Abin da ya sa muka tsoma jama’a a harkar farfado da ilimi – Ganduje

A hanyar Gwarzo za ka ga madatsun ruwa da yawa, ba ruwan sha suke badawa ba, ba noman rani ba. Ba mu ga wata hanya da za a yi amfani da madatsun da aka kashe kudi wajen yinsu ba ta yadda za a yi noma a matsayin sana’a don riba koda yaushe ba sai an […]

Abin da ya sa muka tsoma jama’a a harkar farfado da ilimi – Ganduje
Abin da ya sa muka tsoma jama’a a harkar farfado da ilimi – Ganduje

A hanyar Gwarzo za ka ga madatsun ruwa da yawa, ba ruwan sha suke badawa ba, ba noman rani ba. Ba mu ga wata hanya da za a yi amfani da madatsun da aka kashe kudi wajen yinsu ba ta yadda za a yi noma a matsayin sana’a don riba koda yaushe ba sai an jira ruwan sama ba, kamar yadda muke gani a kasashen waje. Akwai wannan shiri da kuke yi?
kwarai da gaske. Shirin da muka fara yi shi ne, mu samu alkaluma da yanayin kowane dam da muke da shi. Muna da dam-dam, wasu muna aikin wutar lantarki a kai, tun wancan gwamnati muna aikin samar da wutar lantarki a kansu duk da yana cin kudi, amma mun yarda yana da amfani sosai, mun ci gaba da aiki a kansa. Akwai wasu madatsun da su kuma ana ba da  ruwan sha ne, akwai wadanda yadda ka fada din ba a komai da su.  
To yanzu mun dauki alkaluma a kan wannan, kowane dam mun dauki yanayinsa, muna da littafi wanda muka yi a kan wannan. Amma abin da muke nema shi ne, mutanen da za su shigo a ci gajiyar wadannan madatsu. Domin gwamnati ita kadai ba za ta iya yinwannan ba, kuma mutane da yawa masu sha’awa suna zuwa muna tattaunawa da su. Muhimmin abu shi ne idan akwai sha’awar yin noma, idan kuma an ga noma harka ce wacce take za ka samu kudi, to wannan magana nan za ta shigo. Alal misali yanzu Gwamnatin Tarayya ta yarda cewa a ci gaba da shigo da alkama da shinkafa Najeriya.
Duk wanda zai shugabanci Najeriya yanzu, ya san wannan abu ba za a ci gaba da shi ba, in kuwa an ci gaba da shi, to da ma ba ma so Najeriya ta ci da kanta. To mu a Kano, mun ga wannan haske, sai muka kira duk mai sha’awar noman alkama ya zo, duk mai noman shinkafa ya zo, sannan muka kirawo kamfanoni masu sarrafa alkama, muka ce su kuma mece ce matsalarsu. Sun tabbatar mana cewa alkamar da ake nomawa yanzu a Jihar Kano nagartarta ta kai alkamar da ake shigowa da ita. Su kuma manoman alkama muka ce, to, ga masu sayen alkama sun yi alkawarin duk alkamar da kuka noma za su saya, ku kuma mece ce matsalarku? Suka ce babbar matsalarsu ita ce iri mai inganci da kudin da za su sayi iri mai inganci. Muka ce in wannan ne ku kwantar da hankalinku, muka kawo Naira miliyan 100 muka ajiye.
A yanzu muna da manoman alkama fiye da dubu biyar wadanda suka karbi wadannan kudi a matsayin bashi ba kyauta ba. Sun sayi wannan iri suna nomawa, abin da muke sa idonmu a kai shi ne, muddin wannan abu ya yi nasara, masu noman alkama za su taho a guje domin sun san akwai riba. Idan sun yi haka, wadannan madatsun ruwa namu za ka ga cewa dole an fito da hanyoyin da za a yi amfani su. Mutanen da suke son zuba jari a noman alkama za su zo mu daidaita da su. Amma muddin za ka noma abinka babu mai saye to akwai mishkila.
Masu noman shinkafa yanzu ake girbin shinkafa, muka ce ku kuma mece ce matsalarku? Suka ce matsalarmu ita ce tunda shinkafar nan ana shigo da ita, kada shinkafar da muka noma ya zamana ba za a saya ba. Saboda haka yanzu muna nan muna yin doka za mu dawo da Hukumar Sayen Kayan Amfanin Gona, mun ware Naira biliyan daya saboda sayen shinkafar da aka noma ta yi yawa, a tabbata cewa su manomanta ba su yi asara ba. Kuma akwai lokaci da zai zo gwamnati ma sai ta ci ribar wannan shinkafa. Saboda haka irin wadannan ayyuka ne muka sa a gaba muna yi a cikin wannan gwamnati tamu.
Akwai lokacin da aka bullo da shirin noman alkama amma a karshe aka watsar saboda siyasar duniya, ba ka ganin za a sake maimaita hakan, ko kun yi la’akari da wadannan al’amura?
