Abin da ya sa na agaza wa ‘ya’yana mata 4 suka zama likitoci -Malam Sa’idu

Malam Sa’idu Bala malami ne, kuma dan siyasa, haka kuma dan kasuwa ne a Kano, duk da cewar bai yi karatun boko a farkon rayuwarsa ba hakan bai hana shi tsayawa tsayin daka don ganin dukkanin ‘ya’yansa sun sami ilimi, inda har ‘ya’yansa mata guda hudu suka zama likitoci ba. A tattaunawarsa da Aminiya ya […]

Abin da ya sa na agaza wa ‘ya’yana mata 4 suka zama likitoci -Malam Sa’idu

????????????????????????????????????

Malam Sa’idu Bala, mahaifin mata Likitoci huduMalam Sa’idu Bala malami ne, kuma dan siyasa, haka kuma dan kasuwa ne a Kano, duk da cewar bai yi karatun boko a farkon rayuwarsa ba hakan bai hana shi tsayawa tsayin daka don ganin dukkanin ‘ya’yansa sun sami ilimi, inda har ‘ya’yansa mata guda hudu suka zama likitoci ba. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana irin gwagwarmayar da ya yi wajen neman ilimi da kuma sauran al’amuran rayuwa. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya:  Za mu so sanin takaitaccen tarihin rayuwarka.
Malam Sa’idu Bala: Kamar yadda aka sani, sunana Sa’idu, sunan mahaifina Haruna, Bala yayana ne. An haife ni a unguwar Makwarari gidan Alhaji Ali a shekarar 1928. An sa ni a makarantar allo inda na yi karatun Alkur’ani a hannun Malam AbdulYassari  a unguwar kwalwa. Baya ga karatun Alkur’ani na yi karatun litattafan addini a wurinsa. Daga baya sai ya hada ni da malamansa, irinsu Shehu Mai hula da Malm Tijjani Zangon Barebari. Bayan wannan na yi karatu a wurin malamai da dama. Na yi karatu har  a Ibadan da kuma kasar Ghana.
Ban san komiai a sha’anin karatun boko ba sai a 1955, inda a cikin shekara guda na koyi rubutun Hausa. Ba na mantawa har na rubuta wata makala a kan sha’anin addinin Musulunci, musamamn abin da ya shafi sallar kablu da matsayin sadakar da ake yi wa mamaci bayan ya mutu, irinsu sadakar uku da sauran abubuwa na addini da dama. An buga wannan makala a Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta shekarar 1957. Wannan makala ta jawo cece-kuce a tsakanin malaman Kano ,inda suka yi karata gaban Sarkin Kano Sanusi har sai da aka daure ni tsawon kwanaki 17. Da har jaridun Daily Times da Citizen sun yi niyyar daukar mini lauyoyi, sai kuma aka daidaita maganar inda Sarki ya bayyana cewa ba a yi kuskure a cikin wannan rubutu ba.
Da ma a duk lokacin da na dauka ina neman ilimin addini a gefe guda kuma ina gudanar da harkar kasuwanci, inda wani yayan mahaifina da ake kira da Maso Kano ya sanya ni a harkar kasuwanci, inda muke sayar da kayan sutura a Kasuwar Kurmi. Na dauki shekaru kusan bakwai ina gudanar da harkar kasuwancin. Sai kuma na yi tunanin in tafi kasar Ghana don ci gaba da  karatuna na addini. Ban dawo garin nan ba sai da yayana Bala ya rasu.
Dokta RakiyaA wanann lokaci ne Farfesa Galadanchi ya zo yi wa mahaifiyata ta’aziyya, da ya samu labarin dawowata sai ya shawarce ni da in dawo gida Kano in yi karatuna, inda ya sama mini gurbi a Makarantar  koyar da Arabiyya (SAS) a shekarar 1959. A nan muka ci gaba da karatu, sai dai ba a koya mana turanci, hakan ya sa muka nemi a sanya mana Turanci a tsarin karatuttukanmu.
