Abin da ya sa na bar siyasa – Buba Galadima
Injiniya Buba Galadima yana daya daga cikin fitattun ’yan adawa a Najeriya. Ya yi gwagwarmaya wajen kafuwar jam’iyyun siyasa da dama da suka hada da ANC da APP da ANPP da CPC da kuma sabuwar Jam’iyyar APC. Sai dai kwatsam, a farkon wannan mako, an ruwaito shi yana cewa zai kaurace wa fagen siyasa. Wakilanmu […]

Injiniya Buba Galadima yana daya daga cikin fitattun ’yan adawa a Najeriya. Ya yi gwagwarmaya wajen kafuwar jam’iyyun siyasa da dama da suka hada da ANC da APP da ANPP da CPC da kuma sabuwar Jam’iyyar APC. Sai dai kwatsam, a farkon wannan mako, an ruwaito shi yana cewa zai kaurace wa fagen siyasa. Wakilanmu sun tatttauna da shi, inda ya yi dogon bayani kan dalilinsa na yanke wannan shawara:
Aminiya: Kana daya daga cikin fitattun ’yan adawa da suke kokarin kafa kakkarfar jam’iyyar adawa da za ta iya kawo gyara a harkokin siyasar Najeriya, amma kwatsam sai aka ji ka ce za ka janye daga harkokin siyasa, me ka hango kuma me ya sa ka yi wannan tunani?
Buba Galadima: Tabbas idan ka karanta wannan jarida za ka ga na yi amfani da wata kalma (janyewa daga fafatawa a harkokin siyasa). Kuma har yanzu ina kan wannan matsayi nawa. Na fara shiga harkar jama’a ce tun 1959, inda nake dauke da nauyi na jama’a wato lokacin da na shiga makarantar firamare inda na yi monita na ajinmu na shekara bakwai na kuma yi shugaban dalibai. A sakandare tun daga aji daya har na yi aji biyar ni na yi monita kuma na yi shugaban dalibai. A makarantar share fagen shiga jami’a ni ne shugaban na Fista Hall kuma na zauna a majalisar dattawa ta dalibai. A jami’a na tsaya neman shugabanci na kungiyar dalibai. A takaice daga 1979 ina aiki na shiga cikin harkokin siyasa dumu-dumu. Ina daya daga cikin shugabannin Jam’iyyar NPN., domin ni ne shugaban samari a wancan lokaci. Kuma na rike mukamai da yawa a wancan gwamnati, kuma a gwamnatin soja ta Janar Muhammadu Buhari da ta Janar Babangida har zuwa ta Janar Abacha na rike muhimman mukamai a wadannan gwamnatoci. Bayan na zo majalisar gyara tsarin mulki a 1988 ne na sayi wannan gida da nake ciki a yanzu. Kuma na zo taron tsarin mulki a 1994, ka ga duk wadannan harkoki ne da suka danganci siyasa da zamantakewar jama’a. Kuma na yi Sakataren Kudi na kasa na Jam’iyyar NRC. Kuma ni da Abba Dabo muka kafa Jam’iyyar ANC da gwamnatin Abacha ta ki yi wa rajista. A lokacin mun tattara muhimman ’yan siyasa a Arewaci da Kudancin kasar nan a jam’iyyar. Amma saboda wasu hujjoji na gwamnatin soja ta wancan lokacin aka hana mu rajista. Cikin mutanen da muka tara, akwai Alhaji Umaru Shinkafi da Malam Adamu Ciroma da Janar Shehu Musa ’Yar’aduwa da Alhaji Lema Jibrilu da Alhaji Bamanga Tukur da Cif Alani Bankole da Cif B.B. Afugu da sauransu. Da aka ki yi mana rajista, sai na ce na bar siyasar. Kuma da na ki shiga harkokin siyasa na jam’iyyu biyar da aka kafa lokacin Janar Abacha, sai aka nada ni Darakta Janar na Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa. Da aka dawo siyasa da ni aka kafa Jam’iyyar APP, mu ne manyanta, mu ne muka kafa ta. Duk mutumin da ya samu mukami a APP ina da lada a ciki, in ya aikata assha kila ina da kamasho a ciki. Aka zo ta koma ANPP, daga nan muka yi ta gwagwarmaya har muka zo muka kafa TBO wato kungiyar Masoya Buhari a lokacin da ya shiga harkokin siyasa. Kowa ya ga irin rawar da muka taka ni da Alhaji Sule Yahaya Hamma, mutumin da nake girmamawa kwarai da gaske saboda irin kwanyar da Allah Ya yi masa da basira da sanin aikin gwamnati. Na koyi abubuwa da yawa daga shugabancin da ya yi mana. Muka zo Jam’iyyar ANPP wasu baragurbi saboda alakar da suke da ita da gwamnatin PDP suka sa dole muka kauce muka kafa Jam’iyyar CPC, a yau ni ne Babban Sakataren wannan jam’iyya. To wadannan abubuwa da na lissafo maka sun nuna cewa akwai rawa ta musamman da kuma mukamai da nake rike da su da suka sa nake sahun gaba a tafiyar da wadannan abubuwa baki daya.
