Abin da ya sa mutanen Turkiyya ke son Shugaba Erdoğan

TarihiAn haifi Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a ranar 26 ga watan Fabrairu shekarar 1954, mahaifinsa sojan da ke tsaron bakin teku ne. Shugaban ya yi tallan tsimi. Ya yi karatun jami’a kuma kwararren dan wasan kwallon kafa ne, inda kungiyar Fenerbache ta nemi ya buga mata wasa, amma mahaifinsa ya hana shi.Ya auri Amina […]

Abin da ya sa mutanen Turkiyya ke son Shugaba Erdoğan
Abin da ya sa mutanen Turkiyya ke son Shugaba Erdoğan

Tarihi
An haifi Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a ranar 26 ga watan Fabrairu shekarar 1954, mahaifinsa sojan da ke tsaron bakin teku ne. Shugaban ya yi tallan tsimi. Ya yi karatun jami’a kuma kwararren dan wasan kwallon kafa ne, inda kungiyar Fenerbache ta nemi ya buga mata wasa, amma mahaifinsa ya hana shi.
Ya auri Amina Gulbaran, wadda suke da ’ya’ya hudu kuma yana bin darikar Sufanci ne na Nakshbandi.
Siyasa
Ya zama magajin Garin Istanbul, an tsige shi sannan aka jefa shi kurkuku na watanni 10 don ya rare kasidar da ke cewa: “Masallaci ne barikinmu, Rufin masallaci ne hular mu, tsinin hasumiya takobinmu Muminai su ne ne sojan mu”. Bayan an haramta jam’iyyarsa, da ya fito sai ya kafa wata sabuwar jam’iyyar AKP a shekarar 2001 kuma ta ci zaben ban mamaki wato kifa-daya-kwala a shekarar 2002 sannan abokinsa Abdullah Gul ya zama Firaminista sannan ya yi masa afuwa abin da ya sa ya dawo siyasa.
Farin jininsa ga jama’a
“Fada-da-cikawa” ya sa bayan an zabe shi a matsayin Magajin Garin birnin Istanbul (1994-98) ya magance matsalar ruwan famfo, da kawar da shara, ya rage cinkoson a tituna ta hanyar gina sabbin hanyoyi da gina gadoji 50, ya kara yawan tashoshin jiragen sama daga 26 zuwa 50, ya hana cin hanci, ya biya bashin Dala biliyan biyu da ake bin birnin Istanbul, sannan ya tara Dala biliyan hudu. Hakazalika, ya kulla yarjejeniya da kurdawa masu dauke da makamai, ya gina hanyan jirgin sama mai gudan gaske, ya rage karfin soja a harkokin siyasa da yin ba-sani-ba-sabo ga masu tauye harkar shari’a, ya yi hadaka da Shehun Malami Fethullah Gulen dan kasar Turkiyya wanda ke zaune a Amurka don ci gaban kasa. Ya haramta kungiyar ’yan madigo da luwadi, ya mayar da gidajen Yahudawa da Kiristoci da aka kwace a shekarar 1930 wanda darajar su ta kai Dala biliyan biyu, ya hana tallan giya, sanna ya haramta kwankwadanta a shekarar 2013, kuma ya haramta zubar da ciki.
Tattalin arziki
Ya inganta masana’antu. Ya kara kudin ajiya na kasa daga Dala miliyan 600 zuwa Dala biliyan 48. Bayan ya zama shugaban kasa, ya gaji bashin Dala biliyan 23 ya rage shi zuwa kasa da Dala biliyan daya. Ya daina karban bashi daga Bankin Duniya. Ana iya cewa Allah-wadan-naka-ya-lalace, don namu suna kuriciyar bera, amma shi gwarzon ya tabbatar da cewa kwalliya ta biya kudin sabulu don ya yi shagube ga Bankin Duniya inda ya ce bankin na iya karbar bashi daga kasar Turkiyya. Babban bankin kasar Turkyiya ya samu kudi mara ciwon-kai wato rarar kudin ajiya a shekarar 2002 daga kudi Dala biliyan 26 zuwa Dala biliyan 92 a shekarar 2011. Hakan ya sa talauci ya ragu daga kashi 32 zuwa kashi 9 cikin 100 a shekarar 2004.
