Abin da ya sa muke tallafa wa mata ’yan gudun hijira – Zainab Dalori

Ganin matsalar da mata ’yan gudun hijira da matan karkara suke fuskanta wajen samun audugar kunzugu idan suna al’ada da inda suke amfani da tsumma da hakan ke haifar musu da cututtuka iri-iri, a wasu lokutan ya kai ga hana mace haihuwa ne ya sa Zainab Lawan Dalori, ta kafa gidauniya don kawo wa matan […]

Abin da ya sa muke tallafa wa mata ’yan gudun hijira – Zainab Dalori

Zainab Lawal Dalori a tsakiya da wadansu ma’aikatanta

Ganin matsalar da mata ’yan gudun hijira da matan karkara suke fuskanta wajen samun audugar kunzugu idan suna al’ada da inda suke amfani da tsumma da hakan ke haifar musu da cututtuka iri-iri, a wasu lokutan ya kai ga hana mace haihuwa ne ya sa Zainab Lawan Dalori, ta kafa gidauniya don kawo wa matan dauki, kamar yadda ta shaida wa Aminiya. Matashiyar ta ce burinta taimaka wa mata marasa galihu da kananan yara, ta hanyar gidauniyarta mai suna Zaidal Programme Inneciatibe), ta shaoda wa Aminiya yadda ta assasa gidauniyar da yadda suke taimaka wa mata ’yan gudun hijira da kananan yara wanda har sai da Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya yaba mata:

Me ya ba ki sha’awar tallafa wa mata da yara musamma, ’yan gudun hijira?

Na fara tunanin taimaka wa duk wasu al’amura na mata ne musamman gajiyayyu da suke zaune a yankunan karkara da sansanonin ’yan gudun hijira saboda suna bukatar taimako, kama daga zuwan jinin al’ada da mata suke yi a duk wata da harkokin karatun yara da ciyar da kai da koyar da su sana’o’i ta yadda za su rike kawunansu. Na lura cewa akasari mata da kananan yara suka fi shiga mawuyacin hali idan wani tashin hankali ya faru. Su ke shiga mawuyacin hali ta bangaren ciyarwa da shayarwa da tufatarwa da samun abin yi a lokacin da aka kashe mazansu. To wannan abin ne ya sani  cikin damuwa da bakin ciki, don haka na yi tunanin daukar nauyin wasu matsalolinsu daya bayan daya don in magance masu wasu daga ciki. Abin akwai ban tausayi, sai na yi tunanin kirkiro wannan gidauniya wadda za ta iya duba lamuran mata ta magance a ta yadda zai kasance idan suna da wata matsala a nan da can sai mu yi kokari mu toshe na nan ko na can ko ba a magance matsalar  gaba daya ba, an dai rage. Wannan ne ya sa na kafa  gidauniyar Zaidal Women and Girls Inniciatibe Organisation  wadda za ta rika sanya ido a kan harkokin mata da yara kanana.

Wadanne irin abubuwa gidauniyar take yi don tallafa wa mata?

Eh, wato na yi bincike na gano cewa akasarin matan da ke sansanin ’yan gudun hijira da matan karkara a wasu lokuta har da birane idan lokacin al’adarsu ta zo a wata ana samun matsaloli ta yadda  kan kai ga cutar da su. Don wadansu suna amfani da tsumma, wadansu da auduga, a yayin da wadansu suke amfani da wani abin da bai dace ba. Akasari irin wannan yana haifar musu da cututtuka iri-iri musamman ciwon sanyi. Ganin haka na fara tunanin wacce hanya ce zan samar wa mata su samu saukin kula da al’adarsu ba tare da wata matsala ko cuta ta kama su ba. Sai na yi tunanin samar da abubuwan da za su samu kariya  daga cututtukan da suke samu ta dalilin al’adar, sai na kirkiro wata na’ura da za ta iya saukaka musu lokacin da suke al’ada mai suna Zaidal Diginity Keet. Wannan na’ura tana karkashin wannan gidauniya tamu ta ZAIDAL inda muke fitar da kayan mata nau’o’i 4 zuwa 5 mu bai wa mata su yi amfani da su tsawon wata daya zuwa biyu, ta yadda za su samu kariya kuma babu ruwansu da kamuwa da duk wata cuta.

