‘Abin da ya sa na barranta daga Boko Haram’

Abin da Bana Umar ya shaida wa sashin Hausa na Muryar Amurka da wani dan jarida wanda ya lallashe shi ya bar kungiyar Boko Haram. Kafin ranar 18 ga Agustan da ya wuce, Umar wani mayakin kungiyar Boko Haram ne da yake zaune a wani sansanin a dajin Sambisa, daya daga cikin inda kungiyar ta […]

‘Abin da ya sa na barranta daga Boko Haram’

Abin da Bana Umar ya shaida wa sashin Hausa na Muryar Amurka da wani dan jarida wanda ya lallashe shi ya bar kungiyar Boko Haram.

Kafin ranar 18 ga Agustan da ya wuce, Umar wani mayakin kungiyar Boko Haram ne da yake zaune a wani sansanin a dajin Sambisa, daya daga cikin inda kungiyar ta dade tana zaune a Arewa maso Gabacin Najeriya.

Abin da ya fadi hakika mai ban mamaki ne. Umar ya ce ya yi aiki a matsayin dogarin wani kwamanda mai suna Abu Gaidam wanda ya ce na hannun dammar Abubakar Shekau ne sosai.

Kuma ya ga abubuwa a sassan Jihar Borno. “Na halarci yake-yake har sau biyar. Na yi yaki a Wulari. Na yi yaki a Bita, kuma na fafata yaki a wajejen Chadi. Kuma ina cikin tawagar da suke korar sojojin Najeriya duk lokacin da suka yi yunkurin shiga Sambisa.”

Sai dai tunaninsa yana aiki ne kamar na bindigarsa. Domin lokacin da aka tambaye shi ko abin da Boko Haram suke yi mai kyau ne ko daidai ne, sai ya ce, ba daidai ba ne, saboda suna kai hari ga mutane “cikin rashin imani ba gaira ba dalili,” kuma a fahimtarsa suna murguda Musulunci don dacewa da halinsu na tashin hankali.

Rediyo ne ya karfafa masa gwiwar yadda zai gudu. Umar ya ce, ya ji alkawuran da Babban Hafsan Sojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya yi cewa, duk wanda ya mika wuya daga Boko Haram za a yi maraba da shi, kuma ba za a hukunta shi ba. Kuma ya ji yadda duniya take Allah wadai da kwanton bauna da hare-haren kunar bakin waken da Boko Haram ke kaiwa.

“Da dama muna sauraren tashoshi irin su BBC da Muryar Amurka. Ina sauraron wadannan tashoshi a kai- a kai ta yadda idan zan kwanta nakan yi ta tunanin abin da na ji. Na fahimci cewa dukan abubuwan da muke yi ba su da kyau. Mu kashe, mu sace, mu kwace wa mutane dukyarsu da sunan addini. Amma abin da muke ba addini ba ne, a karshe na dawo daga rakiyar kungiyar,” inji shi.

Yanzu dai Umar yana Maiduguri fadar Jihar Borno, bayan ya gudo daga sansanin Boko Haram. Ya shaida wa wakilin sashin Hausa na Muryar Amurka, Haruna Dauda abubuwan da suka faru da shi, inda ya bayar da bayanin yadda ake daukar mayaka da sake rike mayaka da kuma yadda suke kubuta daga hare-haren dakarun kasashen hadin gwiwa. 

An lallabe shi ya shiga, ya ji tsoro ya gudu: 

Umar mai shekara 27, ya fito ne daga garin Banki da ke iyakar Najeriya da Kamaru. Kafin shekarar 2014, yana gyaran wayoyin hannu ne da dora abubuwa a kan kaset din sidi.

Amma a shekarar sai Boko Haram suka mamaye garin. Umar ya ce abokinsa Abu Mujahid ne, ya janyo ra’ayinsa ya zama mamban kungiyar. Mujahid ya ce, dukan ’yan Najeriya kafirai ne, mabiya Shekau ne kawai Musulmin kwarai. Ka shigo za ka iya yaki ka kashe kafirai.