A shekarar 2012 kuwa, a cikin kasashen Turai 27, ta kasance ta shida a cikin wadanda ba abin jama’ar ta bashi, wato suna da arziki da kuma rashin gibin kasafin kudi.
Dangantakarsa da ’Yan kwadago
Ya hana bambanci tsakanin maza da mata, da bambancin addini ko siyasa. Ya inganta tsarin fensho.
Inganta harkar ilimi
Ya sa ma’aikatar ilimi ta fi ta tsaro samun kudi daga Lira biliyan bakwai da rabi a shekarar 2002 zuwa Lira 34 a 2011.Ya sa dokan dole dan kasa ya yi karatun shekara 12 maimakon shekaru takwas. Ya raba wa ’yan makaranta takardun guraben karatu kyauta. Aka gina jami’a a ko wane yanki na kasar, inda suka karu daga guda 98 a shekarar 2002 zuwa guda 186 a 2012. Ya kuma cika alkawarin da ya dauka na zabe, inda ya raba kwanfutoci kyauta ga dalibai.
Fannin Kiwon Lafiya
Ya inganta asibitocin gwamnati domin jin dadin jama’a. Ana duba ’yan kasa da shekara 18 kyauta. Ya ce kowa ya bi layi a asibiti, ya hana karrama ma’aikatan gwamanti don ba sa bin layi. Ya hana shan taba a bainar jama’a.
Siyasar Duniya
Ya zargi kasar Amurka da Isra’ila a shekarar 2013 da yunkurin haddasa bore. Ya ce zai dauki mataki kan Mataimakin Shugaban Amurka Mista Joe Biden don ya yi masa kazafin cewa yana tallafawa ’yan kungiyar ISIS. Hakan ya sa Mista Biden ya nemi afuwa.
A shekarar 2015, sanatocin Amurka 74 suka aika da wasika ga Sakataren Harkokin Waje, John Kerry cewa Erdoğan ya na kaucewa akidojin Demokradiya. Watanni biyu da suka wuce tsofaffin Jakadan Amurka Morton Abromowitz da Eric Edelman da suka taba yin aiki a Turkiyya, sun rubuta hakan ne a jaridar Washington Post inda suka ce: “…Dimokradiyya ba za ta wanzu ba a Turkiyya a karkashin shugabancin Erdoğan a yanzu don an hana ’yancin fadin albarkacin baki da tauye shari’a.”
Iya Magana
An ce “Magana jari ce”. Lallai Erdoğan ya iya magana don lokacin da aka zarge shi: Yana son yin mulikiya ne, sai ya ce: “Yana son ne ya zama kamar sarauniya Elizabeth ta Biritaniya” don tun ba a haife shi ba take mulki. An bashi lambobin girmamawa guda 36, digirorin girmamawa 38 da makullan birane uku.
 Bugu da kari wannan yunkurin juyin mulki ba shi ne na farko ba. An taba shirya yi masa juyin mulki da aka yi wa lakabi da “Guduma”, amma abin bai yi nasara ba. Na bayan nan shi ne na ran 15 ga wannan watan nan, inda ya ce ta sakon wayar hannu cewa jama’a su fito kan titi don dakile juyin mulkin, kuma jam’a suka karba kiran Shugaba  Recep Tayyip Erdoğan. Hakan ta sa ake yi wa yunkurin lakabi da cewa da suna “Juyin Mulki ta hanyar Wayar Salula”. Lailai ta zama salula ga sojan da ba sa son wanda jama’a suka zaba. Duk wanda yunkuri da ake son yi shi ne don yana gina kasarsa, ba ya cin bashi, sannan ya ce tun da mutanen kasar na son Musulunci, to ba ja da baya.