Ai ka san siyasar duniya tana canjawa. Hulda tsakanin kasa da kasa ya danganta ga Shugaban kasar da yake mulkin wannan kasar. Saboda haka, in an yi nasara a kan wani Shugaban kasa a wani Shugaban kasar musamman Muhammadu Buhari ba na jin wannan zai yi nasara, na daya ke nan. Abu na biyu, masu sayo alkamar nan daga kasashen waje babu dokar da ta ce dole su sayo daga kasashen waje. Idan suka yarda za su sayi alkama a cikin gida, suna sayen alkama a cikin gida ai ka ga wannan ba magana ce ta siyasar duniya ba. Magana ce ta tsakanin mai so ya saya da mai kayan sayarwa. Karya farashinta da ake zargin za su yi ba zai hana wannan yunkuri ba, idan akwai niyyar yin haka din, Gwamnatin Tarayya tana iya kin a shigo da ita.   
Baya ga noma me za ku ba fiffiko?
Akwai batun hanyoyin karkara, domin akwai kauyukan da suke da manyan gonaki ana samun amfanin gona sosai, amma yadda za a fito da shi a kawo kasuwa matsala ce. Saboda haka mun sa kwamiti mai karfi wanda ya zagaya kauyuka, yanzu haka muna da taswirar hanyoyin kauyukan.  Mun fito da taswirar nau’o’in hanyoyi  uku da za mu yi. Akwai kwalta da ake kira nailon, sai kwalta mai kirci-kirci sai ta uku, irin hanyar nan ta karkara da za a yi gada ko kwalbati a  zuba kasa ta yadda akalla komai girman mota za ta shiga kauye ta fito da kaya da sauransu. Sannan can gaba idan kana so ka maida ita mai kirci-kirci ko kwalta nailon dama an samu dababbiyar hanya. Muna ganin fito da wannan zai inganta ci gaban ayyuka da dama. Mun ce a yi mana taswirar rafuffuka da koramai na Jihar Kano don mu ga yaya za mu taimaka wa noman rani, domin akwai ruwa a kasa.
Akwai batun ci bayan Arewacin Najeriya, ku da kuke rike da madafun iko akwai wani abu da kuke yi a tsakanin gwamnoni musamman bayan da aka ga haza kan matsalar Boko Haram?
Babu shakka koma bayan Arewa, mutum mai hankali ya san magana ce ta ilimi. Mu (mutanen Arewa) muna da yawa, kuma idan akwai yawa, to daya cikin biyu zai faru. Kodai ya zama yawanka jidali ne ko kuma yawanka ya zama jari. Kano muna da yawa, Arewa muna da yawa. Saboda haka magana ce ta yawanmu ya zama jidali, maimakon ya zama jari. Saboda haka yunkurin da ake yi, shi ne a ga an rike ilimi sosai, an tallafa wa ilimi yadda yawanmu zai zama jari. Idan ba an yi haka ba, duk wadannan matsaloli da ake samu na Boko Haram shi kansa rashin ilimi ne. Ilimin addinin Musuluncin ma a gurgunce yake, kuma ka yi ilimi ba ka da sana’a, ko dama ilimin da ka yi ba na sana’a ba ne. Saboda ka ga mu Arewa abin da muke dubawa ya zama ilimi daga makarantu firamare zuwa karamar sakandare ya zama wajibi kuma ya zama kyauta. Sannan a ba ilimin koyon sana’a muhimmancin gaske. Na uku, dole ’yan Arewa su dauki ilimi da muhimmanci a kashin kansu ba su bar gwamnati da komai ba. Domin mutum ne za ka ga yana da motoci, yana da gidaje, yana da kamfanoni, in ya kwanta yana ta tunanin jarin da zai samu, amma da wuya ka ga wanda yake tunanin ’ya’yansa kan karatun da suke yi. To in ba mun koma wannan hali na yadda za mu rika kiwon ’ya’yanmu ba, mu tabbatar sun samu ilimi mai inganci. To fita daga wannan hali zai dauki lokaci kwarai da gaske. Dole ne al’umma ta taimaka kan batun ilimi, gwamnati ita kai ba za ta iya wannan ba.
Game da kwamitin ilimi, zuwa wane lokaci ne kake sa ran zai mika maka rahoto kafin ka dauki matakin da ya dace?
Wato maganar kwamitocin da muka kafa kan inganta cin gaban ilimi, mun bullo da shi  ne yadda al’umma za su shiga harkar farfado da ilimin. Mun lura cewa a Arewa, misali idan iska ta dauke rufin kwano mutanen wannan kauye da duk ’ya’yan da suke karatu a makarantar ’ya’yansu ne, maimakon su duba yadda za su mayar da wannan kwano, sai su zo suna wawa a kan daukar wannan kwano. To ka ga akwai mishkila a nan, akwai rashin damuwa a nan.
