Abin da ya sa muke yi wa kasa addu’a duk farkon shekarar musulunci – Sheikh Dahiru Bauchi
Sanannen Malamin addininin Musulucin nan kuma jagora a Darikar Tijjaniyya, kuma Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatwa na Majalisar Koli kan Harkokin Musulunci ta Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana alfanun shekara da watannin Musulunci da kuma dalilin da yake jagorantar yi wa kasa addu’ar zama lafiya duk farkon shekara: Duk sabuwar shekarar Musulunci Shehi […]
Sanannen Malamin addininin Musulucin nan kuma jagora a Darikar Tijjaniyya, kuma Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatwa na Majalisar Koli kan Harkokin Musulunci ta Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana alfanun shekara da watannin Musulunci da kuma dalilin da yake jagorantar yi wa kasa addu’ar zama lafiya duk farkon shekara:
Duk sabuwar shekarar Musulunci Shehi yakan kira taron zikirin shekara, ko mece ce fa’idar yin haka?
Alhamdulillahi! Duk farkon shekarar Musulunci wato watan Almuharram mukan shirya wannan zikiri. Mukan fara a nan Bauchi, sannan Juma’a ta biyu mu yi a wani waje, Juma’ar karshe kuma mu yi a Abuja. Ubangiji Yana cewa Lailaha ilalllahu babbar katanga ce, duk wanda ya shige ta ya huta da azaba, muna gabatar da wannan Lailaha Illallahu mu sa Najeriya a cikin wannan babbar katanga don Allah Ya kiyaye mu Ya kiyaye mana kasarmu daga dukan fitina. Kuma za mu fuskanci sabuwar shekarar da Lailaha Illallahu sannan mu roki Allah Ya Yafe mana zunuban da muka aikata bara, abubuwan da muka yi na lada kuma Allah Ya karba, sabuwar shekarar da muka shiga kuma Allah Ya sa mun shiga da alheri ta zama shekarar alheri, shekarar zama lafiya da kwanciyar hankali. A lokacin taron mukan gayyaci dukan Musulmi domin Laillaha Illallahu kayan dukan Musulmi ne, mu zo mu yi zikiri tare a saurari jawabai kuma a roki Allah tare.
Ko Shehi zai ba mu takaitaccen tarihin shekarar Musulunci?
Lokacin da Annabi (SAW) ya bayyana ba a ajiye tarihin shekarun Musulunci a wancan lokaci ba sai dai ana cewa shekarar yakin kaza ko shekarar kaza da wani abu ya faru amma babu tarihi guda daya ajiyayye.
Haka dai har lokacin Sayyidina Umaru ya karba, bayan ya yi shekara biyu sai ya kira taro ya ce jama’a musifu suna faruwa muna cewa Sha’abana! Sha’abana!! to wani Sha’aban ke nan cikin sha’abanonin? Sha’aban na bana ko na bara ko na badi ya kamata mu ajiye tarihi, dama an ce a shawarci al’umma cikin al’amura. Sai aka yi shawara; wadansu suka ba da shawara cewa a ajiye tarihin Musulunci daga lokacin da aka haifi Manzon Allah Annabi Muhammadu (Sallalahu Alaihi Wasallama), wadansu suka ce lokacin da aka haife shi ai ba a san shi ne ba, wadansu suka ce a sa lokacin da aka aiko shi, wadansu suka ce lokacin da aka aike shi ai ba a riga an daidaita da jama’a ba. Sai Sayyidina Usmanu da sauran wadansu sahabbai suka ce a sa lokacin da ya kaura ya koma Madina. Shi ne aka sa farkon tarihin Musulunci ya fara daga lokacin da ya kaura daga Makka ya koma Madina ta zama daya ga Almuharram.
Ko me Malam zai ce kan batun hadin kai a duniyar Musulmi ganin halin da Musulmi suke ciki a yau?
A tsakanin Musulmi dama Allah Ya halici mutane da haka daga farko Allah Ya ce “Ba Mu halicci mutum da aljan ba sai don su bauta Mini.” Sai kuma aka samu ayar da take cewa mutane ba za su gushe ba suna ta sabani da junansu sai dai wadanda Allah Ya yi wa rahama domin haka aka halicce su ba a halicci mutane don su hada kai gaba daya ba, sai dai Allah Ya ba da umarni mu Musulmi mu yi riko da igiyar Allah baki dayanmu, mu kankame mata kada mu rarraba. Amma duk da haka abin da Allah Ya yi nufi kullum shi ne yake tabbata, kullum ana cikin sabanin tsakanin Musulmi, haka kuma tsakanin Kirista da Kirista ma akwai sabani. Haka Allah Ya yi nufin mutane da yin sabani.
Wane sako Malam ke da shi ga al’ummar Musulmi?
Na farko dai ina kira ga Musulmi mu roki Allah Ya yi mana gafarar dukan zunuban da muka aikata cikin shekarar da ta wuce, kuma mu roki Allah Ya yafe mana laifuffukan da muka aikata, mu roki Allah Ya karba mana ibadun da muke yi. Allah Ya kawo mana zama lafiya da kwanciyar hankali a kasashenmu.
Ina kira ga Musulmin Najeriya da na duniya gaba daya mu yi addu’a Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya. Duk inda Musulmi suke kuma Allah Ya taimake mu sannan mu rika mutunta addini. Kana Kirista ka sani Musulmi yana da addini ka mutunta addinina, haka kai Musulmi ka sani Kirista yana da addini ka girmama addininka ka mutunta addininsa. Addinin Musulunci addini ne na tsoron Allah da zama lafiya, sunansa ma Islam, shi kuma Kirista addininsa addini ne na tausayi da mai addinin tausayi da mai addinin zama lafiya ai bai kamata suna fada ba, kai mai tausayi za ka zauna lafiya da kowa ballantana mai zaman lafiya, kai mai zama lafiya za ka zauna lafiya da kowa ma ballantana mai tausayi. A daina zuga mutane suna kashe junansu don biyan bukatar wasu ‘yan tsiraru.