Abin da ya sa muka zabi Mu’azu – Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan ya ce an zabi Alhaji Ahmadu Mu’azu a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa ne saboda shi wata gada ce da zai iya kaiwa ga mabobin jam’yyar da aka fusata.Jonathan na magana ne a Abuja a taron musamman na Kwamitin Zartarwa na kasa na PDP bayan shafe dare ana tattaunawa da […]
Shugaba Goodluck Jonathan ya ce an zabi Alhaji Ahmadu Mu’azu a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa ne saboda shi wata gada ce da zai iya kaiwa ga mabobin jam’yyar da aka fusata.
Jonathan na magana ne a Abuja a taron musamman na Kwamitin Zartarwa na kasa na PDP bayan shafe dare ana tattaunawa da gwamnonin jihohi kan zaben wanda zai maye gurbin saukakken shugaban jam’iyyar Alhaji Bamanga Tukur, wanda ya yi murabus a makon jiya.
A lokacin taron, Mu’azu wanda tsohon Gwamnan Jihar Bauchi ne babban abokin gabar siyasarsa Gwamnan Jihar Bauchi Isa Yuguda ne ya zabe shi.
Lokacin da yake zabensa Gwamna Yuguda ya ce kowane irin sabani ke tsakaninsa da Mu’azu yanzu ya zama tarihi sun yanke shawarar su yi aiki tare domin bukatun jam’iyyar.
Ya ce za su karya lagon shugabbanin jam’iyyar da ba su aiki kafada-da-kafada da gwamnonin jihohinsu a baya.
Shugaba Jonathan ya ce, an zabi Mu’azu a kan sauran ’yan takarar ne saboda zai iya shawo kan jama’a tare da kulla abota da wakilan jam’iyyar da aka fusata. Ya ce a yanzu PDP tana bukatar shugaba ne da zai zama gada dinke jama’a da zai dawo da abokansa cikin jam’iyyar, wanda bai dabi’ar nuna girman kai ga saura.
“Mutane sun zo gare ne, wasu ba su ambaci suna ba, amma sun ba da shawarwari, kuma na amince da su cewa abin da muke bukata yanzu shi ne mutumin da zai iya gina jam’iyyar, ya samo abokai, kuma ya shawo kan jama’a. Duk wadanda suka nuna sha’awa sun cancanci mukamin amma abin da ya dora Mu’azu a kansu shi ne jawaban da ake yi kansa cewa yana da dabi’a ta musamman ta son zaman lafiya da yake da dimbin abokai daga Arewa zuwa Kudu daga Gabas zuwa Yamma,” inji shi.
Ya ce Mu’azu dan Najeriya ne marar kabilanci da ba zai yi amfani da kabilanci ko addini don cutar da wasu lokacin da yake mu’amala da jama’a ba. Ya ce PDP tana bukatar mutanen da za su rika karfafa dangantaka ne ba wadanda za su rika “fada, fada, fada” ba.
Ya bukaci sabon shugaban ya kwantar da kurar da ta taso a jihohi kuma ya fadada damar jam’iyyar na lashe zabubbuka, inda ya ce PDP ta rasa zabe a wasu jihohin ne saboda shugabanninta a jihohin sun gaza hada kansu.
Mu’azu, mai shekara 58, ya ce jam’iyyar ta zama abar magana a kwanakin nan, kuma zai yi kokarin dawo da martabarta.