Abin da ya sa na ce na janye na koma bayan fage ba na rike da mukamin siyasa shi ne, idan kana rike da mukamin siyasa akwai abubuwan da za ka yi da komai girman dan siyasa ba zai iya yinsu ba, ba zai iya samun dama ba. Misali in an kira taron shugabannin jam’iyya a hukumar zabe komai girmanka a siyasa in ba ka shugabancin jam’iyya ba za ka ba. A wannan irin matsayi da Allah Ya kai ni, na yi mu’amala da mutane da yawa kamar jakadun kasashen waje ko shugabannin gwamnatocin kasashen waje da za su zo Najeriya sukan kira mu su tambayi hakikanin abin da ke faruwa, kila ina cikin na kan gaba da za a nema domin a ji tabbas. To irin wannan a yau babu shi, ka ga kuwa na koma gefe ko dan kallo ko mai taimakawa ta bayan fage, domin ba ni da wannan hurumi. Amma mutane da yawa sun yi gurguwar fassara ga wannan batu.
Aminiya: Ba ka ganin mutane suna wannan tunani ne saboda rikice-rikicen da kuka yi fama da su tun daga ANPP zuwa CPC, musamman kan tsayar da ’yan takara kamar a jihohin Kano da Katsina da Bauchi da kuma maganar shugabanci ga kuma batun Rufa’i Hanga shugaban Jam’iyyar CPC na farko da ya kai karar jam’iyyar…
Buba Galadima: Wato kawaici ka yi, ka ki tambayata kai-tsaye. Mun san da zaman zarge-zarge da yawa da aka yi mana. Kuma daya daga cikin zargin nan ko a jiya da muka yi zama na Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar CPC na kasa, na fito da daya daga cikinsu. Domin akwai lokacin da aka yi babban taron jam’iyyarmu ranar 11 ga Mayu (na bana) akwai wani mutum da ake kira Dokta Ibrahim Dauda daga Jos. Yana mamba na kwamitin babban taron. ’Yan garinsu da ba su sonsa suka zo inda ake aikin suka fada shi da duka, suka fasa masa ido, suka fasa masa gilashi, sai da jam’iyya ta dauki nauyin kai shi asibiti da yi masa jinya. To sai ya rubuto takardar kuka ga jam’iyya cewa ga abin da su wane, su wane suka yi masa. Ni ba na wurin taron, da na zo a matsayina na Sakatare, sai aka ce in rubuta musu takarda kan kukan da ya yi, su dubi kukan su yi mana bayani, gaskiya ne ko ba gaskiya ba. Kawai kwatsam, za mu je taro, sai na ga takarda daga Filato sun yi min zagin uwa uba, duk da cewa a lokacin da na rubuta musu takardar na ce, Majalisar koli ta Jam’iyya ta umarce ni in rubuta muku takarda ku duba, ku yi sharhi a kai, in gaskiya ne ko ba gaskiya ba. Amma in ka ga yadda suka rubuta suka zazzage ni, suka zazzagi iyayena, suka dauka suka kai wa shugaban jam’iyya, suka kai wa Janar Buhari, abin babu kyau. Na kawo na gwada a gaban taro a san irin halin da muke ciki.