Shin kina zuwa dakin bincike ne ki gudanar da bincike a kan sinadarin kariyar da kike hada wannan kunshi da shi?

Eh, to na’urar nan dai ba wata aba mai wahala ba ce,  duk abubuwan da aka sani ne irin su sabulu da wasu nau’o’in mai, kuma kafin in fara hadawa sai da na je  masana’antar da suke sarrafawa suka koyar da ni na tsawon mako uku,na zo na yi amfani da ita a gida na ga amfaninta kafin in fitar, in fara raba wa mata. Kuma nakan zabi wadansu daga cikin matan, mu koya musu ta yadda za su iya hadawa da kansu, ya kasance ko da ba ma nan za su iya su hadawa su raba wa kawunansu su yi amfani da su. Na je dakin bincike da dama an gwada kayayyakin da muke amfani da su, an tabbatar suna da inganci kuma sun dace a yi amfani da su domin samun kariya daga cututtuka.

Ta yaya kike samun kudin tafiyar da wannan gidauniya da samar da wadannan kayayyaki?

Lokacin da na fara wannan abin na kai wata 3 zuwa 4 kafin a gane cewa ina samar da su. Sai na zo na hadu da wata kungiya mai suna North-East McArthur da ke karkashin  Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya hada ni da tsohon Gwamnan Jihar Borno  Alhaji Kashim Shettima, shi ke nan sai gwamnatin jiha ta ba mu kwangilar yin dubu 10. To da muka yi sai aka rarraba wa dukkan matan da suke  sansanonin ’yan gudun hijira da ke Jihar Borno, shi ne muka samu damar mikewa muka fara tashi muna takawa tare da taimaka wa matan.

Baya ga kwangilar da gwamnati ta ba ku babu wani tallafi da ta sake ba ku don ku ci gaba da yin wannan abu a sansanonin gudun hijirar da sauran mata na gida?

Lokacin da muka hadu da Tsohon Gwamna Kashim Shettima, na ce masa a gaskiya muna neman a rika taimaka mana duk wata a ce muna sarrafa wannan abu ana raba wa ’yan gudun hijira ko a gidajen matan aure, don  wadansu matan  jinin al’ada na zuwa  mata da yawa wata kuma ba ya zuwa da yawa. Wata zai dauke ta tsawon mako guda, wata kwana 3, sai nake fada masa cewa ya kamata a ci gaba da yin wannan abu a yi ta rarraba wa mata a ko’ina suke. To abin sai bai yiwu ba, har ga shi mun samu canjin gwamnati.

Za ki iya tuna mata nawa kuka koya musu wannan sana’a?

Akwai mata sama da 175 wadanda muka koyar da su wannan abin. Domin mukan dauki mata daga cikinsu sai mu yi musu bayani za mu dauke ku kuma mu biya ku, amma ku sani ya kamata ku koyi wannan abu don gaba zai iya yi muku amfani a duk inda kuke. To a haka mun koya wa mata sama da 175, wadanda yanzu haka za su iya sarrafa wannan abu su kuma raba shi ga sauran mata. Mun shiga sansanonin ’yan gudun hijira na Bakasi da Dalori da Teachers Billage da Bocolis da na Gubio da sauransu. Kuma duk mun koyar musu yadda ake yin wadannan sana’o’i na hannu hade da wannan (Diginity keets) da muke rarrabawa.

Shin akwai wata hanyar da kike tunanin bi don ci gaba da samun tallafi?

