‘Abin da ya sa na ɗaure ɗana cikin dabbobi’

Jibril Aliyu ɗan shekara 10 da ke Unguwar Badariya Birnin Kebbi, mahaifinsa tare da kishiyoyin mahaifiyarsa sun ɗaure shi tsawon shekara biyu tun bayan rasuwar mahaifiyarsa. Jibril yana ɗaure tare da dabbobin gidan, abincin dabbobi yake ci da kuma bayan gidansa kafin hukumar kare haƙƙin bil Adama da ƙungiyar lauyoyi mata mai suna FiDA reshen […]

‘Abin da ya sa na ɗaure ɗana cikin dabbobi’

Jibril Aliyu ɗan shekara 10 da ke Unguwar Badariya Birnin Kebbi, mahaifinsa tare da kishiyoyin mahaifiyarsa sun ɗaure shi tsawon shekara biyu tun bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Jibril yana ɗaure tare da dabbobin gidan, abincin dabbobi yake ci da kuma bayan gidansa kafin hukumar kare haƙƙin bil Adama da ƙungiyar lauyoyi mata mai suna FiDA reshen Jihar Kebbi suka samu labarinsa.

Wakilin Aminiya ya zanta da shugaban hukumar kare haƙƙin bil Adama ta ƙasa reshen Jihar Kebbi Barista Hamza Attahiru kan lamarin a matsayinsa wanda ya jagoranci kuɓutar da yaron.

Barista Hamza ya ce a ranar Asabar da ta gabata ce da misalin ƙarfe 8:30 na dare wani abokin aikinsa wato Barista Dagalo ya kira shi yake faɗa masa cewa ya samu labarin an ɗaure wani yaro a turke don kishiyoyin mahaifiyarsa sun ce yaron ya samu taɓin hankali.

“Na ce masa mu haɗu ranar Lahadi sai na same shi a ofis daga can muka je muka sanar da D.P.O ya ba mu ’yan sanda uku ciki har da mace ɗaya muka tafi gidan.

“Barista ne ya san gidan da muka je mace ’yar sanda ta shiga gidan sai ta samu yaron na daure a cikin wata inuwa an yi masa rumfa a fili yake gaba ɗaya yana cikin dabbobi da talo-talo.

“A lokacin da muka je mai gidan ba ya nan ya je garin Ambursa cin kasuwa, hakan ya sa muka tafi da matansa uku da yake aure ofishin ’yan sanda tare da yaron bayan mun kwance shi.

“Bayan mun isa ofishin ’yan sanda aka kira mahaifin yaron ya zo don an kama matansa da ya zo aka riƙe shi.

“Daga nan muka kai yaron asibiti don likita ya duba lafiyarsa, a can ne aka yi wa yaron wanka da aski aka ba shi abinci”, a cewarsa.

Ya ce, “lamarin yaron nan akwai ban tsoro a lokacin da ake yi masa aski, gashin kansa in ya zubo yake ci. Kayan da ake goge masa jini a jiki ma ya dauka ya sa a baki.

Shi komai ya samu abinci ne gare shi, an rikita shi ya koma mahaukaci. Amma dai in ya samu kulawa zai dawo daidai ya riƙa rayuwarsa kamar kowa.

“Abin da kishiyoyin uwar yaron da mahaifinsa suka yi rainin wayo ne domin akwai yara 17 a gidan, amma an ƙyale yaron ya koma dabba.

Da zarar ’yan sanda sun gama bincike za su tura su kotu ba za mu tsaya ba sai mun ƙwatar wa yaron haƙƙinsa”, inji shi.

– ‘Ba shi da hankali ne’

Mahaifin yaron Malam Aliyu ya ce yaron yana fama da rashin hankali, kuma ya yi iyakar ƙoƙarinsa har abun ya fi ƙarfinsa. 

Yanzu dai yaron yana Asibitin Sir Yahaya Memorial Hospital a Birnin Kebbi.

Babban Sakatare kuma Shugaban Asibitin, Dakta Aminu Bunza ya ɗauki nauyin magani, sannan ya saya wa yaron abinci da kayan sawa.

Gidauniyar bayar da tallafi ga marasa ƙarfi ta Zaki’s Gem ta tallafa masa da kayan wanka, wanki da abinci kuma sun yi niyyar ci cigaba da ba shi abinci kullum a zamansa asibiti.

Shugabar Gidauniyar Hajiya Nafisa Zaki ta yi kira ga mata su ji tsoron Allah.

“Mu tuna cewa Allah Ya ba mu yara matsayin amana kuma ranar lahira zai tambaye mu alhakinsu, ya kamata mu kula”, inji ta.

– Gwamnati za ta ci gaba da kula da shi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ɗauki nauyin kula da yaron da karatunsa gaba ɗaya kamar yadda mai ba gwamna shawara kan mata da cigaban al’umma Hajiya Zara’u Wali ta sanar jim kaɗan bayan ta ziyarci yaron a asibiti.

Ta nuna rashin jin daɗin Gwamnan Kebbi kan  lamarin da ya faru, sannan ta yi kira ga Majalisar Dokokin jihar ta gaggauta yin dokar kare haƙƙin yara don magance irin wannan lamari.

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

1.5bn kaɗai aka sanya a asusunmu — Tsohon Kwamishinan Sakkwato