Abin da ya sa na ayyana sake tsayawa takara kafin in bar kasar- Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ya ayyana kudurinsa na sake tsayawa takara ne kafin ya bar kasar saboda yadda mutane suke tafka muhawara a kan lamarin, sannan kuma ya ce tun tuni ya so ya sanar.   Mai taimaka masa na musamman a kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya sanar da hakan […]

Abin da ya sa na ayyana sake tsayawa takara kafin in bar kasar- Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ya ayyana kudurinsa na sake tsayawa takara ne kafin ya bar kasar saboda yadda mutane suke tafka muhawara a kan lamarin, sannan kuma ya ce tun tuni ya so ya sanar.

 

Mai taimaka masa na musamman a kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya sanar da hakan inda ya ce, shugaba Buhari ya ce, “Na sanar da zan sake tsayawa takara ne saboda ‘yan Najeriya suke muhawara a kan ko zan sake tsayawa takara ko ba zan sake ba. Wannan ne ya sa na ga ya dace in yi bayani domin hankali ya kwanta. Muna da sauran aiki, musamman a bangaren tsaro da bunkasa aikin gona da tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawar. Muna bukatar mayar da hankalinmu wajen, bai kamata siyasa ta shiga ta kawo mana tsaiko ba. Da yawa daga cikin ‘yan Najeriya suna jin dadin abin da muke gudanarwa, wanda shi ne ya sa zan sake tsayawa takara.”