Abin da ya sa muka yi yajin aiki – Dokta Dauda Yusuf

Dokta Muhammed Dauda Yusuf shi ne sabon shugaban kungiyar Likitoci ta kasa reshen Jihar Bauchi a tattaunawarsu da wakilinmu ya yi tsokaci kan halin da mambobin kungiyar suke ciki a Bauchi da kuma dalilin da ya sa suka shiga yajin aiki a kwanakin baya: Ko z aka gabatar mana da kanka?Sunana Muhammed Dauda Yusuf sabon […]

Abin da ya sa muka yi yajin aiki – Dokta Dauda Yusuf
Abin da ya sa muka yi yajin aiki – Dokta Dauda Yusuf

Dokta Muhammed Dauda Yusuf shi ne sabon shugaban kungiyar Likitoci ta kasa reshen Jihar Bauchi a tattaunawarsu da wakilinmu ya yi tsokaci kan halin da mambobin kungiyar suke ciki a Bauchi da kuma dalilin da ya sa suka shiga yajin aiki a kwanakin baya:

Ko z aka gabatar mana da kanka?
Sunana Muhammed Dauda Yusuf sabon shugaban kungiyar Likitoci ta kasa reshen Jihar Bauchi, kuma ina aiki ne a asibitin Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Abubakar Tatari Ali da ke nan Bauchi.
Kwanakin baya ne muka gudanar da zaben shugabannin wannan kungiya inda aka zabe ni a matsayin shugaba da masu rufa mini baya.  Likitoci suna da matukar mahimmanci a tsakanin al’umma, kamar yadda ba za mu taba rayuwa ba sai da hukumomin tsaro haka babu wata al’umma da za ta rayu sai tana da likitoci masu ilimi da sanin ya kamata.  Bayan haka za mu ci gaba da aiki da ma’aikatar lafiya ta Jihar Bauchi tare da sauran kungiyoyin da suke bada tasu gudunmawa wajen inganta rayuwar al’umma. Idan aka duba da yawa daga cikin mutanen karkara suna fama da karancin likitoci da suke da kwarewa a fannin kiwon lafiya.
Wadanne hanyoyi za ku bi wajen inganta rayuwar likitocin Jihar Bauchi?
Kamar yadda kowa ya sani babban abin da wannan kungiya ta sa a gaba shi ne inganta rayuwar mambobinta wato likitoci. Tsohon shugaban wannan kungiya Dokta Yusuf Abdu Misau ya yi aiki tsakani da Allah wajen hada kan ’ya’yan wannan kungiya. Kuma zan ci gaba da ayyukan alheri kamar yadda na gani a lokacin da yake rike da shugaban wannan kungiya. Kuma kofata a bude take domin karbar koke-koke domin ta haka ne za a samu ci gaba mai amfani.
Mene ne sakonka ga ’ya’yan wannan kungiya a Jihar Bauchi?
Babban sakona ga ’ya’yan wannan kungiya shi ne ya kamata kowa ya gyara halinsa sannan mu ci gaba da yin hakuri a lokutan da muke gudanar da ayyukanmu. Sannan zan yi amfani da wannan dama domin yin kira da babbar murya ga gwamnatin Jihar Bauchi a karkashin shugabancin Malam Isa Yuguda da ta taimaka wa wannan kungiya da ofis domin a halin yanzu ba mu da ofis mallakarmu. Kuma za mu rubuta wa masu hanu da shuni su taimaki wannan kungiya na likitoci domin kowa ya san irin gudunmawar da muke bayarwa wajen inganta kiwon lafiya.
Me za ka ce kan sabuwar cutar nan ta Ebola?
To, kamar yadda kowa ya sani ne cutar Ebola ta hallaka dubban jama’a a kasashen Liberiya da Saliyo da Guinea kuma daga bisani ta shigo Najeriya. Babban abin da zan fada wa al’umma shi ne mu rika kula da tsabtace abubuwan da muke ci. Bayan haka a rika wanke hannu da sabulu ko toka da zarar an fito daga bayi. Wannan shi ne mataki na farko da ya kamata kowa ya yi amfani da shi wajen kare kansa daga cutar Ebola.
Me ya sa kusan kullum sai ka ji likitoci sun tsunduma yajin aiki a Najeriya?
Akwai masu cewa gwamnatin Najeriya ba za ta taba biya muku bukata ba, sai an shiga yajin aiki, wannan kungiya ta likitoci da sauran kungiyar suna shiga yajin aiki ne domin kishin talakawa saboda babban bukatar shi ne mu ga an samu tsari na kyautata rayuwar ’yan Najeriya.
Kana da sako ga ’yan Najeriya?
Sakona ga ’yan Najeriya shi ne ya kamata mu zamo masu bin doka da oda, domin bin doka yana haifar da alheri ga ’yan kasa. Bayan haka kowa ya ga halin da muke ciki a yankin Arewa maso Gabas da ke fama da tashe-tashen hankula. Mu fara gyara halayenmu sai Allah Ya magance mana matsalolin tsaro da muke fuskanta, sannan mu guji yada jita-jita a tsakanin al’umma.