Abin da ya sa na bai wa Buhari gudunmuwar Naira miliyan daya – Dattijuwa Fati
Malama Fati Ibrahim Talle-Tara mai shekara 80 da take sayar da abinci a karamar Hukumar Koko/Besse a Jihar Kebbi. Dattijuwar ta bai wa dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari gudunmawar Naira miliyan daya a lokacin da ya ziyarci jihar domin gudanar da yakin neman zabensa. Aminiya ta tattauna da ’yar kasuwar. […]
Malama Fati Ibrahim Talle-Tara mai shekara 80 da take sayar da abinci a karamar Hukumar Koko/Besse a Jihar Kebbi. Dattijuwar ta bai wa dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari gudunmawar Naira miliyan daya a lokacin da ya ziyarci jihar domin gudanar da yakin neman zabensa. Aminiya ta tattauna da ’yar kasuwar. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Me ya sa kika bai wa Janar Muhammad Buhari kyautar makudan kudi?
Malama Fati: A lokacin farko da ya fara tsayawa takara bai samu nasara ba. Hakazalika, a karo na biyu da na uku duka labarin bai sauya ba, amma sai ya umarce mu da mu yi hakuri. A wannan karon shi ne yunkurinsa na hudu. A gaskiya ina goyon bayansa ne saboda kishin kasa da yake da shi da gaskiyarsa da kuma kankan da kai. Kuma a wannan lokacin da nake magana da ku, akwai dana da na aika Kano domin ya je ya bugo fostocin Janar Buhari guda dubu 300. A yanzu sun iso garin Jega za a fara raba su ga jama’a.
Aminiya: Wannan ne karon farko da kika bai wa Janar Buhari gudunmawar kudi?
Malama Fati: Na sha taimaka masa a sauran lokutan da ya tsaya takara a baya. Akwai lokacin da na kashe Naira miliyan biyu. Ina kashe kudina ne wajen tallata shi saboda kowa ya san cewa ba shi da kudin yin hakan. Kuma nakan yi amfani da kudin da na tara ne daga sana’ar sayar da abinci da na shafe shekara masu yawa ina yi.
Aminiya: Yanzu da kika yi kyauta da duk abin da kika tara, yaya kike ji?
Malama Fati: Ai ba wasu kudi ba ne masu yawa idan aka kwatanta da irin ci gaban da za mu samu idan ya samu nasara. A gaskiya gudunmawata aba ce kankanuwa.
Aminiya: Yaya kika ji lokacin haduwarki da Janar Buhari a filin jirgin sama?
Malama Fati: Na kwashe tsawon yini guda ina jiran isowarsa. Kuma daga karshe na yi tozali da shi a karon farko a rayuwata. Wannan kansa wani burina ne da ya cika. A gaskiya na ji dadi matuka saboda shi kansa ya bayyana farin cikinsa lokacin haduwarmu. Wani arashi kuma shi ne mahaifina sunansa Buhari. Ka ga zan iya wa Janar Buhari duk wani abu da zan yi wa mahaifina. Ga shi kuma Janar Buharin mutum ne mai kishin kasa da gaskiya.
Har ila yau, lokacin da suka sauka a filin jirgin sama, ya umarci Gwamnan Jihar Sakkwato Aliyu Magatakarda Wamakko da ya rika kula da bukatuna.
Aminiya: Ko Gwamnan ya yi abin da ya umarce shi ?
Malama Fati: Ah, lokacin da muke Jihar Sakkwato tare da jama’a ta, Gwamnan ya saukar da mu ne a wani babban otel. Ya kuma umarce ni da na fadi duk abin da nake bukata. Sai na ce masa abin da nake bukata da shi, shi ne ya ci gaba da aiki da kuma ba da goyon bayansa wajen shugabanci nagari. Daga nan sai ya ba ni kyautar Naira miliyan daya da kujerun aiki Hajji biyu. Guda tawa, guda ta diyata Umma wacce mijinta ya rasu ya bar ta da ’ya’ya bakwai.
Aminiya: Yaya za ki ji a ranki idan canjin da kike fata bai samu ba?
Malama Fati: Zan ci gaba da tallafa wa fafutikar kafa shugabanci nagari a kasar nan kuma ba zan taba yin da na sani yin hakan ba. Mun yi amanna cewa Ubangiji a wannan karon zai ba mu sauyin da muke nema ruwa a jallo. Idan kuma har ba mu samu nasara ba a bana, za mu ce hakan ya faru ne ba wai domin ba mu ne muka yi nasara ba.
Aminiya: Wace gudunmawa kike bayarwa wajen samun sahihin zabe da kuma kauce wa tarzomar zabe?
Malama Fati: A yanzu akwai malamai da nake daukar nauyinsu domin su yi wa kasar nan addu’a. Mun yi imani cewa ba wani rikici da zai faru.
Aminiya: Wane fata kike da shi ga kasar nan?
Malama Fati: Burina shi ne na ga Janar Buhari ya lashe zabe kuma an rantsar da shi, ya kuma kama aiki. A ranar zan yanka sa da dafa abinci mai yawa, inda za a yi gagarumar walima. Jama’a a ranar za su ci abinci a shagona kyauta saboda murna.
Aminiya: Ya batun iyali?
Malama Fati: Mijina ya rasu. Ya bar ni da ’ya’ya 15 da jikoki 15 kuma galibinsu su ne suke taimaka mini a wajen kasuwancina . Ni dai na fito ne daga garin Jega. Kuma aure ne ya kawo ni garin Koko.