‘Abin da ya sa muka takaita aikin Keke Napep a Abuja’
A ranar Talatar da ta gabata ce sabuwar dokar takaita amfani da Keke Napep a Abuja ta fara aiki a kwaryar birnin, bayan Hukumar Birnin Tarayya ta zargi masu sana’ar da saba wa ka’idojin da aka cimma da su yayin gudanar aikinsu. Jami’an tsaron hadin gwiwa da suka hada da ’yan sanda da na kiyaye hadurra […]
Shugaban Hukumar VIO ta Abuja Malam Wadata Aliyu Boxinga
A ranar Talatar da ta gabata ce sabuwar dokar takaita amfani da Keke Napep a Abuja ta fara aiki a kwaryar birnin, bayan Hukumar Birnin Tarayya ta zargi masu sana’ar da saba wa ka’idojin da aka cimma da su yayin gudanar aikinsu. Jami’an tsaron hadin gwiwa da suka hada da ’yan sanda da na kiyaye hadurra da na kula da ababen hawa wato (BIO) sun yi ta sintiri a titunan da lamarin ya shafa don tabbatar da dokar.
Masu gudanar da sana’ar da suka ce adadinsu ya kai dubu 30 a Abuja, sun kaurace wa titunan birnin ciki har da yankunan da aka amince musu su gudanar da sana’ar. Sun ce sun dauki matakin ne don nuna bacin ransu a kan sabuwar dokar, lamarin da ya jefa daruruwan mutane cikin wahala da daukar tsawon lokaci suna jiran ababen hawa.
A zantawarsa da Aminiya Shugaban Hukumar Kula da Lafiyar Ababen Hawa (BIO) ta Abuja Malam Wadata Aliyu Bodinga ya ce daukar matakin ya zama dole don kare hakkin sauran masu zirga-zirga da ababen hawa da ke amfani da titunan. Ya ce yarjejeniyar da suka yi da jagororin kungiyar ita ce ba a ba su damar yin aiki a tagwayen titunan birnin ba, sai dai a cikin unguwannin rukunin gidaje ko kuma garuruwa da ke wajen birnin.
“Shi dama aikin Keke shi ne karasawa da matafiya, ma’ana idan mota ta sauke ka a babbar hanya, idan kana sauri sai ka hau, amma ba a ba su damar yin doguwar tafiya a manyan titunan Abuja ba, har suna tsere da masu manyan motoci,” inji shi.
Ya ce: “Duk yunkurin da muka yi don su yi amfani da dokokin nan sun bijire, mu kuma ba za mu ci gaba da zuba musu ido haka ba, saboda wannan shi ne aikinmu na tabbatar da dokokin tuki a birnin Abuja da kewaye.”
Aminiya ta zanta da wani jigo a kungiyar masu sana’ar a Abuja Kwamred Abdullahi Aliyu inda ya ce dokar za ta shafi aikinsu da kamar kashi 60 cikin 100 idan ta tabbata. “Kowane Keke da kake gani ba a rasa kamar mutum biyu zuwa uku da ke aiki da shi kuma wani ne ya saya ya bada shi haya ga kanikawa ga masu sayar da abinci da kuma kayan aikinsa da suka dogara da masu sana’ar. A cikin unguwannin rukunin gidajen nan da suke magana, Gwarimpa ce kadai ke da yanayin aikin a daukacin birnin Abuja. Kuma da yawa daga cikin yara ’yan makaranta da sauran masu kananan sana’o’i a unguwar sun dogara ne da Keken wajen zirga-zirgarsu. Sauran unguwannin da suke magana yawancin mazauna wuraren ba su bukatar aikinmu saboda suna da motoci da suke daukar iyalansu. A wasu wuraren ma masu unguwannin korarmu suke yi,” inji shi.
Ya ce wannan ya sa suka gwammace dakatar da sana’arsu a daukacin birnin a ranar ta Talata ko za su samu fahimta a tsakaninsu da hukuma.
Sai dai a yayin zantawarsa da Aminiya Wadata Aliyu Bodinga ya ce babu gudu babu ja da baya a kan kudirinsu na tabbatar da fara aiki da dokar.