‘Abin da ya sa na amince a yi min dashen zuciyar alade’
Karon farko ke nan a tarihi da aka yi da dan Adam aikinn dashen zuciyar alade a cikin nasara
Wani mara lafiyan da aka yi wa dashen zuciyar alade ya bayyana dalilinsa na amincewa, duk cewa ya san akwai hatsari a tattare da yin hakan.
Likitoci a kasar Amurka ne suka yi nasarar yi wa mutumin mai suna David Bennett mai mai shekara 57 dashen zuciyar alade da aka sauya kwayar halittarta a karon farko a tarihi.
- Yajin aiki: ’Yan Adaidaita Sahu sun tafka asarar N300m a yini daya a Kano
- Matan da suke fitar da kanshi daga jikinsu
A ranar Litinin ne aka sanar da hakan bayan likitocin sun kammala aikin dashen zuciyar a Asibitin Koyon Aikin Likita na Jami’ar Marylanda da ke Kasar Amurka.
Karon farko ke nan a tarihi da aka gudanar da irin wannan aiki cikin nasara a wani yunkuri na shawo kan matsalar karancin masu bayar da gudunmawa, domin ceton rayukan masu fama a matsalar zuciya.
Sanarwar da aka fitar ta ce bayan aikin da aka gudanar a ranar Juma’a ya gudana cikin nasara, an kafa sabon tarihi a fannin yi wa dan Adam dashen sassan jikin dabba.
Ta bayyana cewa an yi wa wani mara lafiyan mai suna David Bennett, dashen zuciyar aladen na bayan gwajin da aka yi masa ya nuna jikinsa ba zai iya daukar dashen zuciyar dan Adam ba, saboda wasu cututtuka da ya jima yana fama da su.
Dole na zabi a yi min —Brennett
A halin yanzu Mista Bennett yana murmurewa kuma ana ci gaba da kula da shi a asibitin tun bayan an kammala aikin tiyatar da aka yi masa a ranar Juma’a.
“Ba ni da wani zabi face in yarda a yi min wannan dashen ko kuma a bari in mutu. Ni kuma so nake in rayu.
“Na san akwai tsabar kasada, amma ba ni da wani zabi da ya wuce hakan,” inji Mista Brennett, kafin a shigar da shi dakin tiyata.