Bari in dawo tambayarka, gaskiya ce Jam’iyyar CPC ta shiga wadansu halaye masu ban tsoro a baya. Kuma idan mutum ba a ciki yake ba, ba zai gane lamarin ba. Bari mu fara da magana ta farko, Sanata Rufa’i Hanga, ni Buba a matsayina na wanda yanzu ba ya rike da wani mukamin siyasa, muna yi masa godiya. Domin a lokacin da muka nemi wanda zai iya shige mana gaba a kai takardarmu na neman rajista a INEC shi muka jawo. Shi ya cire kudi a aljihunsa ya biya rajistar wannan jam’iyya, muka ba da sunansa a matsayin shugaban riko. Kuma ya ba mu daya daga cikin rukunin gidajensa, muka yi amfani da shi a matsayin hedkwatar jam’iyya inda INEC ta zo ta duba, kafin su yi mana rajista. Mutumin da ya yi irin wannan sadaukarwar, ba za mu taba mantawa da shi ba. Kuma idan mu ’yan halal ne ko da muna da wata rigima da shi, ya ci mu gode masa. Amma a yanzu shi korarre ne daga jam’iyyar ta CPC. Amma jiya a taronmu na karshe na cire shi da shi da Alhaji Almaijiri Gaidam, wanda ya yi mataimakin Shugaban Jam’iyya da Injiniya Mutallib Badmus, wanda ya yi Sakataren Jam’iyya, na yi musu godiya ta musamman a kan irin gudunmawar da suka bayar. Na biyu, ba ma an samu riginginmu kan tsayar da ’yan takara a Kano da Katsina da Bauchi da sauransu kawai ba ne. An zarge mu da abin da ya fi haka, musamman ni da Alhaji Sule Yahaya Hamma. An yi mana zargi fiye da yadda aka sani. Misali ko ranar Lahadin nan da ta wuce ina dawowa daga ta’aziyya daga Gashuwa da Kano, na tsaya a Kaduna wurin wani aminina da magoya bayan jam’iyyarmu suka ce ya saya musu motoci in je in yi masa godiya. Mun dade ba mu hadu ba, da na je muka gaisa da shi, sai ya ce da ni ‘kai Buba, ana fa zarginka’. Na ce da me? Ya ce, ‘ana ta zarginka, an ce ka karbi makudan kudi a Katsina don tsaida dan takara; ka karbi makudan kudi wajen tsaida dan takara a Kano; ka karba a Bauchi’, ya kirga min. Idan aka tara kudin da ya fada, sun fi Naira biliyan daya. Mai irin wannan kudi duk yadda ya iya cin hatsi ko a fuskarsa za a gane, ko a muhallinsa. Ka ga dai gidan da nake zaune daki ne biyu tun 1988 yau shekara 25 nake cikin wannan gidan a zaune bai canju ba. To ina son yin amfani da wannan jarida taku in gaya wa duniya cewa zama fa aka yi a jam’iyyance aka tabbatar da ’yan takara aka wanke ’yan takara, aka ba mu umarni, ni da shugaban jam’iyya ta kasa Yarima Tony Momoh, muka sa hannu a jerin sunan muka aika wa INEC. A zaman da muka yi har da Janar Muhammadu Buhari, in kudi ne muka karba, shin Yarima Tony Momoh da Buhari ma sun karba? Ko kuma kawai mun yaudare su ne muka sa ’yan takara na aika hukumar zabe? Abin da mutane ba su sani ba, idan ma kudi ne ake bayarwa a nemi takara tsakanin Muhammadu Abacha da Lawal Ja’afaru Isa wa yake da kudin da zai iya ba mu, mu ba shi takara? A maganar da abokin nawa ya yi min an ce Muhammad Abacha ya ba ni Naira miliyan 300. Muhammad Abacha yana da rai, bai samu takara ba, ka je ka tambaye shi, shin kudin nan da ya ba ni ya yafe ne ko sadaka ya ba ni? A Katsina da Lado da Masari, in kudi ne ake bayarwa, shin wa ya kamata ya ba da kudi mafi yawa? Lado, me ya sa ba mu ba shi ba? Kuma a hankalce da al’adance, yanzu kana ganin zan iya daukar kujerar dan takarar Gwamna in ba wani mutum a Katsina ba tare da yarda ko sanin Janar Buhari ba, jihar da ya fito? In mafadin magana wawa ne, bai kamata mai saurare ya zama wawa ba.