Muna cikin shekararmu ta uku a makarantar sai gwamnatin Jihar Arewa ta nemi a ba ta dalibai za ta tura su kasar waje, aka kai sunanmu. Amma ni ban san ina da abokan hamayya ba, sai aka soke sunana. Amma da shekara ta kewayo sai aka sake sanya sunana, to a wannan karon har mun je Legas za a ba mu tikitin tafiya sai aka ce wai an soke tafiyartamu. Wannan karon ma saboda ni aka yi hakan. Haka dai na zauna a makarantar SAS har na kammala karatuna na  shekaru hudu.
Bayan na gama a shekarar 1963 sai Alhaji Aminu dantata ya dauke ni aikin koyarwa a makarantarsu ta Alhassan dantata, inda daga bisani kamfaninsa ya dauki nauyina na  karo karatu a kasar Masar. Bayan na dawo kuma sai gwamnatin Jihar Arewa ta dauke ni aikin koyarwa a makarantar Horan
Malamai ta Kano, inda na zauna tsawon shekara 7. Daga nan ne sai na koma karatu a Jami’ar Bayero, to amma kasancewar ba mu iya turanci ba sai muka fadi a jarrabawar share fagen shiga jami’a. Sai da shekara ta kewayo sannan na samu shiga jami’a, inda na karanta bangaren addini da harshen larabci. Bayan na gama  sai na koma ma’aikatar ilimi na ci gaba da aiki, amam wanann karon a matsayin masu duba makarantu (inspekta). A wanann lokaci ne Gwamnan Kano Sani Bello ya nada ni mamba a Ma’aikatar Jin dadin Alhazai. Daga baya kuma sai aka mayar da ni Establishment. A wanann lokaci ne aka kafa cibiyar horar da ma’aikata inda muka rike ta ni da wani Baturen kasar Kanada.
Dokta Sa’adatuMuna wannan wuri tsawon shekaru bakwai, sai na bar aiki na shiga siyasa na kuma ci gaba da harkar kasuwancina. Dama tun a da can da nake harkar kasuwanci a gefe guda kuma ina yin harkar siyasa tun daga lokacin Jamhuriya ta farko inda muka yi NEPU tare da Malam Aminu Kano, har aka kirkiri NPN. To a lokacin da Malam Aminu Kano ya bar NPN ina daga cikin wadanda suka ki binsa, ganin cewa ba a yi masa laifi a wannan jam’iyya ba. A NPN aka ba ni sakataren kudi, daga baya kuma aka sanya ni a cikin kwamitin yakin neman zaben Shehu Shagari. Da aka kafa gwamnati aka sanya ni a cikin Kwamitin gudanarwa na Jami’ar Bayero.
Haka dai tafiyar siyasa ta gangaro har zuwa lokacin da aka yi NRC, inda muka mara wa Kabiru Gaya baya ya zama Gwamnan Kano. Ya ba ni mukamin Mai ba Gwaman Shawara kan sha’anin addini. Sai dai tun daga wannnan lokaci na yi alkawarin na daina karbar mukami a gwamnati, don haka da siyasa ta dawo a  shekarar 1999 Gwaman Kano Injiniya Rabi’u M usa Kwankwaso ya so ya jawo ni cikin gwamnatinsa amma na ki yarda, sai dai an yi amfani da garin su mahaifiyata aka ba ni mukamin shugaban CRC na garin, wato Dawakin Kudu. Amam shi ma wannan mukami zuwa kwana bakwai na ajiye shi.
Aminiya: Ya batun iyali fa?
Dokta A’ishaMalam Sa’idu: Ina da mata biyu da ‘ya’ya tara. Hudu mata wadanda dukkaninsu likitoci ne a bangarori daban-daban. Ina karatu a SAS aka haifi babbar  ‘yata Dokta Sa’adatu, ita kuma sai da ta shekara bakwai sannan aka haifi mai bi mata Dokta Rakiya. Sai kuma na ukun Aliyu wanda akanta ne, ya yi aiki da banki daga bisani ya koma kasuwanci.
Sanann akwai Dokta Hadiza, ita ma likita ce. Sai kuma Muhammadu, wanda shi kuma Injiniya ne. Sannan akwai Baba (Haruna) wanda shi ma akanta ne. sai kuma Dokta Aisha. Akwai kuma Musa wanda a yanzu yana kasar Jodan yana karantar aikin tukin jirgin sama.