Saboda haka muka kafa kwamiti a kananan hukumomi muka ba su hotunan makarantun kananan hukumominsu da suka lalace, kuma ’ya’yansu ne suke wadannan makarantu, muka ce su je su yi tunani yaya za a yi su taimaka a gyara wadannan makarantu. Mu daga gwamnati kowane kwamitin karamar hukuma mun ba shi Naira miliyan 10, ku kuma ku je a tsakaninku da wadanda suke aiki a karamar hukuma da wadanda suke aiki a jiha da wadanda suke aiki a sassan Najeriya zuwa kasashen waje da sojoji da ’yan kasuwa da wadanda suka yi ritaya da sauransu, ku je ku zauna a karamar hukumarku kuka ga yaya za ku taimaka a zo a gyara makarantun.
Mun ba su wannan kuma kowane wata za  mu yi taro da su kai-tsaye kwamitin ya fadi na  gyara kaza, na gyara kaza. Abin da ya sa muka ce mutane su shigo ba abu ne mai wahala ba, abu ne na zuciya, idan kana da niyyar za ka taimaka za ka taimaka. Misali ka je ka tadda babu taga, ko kwano ya tashi, ba maganar kwangila ba ce.
Idan ka samu kafintan kauyen zai iya gaya maka cewa kwano 10 ne za mu sa a nan, amma idan ka je ka ba mai kididdigar gini, sai ya ce maka wannan wuri zai ci bandir 30 kuma ka sa kudi ka sayo bandir 30. Na biyu, idan ka zo yin wannan aiki a kauyen ai akwai kafinta a kauyen zai iya cewa zai yi aikin nan kyauta ko a biya ni rabin kudin. Haka in babu dabe a aji magini zai iya cewa a biya shi rabin kudin ya yi aikin.
Wani zai iya cewa zan je bakin rafi in dauko yashi a yi wannan aiki, ba sai an samu katuwar tifa an rubuta maka cewa za a biya ta kaza ba. Nan bakin rafi watakila tifa ba za ta iya zuwa ba, amma jakinsa zai je. Wani zai ce zan kawo ruwa tunda dai wannan makaranta duk ’ya’yanmu ne a cikinta. Wanda ba ya da lokaci amma aljihunsa yana da nauyi zai iya cewa ba ni da lokaci, amma ga wannan (ya ba da kudi). To wannan dabi’a muke so mu raya, domin shi ne Bature yake kira tabbatar da dorewar ci gaba.
In wani abu ya lalace ba sai an jira gwamnati ba, ’yan gari za su hadu su gyara saboda suna da kishin abin. Amma idan da farko ka ce mutane su je su yi, masu iya magana sun ce da na gaba ake gane zurfin ruwa, don haka gwamnati muka yi yunkuri muka ce ga Naira miliyan goma-goma ga hotunan makarantunku da ba su da kyau, amma za ku zo ku ba mu bayani. Kuma za mu fito da gasa a tsakanin kananan hukumomi, wace karamar hukuma ce ta fi amfani da wannan kudi a hanyar da ta fi dacewa? Wace karamar hukuma ce ta fi aiki mai nagarta? Wace karamar hukuma ce al’ummar yankinta suka fi bayar da taimako a kan ci gaba da yin wannan aiki? Za mu ba da kofi a kan wannan.
Idan aka gama da wannan sai a koma a dubi batun kayayyakin koyarwa, shin akwai wadannan kayayyaki? Akwai malaman da suke shiga ajujuwa su koyar? Wannan kwamiti zai rika zagayawa yana dubawa ya gani, a rajistarku kuna da malamai 20, amma nan mun ga guda bakwai ina sauran? Saboda haka wannan hanya da muka dauko hanya ce da muke ganin za ta bunkasa ilimi idan aka dauki lokaci ana bin ta.
Akwai ’yan Jihar Kano da aka kama a kasar Indiya bisa zargin ’yan ta’adda ne, an ce an dawo da su Najeriya, mene ne gaskiyar batun?
Wannan magana ba gaskiya ba ne. Akwai yara da aka kama za su haura zuwa wata kasa, saboda haka sai aka ce ai yara ne masu ta’addanci. Ta yiwu haka ne, ta yiwu ba haka ba ne. Amma gaskiyar magana suna son su haura daga wannan kasa zuwa waccan kasa. Saboda haka da muka je Indiya an kawo batunsu, an ce mu je mu yi belinsu mu fito da su. Muka ce ai gwamnati ba haka take ba, sai mun duba shin me ya kawo su wannan kasa, kuma wadanne dokokin wannan kasa suka karya?
Idan sun karya dokokin wannan kasa ba hakkin jiha ce ta ce za ta yi belinsu ba, domin mu ma kanmu muna son idan ’yan kasashen waje sun zo su bi dokokin kasarmu. Irin amsar da muka ba su ke nan, amma ba a tabbatar da ko su ’yan ta’adda ne ko ba ’yan ta’adda ba ne. Wasu ’yan jarida ne suka dauki wannan suka dora musu.
Lokacin da kuka je an dawo da su?
 Lokacin da muka je ba a dawo da su ba.
Amma wasu za su ce ai ’yan jiharku ko ba ku kuka kai su ba?
kwarai kuwa, ko dan jihata ce idan ka yi laifi ba zan yi belinsa ba, kai ko dana ne.