Kuma an zarge ni cewa ana ganina a billa (Fadar Shugaban kasa), to na ji an gan ni a billa. Shin wanda ya zarge ni nan, dan PDP ne ko dan adawa? Idan dan PDP ne, sai in yi kwanciyata in ce sharri ya yi min, kuma wadansu suna iya yarda da ni. In kuwa dan jam’iyyar adawa ne ya gan ni a billa, shi me ya kai shi billa? Ko laifin da na yi shi ma ya yi? Ko kuma mun je billar da shi ne aka ba mu kudi, ni bai ba ni ba ya rike, yanzu a kirawo shi ni ma in nemi tawa la’adar kan rakiyar da na yi masa zuwa billa. Kuma billa din nan ba ita ce gidan gwamnatin Najeriya ba, ni a matsayina, ba ni da hakki a ciki? Ko an ce a kundin tsarin mulkin Najeriya sai dan PDP ne kawai zai iya zuwa billa? Akwai jahilci a cikin wannan maganar.
To hakika ma ban ma je billa ba. Lokacin da na je billa da ni da Fasto Tunde Bakare da Naja’atu Mohammed da Wole Soyinka da Faruk Adamu Aliyu muka je, lokacin da muka je karkashin kungiyar ceto Najeriya (Sabe Nigeria Group), lokacin da muka matsa aka ba Jonathan shugabancin Najeriya. Bayan mun je, ya yi mana godiya ya dauki Dala dubu 50 (kimanin Naira miliyan takwas) ya ba mu. Kowa ya san an buga a jaridun kasar nan, mun mayar masa da kudinsa. In ma aka ce mun ci Dala dubu 50, ba ni kadai na ci ba, sai a kira Wole Soyinka, a kira Tunde Bakare, wanda shi ne mataimakin dan takarar Shugaban kasa ga Janar Buhari. To mutane suna maganganu wadanda ba su dace ba.
Bari ma in gaya maka wata maganar! A ziyarar da na kai wa abokina na Kaduna, ya gaya min cewa ai ni da Sule Hamma ne muka kayar da Janar Buhari a zabe. Sai na tambaye shi, ta yaya? Mu muka je INEC muka rubuta sakamakon zaben ko yaya? Sai ya ce, zan mayar da shi yaro ne, bayan an ce an ba ni rijiyar mai kan hakan? Na ce rijiyar mai! Ka ga dai rigimar da ake yi tsakanin Shugaba Jonathan da Dino Melaye da Adoke (Ministan Shari’a) kan rijiyar mai ta Malabo. Na ce tunda ya ji irin labarin da ake yi a kan rijiyar ta Malabu tsakanin Jonathan da Don Etete da Adoke da Melaye da Okonjo Iweala da sauransu, ana zancen an karbo makudan kudi an sayar da rabin rijiyar ta Malabu wajen Dala biliyan nawa. Ya je tunda ya san wadanda suka ba ni wannan takarda ta rijiyar mai ya karbo, ko da Naira miliyan 100 ya saida, ya ba ni Naira miliyan 50, ina da bukata.
In an zarge ni misali cewa PDP nake wa aiki ko kuma ANPP don ina zuwa gidan dalhatu Bafarawa, tsohon Gwamnan Sakkwato, ina zuwa gidan Yayale Ahmed, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, wadanda suke zargina kila ba su san cewa, a cikin shugabanninmu akwai wadanda suke kwana a gidajen wadannan mutane idan sun je ziyara wurinsu ba. Ni fa ban taba kwana ba, gidajensu nake zuwa.