Sai kuma dan autana Kamilu, a yanzu haka ya gama digirinsa a fannin kwamfuta.
Aminiya: Me ya sa ka zabi ‘ya’yanka mata su karanci aikin likita?
Malam Sa’idu: Abubuwa biyu ne suka sanya ni daukar alkawarin sai ‘ya’yana sun yi karatu. Na farko duba da yadda na yi ta fadi-tashi a harkar samun ilimin bokon nan, ya sa na kuduri aniyar sai ‘ya’yana sun yi karatu. Na biyu kuma dalilin alakata da su Farfesa Shehu Galadanchi da Dokta Hassan Gwarzo, wadanda kowa ya san matsayinsu a harkar ilimi a Jihar Kano. Ganin yadda suka sanya ‘ya’yansu mata a boko ya sa ni ma na samu kwarin gwaiwar sanya nawa ‘ya’yan.
Kasancewar ‘ya’ya mata na fara haihuwa bai hana ni cika burina ba, don haka na sanya su makaranta tare kuma da kula da sha’anin karatunsu. Tasirin ilimin addini ya sa nake ganin  cewa aikin da ya fi dacewa da mace shi ne aikin likita ko na koyarwa, domin zai rage mata cudanya da maza sannan a bangare daya ga ladan taimako. Hakan ya sa lokacin da babbar ‘yata Sa’adatu ta taso na sanya ta a makaranta har ta kammala ina karfafa ta da ta dage ta zama likita, cikin ikon Allah kuma Allah Ya tabbatar da hakan . Sauran ‘yan uwanta mata  da suka biyo bayanta sai su ma suka nuna sha’awarsu ga wannan fanni, a nan su ma na ci gaba da ba su kwarin gwiwa har Alalh Ya cika mana burinmu.
Aminiya: Shin ka fuskanci kalubale daga jama’a na kusa game da sanya ‘ya’yanka da ka yi a boko har suka kai ga samun ilimi mai zurfi?
Malam sa’idu: Babu shakka mahaifiyata ba ta so hakan ba, domin ita ta fi so in aurar da su, musamman Sa’datu. A ra’ayinta ta fi so a yi musu aure in ya so sai su yi karatunsu a gidan mazajensu. Haka kuma mutane sun yi ta mamakin yadda aka yi na sanya ‘ya’yana mata a makarantar boko ta mishan, amma ni da yake na san ina da manufa a kan hakan ban kula da abin da mutane za su fadi ba, na ci gaba da kula da karatun ‘ya’yana.
Dokta HadizaAminiya: Wane abu kake so a tuna ka da shi?
Malam Sa’idu:  Ina ganin abin da zan bari shi ne batun ilimi. Yadda na yi rayuwa a harkar koyo da kuma koyarwa. Har yanzu  mutane na iya tunawa da yadda na nemi ilimi, ina tsaka da gudanar da  harkar kasuwanci, amma na bari na shiga neman ilimi. Kin san kuwa yadda zakin kudi suke, amma a ce mutum ya ajiye neman kudi ya tafi neman ilimi wannan ba karamin abu ba ne . Na biyu kuma ‘ya’yana da Allah ya ba ni wadanda ke aikin taimakon al’umma, domin a yanzu kusan kullum sai na samu sakon godiya daga jama’a inda suke yaba kyautatawar da wata daga cikin ‘ya’yana ta yi masa. Alhamdulillah, ina ganin idan aka kalli ‘ya’yana za a iya tunawa da ni, ganin cewa ni na ba su ilimi na kuma yi musu tarbiyya.
Aminiya: Wace shawara kake da ita ga jama’a game da siyasa da ilimi?
Malam Sa’idu: Game da ‘yan siyasa a yanzu ba ni da shawarar da zan gaya musu duba da yadda suke gudanar da siyasarsu a yanzu ya saba da lokacin da muka yi tamu a baya, wanda a wancan lokaci kasar ce a gabanmu ba wai abin da mutum zai samu ba. Amma mutanen da suke siyasa a yanzu wanda batun son kansu ne a gabansu, sun zama ‘yan barandan siyasa, to wace shawarar za ka ba su, domin sun yi nisa ba jin kira za su yi ba. Ina iya tunawa a lokacin yakin neman zaben Shagari mun sha yawo da kudi cikin motata, amma ko kwabo ba na dauka don amfanin kaina, burinmu kawai shi ne a kafa gwamnati.
Game da ilimi kuwa ina kiran iyaye masu hali ne ko marasa shi, da sa su tsaya tsayin-daka wajen ganin ‘ya’yansu sun samu ilimi. Haka kuma su rika bibiyar abin da ake koya wa ‘ya’yan nasu a makaranta, ko da kuwa mutum bai yi karatu ba akwai hanyar da mutum zai bi wajen ganin ‘ya’yansa sun yi karatu sosai. Girman ilimi ya wuce abin da za a yi wasa da shi, domin kamar yadda Hadisi ya nuna, neman ilimi farilla ne a kan dukkanin musulmi. Haka kuma iyaye su yi kokarin tarbiyyar ‘ya’yansu.