Abin da ya sa muka yi yajin aikin bin hanyar Birnin Gwari – Direbobi

Direbobi a Tashar Kawo da ke Kaduna a Jihar Kaduna sun yi yajin aiki inda suka kaurace wa bin hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari. Direbobin sun yi wannan yajin aiki ne a ranar Litinin da ta wuce saboda rasa abokan aikinsu da suke yi kusan kowane mako a sandiyar kashe su da ’yan ta’addan dajin […]

Abin da ya sa muka yi yajin aikin bin hanyar Birnin Gwari – Direbobi

Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna

Direbobi a Tashar Kawo da ke Kaduna a Jihar Kaduna sun yi yajin aiki inda suka kaurace wa bin hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Direbobin sun yi wannan yajin aiki ne a ranar Litinin da ta wuce saboda rasa abokan aikinsu da suke yi kusan kowane mako a sandiyar kashe su da ’yan ta’addan dajin Birnin Gwari ke yi.

A cewar direbobin, a cikin makon jiya sun rasa direbobi da fasinjoji kusan 10 ban da mutane kusan 40 da suka ce barayin mutane sun shiga da su daji.

Wadansu daga cikin direbobin da Aminiya ta zanta da su sun bayyana damuwarsa da kuma dalilin da ya sa suka ga ya dace su kaurace wa hanyar domin janyo hankalin gwamnati da jami’an tsaro a dauki matakin kare rayukansu.

A cewar Umar Dakare wanda daya ne daga cikin direbobin da ke bin hanyar, ya ce a cikin kwana bakwai da suka gabata an kashe musu direbobi shida.

Ya bayyana sunayen wadanda aka kashe da Sai’du Muda da Rufa’i Kwakwato da Lawal Akalo da Sule Mando da Danbiji da sauransu.

“Baya ga wadannan akwai mahauta biyar da aka kashe a cikin motar Sule Mando. Wannan abin ya firgita mu matuka wanda hakan ya sa tilas mu kaurace wa hanyar domin janyo hankalin gwamnati.

Mun kaurace wa hanyar domin hakkin gwamnati ce ta kare rayukanmu. Don haka muke kara yin kira ga gwamnati ta samar da karin jami’an tsaro a kan wannan hanya ta Kaduna zuwa Birnin Gwari,” inji shi.

Ya kara da cewa sojoji da ke aiki a kan hanyar suna matukar kokari amma duk da haka barayin na yin fito-na-fito da su a wasu lokuta a hanyar.

Shi ma Ibrahim Na-Mama wanda direba ne da ke bin hanyar Birnin Gwari  ya kara da cewa dalilin yajin aikin nasu shi ne rashin tsaro.

“Gaskiya cikin kwana bakwai mun yi rashin mutum 10 ciki har da direbobi ban da wadanda suka dauke su zuwa cikin daji. Sakamakon haka sai muka ga kamar gwamnati ta mance da mu, musamman mu direbobi da ke bin hanyar Birnin Gwari. Mun san wannan gwamnati ce ta talakawa, don haka muke roko a taimaka a kara mana jami’an tsaro a hanyar,” inji shi.

Shi kuwa Bala Dogo Direba da Allah Ya kwaci rayuwarsa a ranar Juma’ar da ta gabata bayan barayin sun bude wa motarsa wuta a hanyar, amma babu wanda ya rasa ransa sai mutum daya da suka dauka, ya ce: “Da suka bude wa motata wuta a kusa da wani wuri da ake kira Falwaya, Allah Ya taimake ni na tsayar da mota sai muka shiga daji a guje suna bin mu suna harbi kamar zomaye. Kuma yara ne kanana ke rike da bindigogi suna harbinmu. Mutum daya wani malamin makaranta suka dauka dan Birnin Gwari mu kuma wadansu ’yan sanda da ke kokari wajen kare hanyar ne suka taimake mu zuwa Kaduna. Mu matsalarmu ba kyan titi ba ne, a taimaka a samar mana karin jami’an tsaro a kan wannan hanya domin mu ci gaba da aikinmu.”

Bala Dogo ya kara da cewa akasarin direbobi da ke bin hanyar na cikin damuwa kasancewar ba sa iya bin hanyar domin neman abinci. Ya ce mafi yawansu na da ’ya’ya da mata da suke ciyarwa amma ga shi rashin tsaro ya hana su yin aiki.

Direbobin sun kuma bayyana inda ake yawan yin fashin kamar Unguwar Yaku zuwa Labi sai Falwaya zuwa Kwaga da Gayan zuwa Falwaya da Kwanar Bola da sauran wurare.