Yayale Ahmed din nan kuma, yau ni na san shi shekara 42. A lokacin da na tsaya neman shugabancin kungiyar dalibai, a Jami’ar Ahmadu Bello da Yayale Ahmed da marigayi Shugaban kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa da marigayi mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Umaru Ahmed su ne manajojin kamfen dina, suna yawo da ni gida-gida. Saboda haka sabon da muke da shi ba na yau ba ne. Ko Yayale yana jam’iyyar Shaidan zan iya zuwa wurinsa. Kuma ba karya ba ne, nakan je wurinsa in yi masa tilas. Wata ran wannan gidan da kake gani, sai in rasa abin da zan ci. In je wurinsa in ce dole sai ya kawo wani abu, kuma dole ya kawo. Kuma domin wani, ba zan iya rabuwa da shi ba. Duk siyasar da na yi a rayuwa, babu mutumin da zai ce ‘Buba Galadima yaron gidana ne’, sai dai ‘abokin tafiyata’. Ko yayana Shinkafi da na yi wa aiki, ba zai taba ce maka ni yaron gidansa ba ne. Sai dai ya ce Buba Galadima dan uwana ne.
Shi ko Bafarawa sanina da shi tun 1979. Yana kansila a Sakkwato muka san juna. Ina zuwa gidansa kowane dare. Shin a siyasa ma, mene ne ake da shi na sirri da za a ce ina zuwa gidajensu don in ba su sirrin jam’iyyata? Shin mu dukanmu din ba a ANPP muke ba da Bafarawa, muka fita muka bari? To shi ne zan dauki sirrin tawa jam’iyyar in je in ba shi, ya kai wa ANPP, wadanda har yanzu ba mu karasa yarda da su ba?
Kuma an zarge ni cewa, mutanen PDP sun ba ni mota (musamman Gwamna Babangida Aliyu). Tabbas ya ba ni mota Jeep Kia ga ta can. A lokacin da ya ba ni motar nan, ba na ma Sakataren Jam’iyya. Kuma dalilin ba da motar, dana ne ya yi aure a ranar 1 ga Janairun shekarar 2011. A lokacin ma ko babban taron CPC ba a yi ba, balle na zama Sakataren Jam’iyya. Shi ya ba da gudumawa ga dana. Kuma don Babangida Aliyu ya ba ni mota, ni a dangantakata da shi, bai ma biya ni ba, domin Babangida Aliyu ko matanmu ba za su iya sanin sirrin da ke tsakanina da shi ba. Kuma duk abin da ya yi min a duniya, bai biya ni ba. Kuma ni ma duk abin da na yi masa a duniya, ban biya shi ba. Domin a lokacin da nake Darakta Janar na Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa, Babangida Aliyu shi ne Daraktan Harkokin Zirga-Zirgar Jiragen Sama a Ma’aikatar Sufuri. A kalla da ni da shi da iyalanmu, mun taka kasa bisa kasa har kasa 20 a duniya. Saboda haka, don dana zai yi aure, yana PDP ya ba da gudunmuwar Jeep, ni ba ni da motar shiga, na kwace Jeep din daga wurin dana, sai a ce don me na karba? Mutane nawa ne da muke wannan tafiya da su, suka karbi kyautar dukiya daga wurin PDP? An yi bincike? To, wadannan zarge-zarge bila adadin, an yi su, ana kan yin su. Amma abu daya da nake so na fada shi ne, ba don magana za ta yi tsawo ba, shin mutumin da yake wa PDP aiki a shekaru 13, na wannan tafiya da muke yi da Janar Muhammadu Buhari, …an tuhumce ni, ko kuma an kulle ni, ko kuma an yi min zargin juyin mulki, an tsare ni har sau 37. Kuma a duk lokacin da Jami’an tsaro suka tuhumce ni, ko suka kira ni, na yi jawabi, babu lokacin da ba su kawo su sani a kan abin da suke zargina, mene ne ra’ayin Buhari ba? Ko ko, mene ne Buhari yake ciki.
