 20 da suka wuce yana zuwa aikin hajji. To, da za a yi adalci ne a ce wanda bai taba sauke faralli ba  ake baiwa da an samu sauki.
Kuma a cikin shikashikan musulunci biyar, aikin hajji ne  aka ce idan kana da hali, ba a ce maka dole ba. To, don me gwamnati za ta kwashe kudin da ya kamata ta yi wa jama’a aiki wajen gina makarantu da asibitoci tana biya wa wadansu kalilan kujerun hajji? sai ake ganin bai dace ba, domin kamata ya yi wannan kudi a yi amfani da shi ta wadansu hanyoyi da suka dace.
Wani gwamna ya taba yin wani abu a Kano, ya dauko mutane daga kananan hukumomi a jahar akalla 100, ya ce ga dubu 800 kudin kujerar hajji,  ga kuma dubu 500 na jari. A cikin mutum 100 din nan mutum uku ne kacal suka amince za su hajji, amma mutum 97 sun yarda su je su ja jari.
Wannan ya nuna maka cewa ba wajibi ba ne, domin kila a cikin wadanda suka karbi dubu 500 na jari a samu wanda a shekara mai zuwa ya biya wa kansa da matarsa hajji.  Saboda haka mu a ganinmu wannan mataki na Gwamna El-Rufai ya dace, kuma abin da ya kamata ke nan.
Aminiya: Wannnan hukunci zai shafi jami’ai masu taimaka wa alhazan ke nan (oficials)?
Namadi: Wadannan an rage su ne. Ina son ka sani cewa, abin da gwamnati za ta kashe a kan jami’an aikin hajji kawai ya kai wajen Naira miliyan 50, saboda akwai kwamitin Amirul hajj mai mutum 5, akwai jami’an tsaro na mutum 5,  akwai manyan hukumar Alhazai mutum 5, akwai malamai da za a tafi da su domin wa’,azi akwai ‘yan jarida, da sauransu, duk kuma gwamnati ce za ta biya. Wannan kadai ma ya isa gwamnati wahala, ba kawai ta rika kwasar kujeru tana raba wa ‘yan siyasa da sauran manyan masu hannu da shuni ba.  
Aminiya: Ba ka ganin wannan mataki da gwamnan ya dauka zai shafi farin jinin jam’iyarku?
Namadi: Ai duk abin da za ka yi idan ka yi don Allah, Allah Ya isar maka. Za mu yi don Allah ne, kuma addu’ar da aka yi mana cewa wannan abin da muke yi idan muna yi ne domin taimakon jama’ar jahar Kaduna ne,  Allah Ka taimake mu, Ka kara mana karfin gwiwa. Idan kuma ba muna yi ba ne domin taimakon mutanen Kaduna, Allah Ka kawar da mana da wannan tunani Ka kawo mana wanda zai sa mu taimake mutanen Kaduna.
Aminiya: Wane jan hankali za ka yi ga al’ummar  jihar Kaduna?
 Namadi:   Ina son su sani cewa hausawa sun ce zaman lafiya ya fi zama dan sarki, saboda haka wannan abu da gwamna ke yi yana son jadda zaman lafiya ne a jahar nan. Ina kuma son jama’a su gane cewa c anji baya zuwa da sauk,i dole mutane su yi hakuri, su kuma kara hakuri, su kuma dogara ga Allah tare da cigaba da yin addu’a. Duk lokacin da ka yi wa gwamna ko wani shugabanka addu’ar ya lalace to idan ya lalace kai ma za ka lalace.