To ni dai na san na yi magana da tsohon Gwamna Kashim Shettima, amma har yanzu ban kai ga magana da sabon Gwamna ba tukuna. Saboda  yanzu ne ya  hau sai nan gaba, kuma  Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi iya kokarinsa wajen tallafa mini, sai dai har yanzu muna rokonsa ya ci gaba da sanya mana hannu, kuma muna sanya lambobin wayarmu a kan wadannan kayayyaki da muke rarraba musu don amfanin kansu to suna yawan kiranmu suna nuna mana suna jin dadin abubuwan da muke raba musu don Allah mu ci gaba kada mu bar su. Haka  muke ta fama ba mu da jari ga shi kuma akasarin matan musamman ’yan gudun hijira da mazauna karkara suna bukatar abin, amma ina tsoron kada abin namu ya tsaya cik. Domin idan ba gwamnati ta saka hannu ba, ba za mu iya tafiyar da shi na tsawon lokaci al’umma ta amfana sosai yadda ake bukata ba, ganin ba mu samun wani tallafi daga wuraren da suka kamata a ce mun samu. In ban da kananan sadakoki da muke samu daga masu karamin karfi  ba wata kungiya mai zaman kanta ko gwamnati da take tallafa mana.

Kin taba tuntubar kungiyoyi masu zaman kansu da ke nan Jihar Borno?

Akwai kungiyoyin sa-kai da ba na gwamnati ba (NGOs) da dama da suka yi mana magana kuma har suka zo nan ofishinamu tare da yin alkawarin za mu hada hannu da su wajen inganta rayuwar al’umma, amma har yanzu muna jira.

Kin yi maganar kuna koyar da sana’o’i ga mata da yara, wadanne sana’o’i kuke koyarwa?

Muna kokarin koya musu sana’o’in hannu irin su dinki da saka da yin sabulu da turaren wuta da taliya da dinkin huluna. A tsakanin yara muna kokarin  koyar musu da karatu da sana’o’in hannu.

Kina da ma’aikata nawa?

Ina da ma’aikata 15 da likitoci 2, sai wadanda muke tuntubarsu idan bukatar hakan ta taso.

Ko kin taba fuskantar kalubale tun fara gudanar Da wannan lamari?

Na fuskanci kalubale da daman gaske, kamar na rashin samun goyon bayan da muke bukata. Har yanzu ba mu samu kashi 15 cikin 100 na goyon bayan kungiyoyi da gwamnati da sauran al’umma da muke nema ba. Don wadansu sun kasa gane abin da muke nufi na inganta rayuwar al’ummar karkara, to kuma in ka zauna kawai ba ka yin komai shi ne ma abu zai zo ya dame ka, amma kana kallon abin da zai kari al’umma don wani ya ki tashi ya yi saboda tsoron maganganun mutane, kai bai kamata ka ki tashi ba. To wannan shi ne babban kalubalen da muke fuskanta na rashin samun hadin kai da goyon baya. Abu na biyu shi ne rashin kudin gudanarwa, domin wani lokacin muna ji muna gani rashin kudi yana durkusar da burinmu na inganta rayuwar al’umma, wani lokacin ma ba na samun zarafin biyan ma’aikatana albashinsu. Su ne kawai suke zuwa su ga cewa aikinmu ya tafi daidai yadda muka tsara.

A karshe wane kira kike da shi ga gwamnatin Jihar Borno da ta Tarayya?

Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Borno su agaza mana musamman abubuwa irin na mata, domin idan aka ce mace to ya shafi kowa saboda idan ba ka da ’ya mace to kana da matar aure, to kuma mu mata muna da rauni sai an rika yi ana tagaza mana sannan za mu mike. Ko ta wajen tarbiyyar yara ne mace ita ce kan gaba, saboda haka idan aka taimaka wa mata babu ko shakka za a samu  nasarar rike gida. Don haka ina rokon gwamnatocinmu su taimaka wa kungiyoyin mata don ci gaban al’umma.