Aminiya: To duk a kan Janar Buhari ne ake yi maka wadannan tuhumce-tuhumce?
Buba Galadima: To a dalilin wane ne, in ba shi ba? Ina neman mukami ne a siyasa ko a gwamnati? Ko na tsaya zabe ne? Ai ban tsaya zabe ba, saboda haka duk wani abu da ya biyo baya a wannan tafiya, ai a dalilinsa ne aka yi min. An yi min fa zargin a kan cewa ina kokarin juyin mulki, a lokacin da muka shirya gangamin abin da ake kira ‘mass action’. Lokacin da muka kira Alhaji Balarabe Musa da Cif Olu Falaye da Odumegu Ojukwu da Janar Buhari da Dokta Tunji Braithwaite da sauransu a watan Maris na 2004. A lokacin an kama ni an kulle ni, aka ajiye ni a karkashin kasa, sauka hudu a karkashin kasa. Ba ni sanin dare ko rana, har idona ya kusa lalacewa. An sanya ni a sarka, sau da kafa hakan nake zaune. Janar 12 na soja masu jan wuya aka sa su bincike ni. Idan Buhari ya zama Shugaban kasa, wanda ina fatan zai zama, don Allah don Annabi ya karbo duk wannan kundin (record), domin in ya ce a kawo masa za a kawo. Ya ga irin zargin da aka yi min saboda shi, kuma ya ga irin amsar da na bayar a wannan matsayi da ba ni da mai taimako duk duniya, sai dai Allah. Amma zan yi amfani da wannan dama a yau, in gode wa gwamnatin Amurka da gwamnatocin kasashen Turai da Attahiru Bafarawa da Janar Aliyu Gusau, wadanda ta hanyarsu ce aka matsa wa gwamnati ta sake ni. Don ba laifi ne da ni ba, kuma ’yancina ne na dan Najeriya in shirya zanga-zanga. Amma an yi shirin a ci min mutunci, ko a ajiye ni a ihunka-banza, har a gama siyasar da ake yi. Duk wannan ya same ni.
A gidan nan, ina da yara bakwai, suna da digiri har da mai digirgir a cikinsu, amma ba mai aikin yi. Ba don ba su yi karatu ba. Ka ga wancan, lauya ne ga shi nan, ba ya da aikin yi. Ba don komai ba, illa iyaka don suna amsa sunan Buba Galadima. Kuma an ce PDP nake yi wa aiki. To wane irin son inna ne wannan? Ni ina yi musu aiki, amma ni ina zama a tagayyare? ’Ya’yana ba su da aikin yi, kuma PDP suna kama ni suna kullewa, suna ci min zarafi, amma duk da haka, a zarge ni cewa ni ba a yarda da ni ba, ina yi wa PDP ne aiki? Sai ga shi Allah da Ya tashi wanke ni, sai ga bakin haure daga PDP sun dako tsalle, takan garu sun fado gabanmu. Aka ce kuma su ne shugabaninmu. Kuma sauran talakawan suna bin su, sun yarda da su. Amma mu duk wannan wahalar da muka yi ta shekaru, an ce ba a yarda da mu ba. Akwai abubuwa fiye da dama da na sani, sai dai in mutu da su a zuciyata. Ko kuma sai dai idan wani ya tsokane ni, in amayar da su. Amma a matsayina na dattijo, na fi karfin abin duniya da zai sa ni na yi wata maganar da ba daidai ba. Wadannan bakin hauren, yau an ce an yarda da su, mu da muka yi wahala shekaru da dama, an ce ba a yarda damu ba. Hanga da muka sa shi ya kafa jam’iyyar, an kore shi. Mu ma muna jingine a yanzu, muna jiran abin da zai faru da bakin hauren su kuma a gobe.
Za mu karasa wannan hirar a mako mai zuwa, in Allah Ya so.