Umar ya shiga, amma ya ce nan da nan ya fara jin tsoro ya nemi ya gudu. Amma bai iya ba, ya ce, saboda Abu Mujahid ya shaida masa cewa za a kashe idan ya yi kokarin guduwa.

Umar ya ce, “Ko jita-jita ko zargi marar tushe aka yi cewa wani yana tunanin barin kungiyar hakan na iya janyo a kashe wannan mutum.”

Ya ce, Boko Haram kan kashe gwiwar masu niyyar gudu ta hanyar shaida musu cewa, alkawarin da Janar Buratai ya yin a yin afuwa ga duk wanda ya gudu karya ce.

Umar ya ce, akwai ’yan Boko Haram fiye da dubu da suke son barin kungiyar “Akwai mutane da dama da aka sace su daga garuruwansu, wadanda ba su san hanyar da za su koma garuruwansu na asali ba. Su (shugabannin Boko Haram), suna wa’azi ga irin wadannan mutane cewa kada su bar kungiyar, suna nuna musu Allah ne Ya hukunta kasancewarsu a wurin,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Hatta wadansu ’ya’yan kungiyar na asali yanzu suna son barinta saboda sojoji suna matsa kaimin yaki da su ba kamar yadda abin yake a baya ba.’

Wajibi ne dukan ’yan Boko Haram su sauya suna idan suka shiga kungiyar, don haka Bana Umar ya sauya sunansa zuwa Abu Mustapha. Ya ce shi ya zama mayaki ne ba kwamanda ba. Ya ce mayakan suna zaune na sashin Jimiya da ke dajin Sambisa, a cewarsa nan ne hedkwatar Boko Haram.

Ya ce a wani lokacin yanayin rayuwa yana da kyau. A shekarar 2014, Boko Haram ta mulki wasu sassa na jihohin Borno da Yobe da Adamawa, kuma tana iya yin komai yadda ta so. Ya ce, “A yanzu rayuwa tana da tsanani. Ba kamar yadda abin yake a baya ba. Abinci yana wahala ga kowa.”

Bana ya ce, wadansu mayakan suna noma abincinsu da kansu, “Amma idan ka yi noman, shugabanka yana iya karbe duk abin da ka noma da sunan addini. Koyaushe ana gaya maka cewa shugabanka yana da iko da duk abin da kake da shi da kuma kai kanka,” inji shi. Ya ce, shugabannin Boko Haram suna yin amfani da addini domin tayar da zaune-tsaye. “Suna yin amfani da addini su ce mana ku kashe tare da alkawarin shiga Aljanna. Shugabannin sukan jawo ayoyi daga Alkur’ani da hadisan Annabi (SAW) domin su kafa hujja. Kuma idan suna yi mana bayanin hujjojinsu, sai mu rika yin kabbara, daga nan sai mu fita mu kama kisa,” inji shi.

Kiran ‘tuba’

Boko Haram ta kashe akalla mutum dubu 20 a sassan Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar, tun lokacin da ta kaddamar da hare-hare a shekarar 2009. Hare-haren bama-bamai sun ci gaba da gudana duk da cewa sojojin hadin gwiwar wadannan kasashe da kuma Benin sunkwace kusan daukacin yankunan da Boko Haram ta taba kwacewa, inda Abubakar Shekau ya ce zai kafa ‘daular Musulunci.’

Ganin irin mugun aikin da kungiyar ke yi ne sai Bana Umar ya rika jin akwai bukatar ya gudu. Amma bai gudu ba, sai da wani ya karfafa masa gwiwa kan ya amince da abin da Janar Buratai ya yi alkawari. Ya gudu a ranar 18 ga Agusta tare da wancan mutum – matar kwamandansa Abu Gaidam. Kuma a ranar 20 ga watan ya mika kansa ga sojoji a Maiduguri.

Da aka tambaye shi me zai ce kan mayakan Boko Haram da har yanzu suke dajin Sambisa, sai Umar ya ce: “Ina kira gare su da su tuba, musamman wadanda suke son su fito amma suke tsoro… Ya kamata su sani sojoji ba za su yi komai ga wanda ya tuba a kashin kansa ba. na fito kuma babu wanda ya cutar da ni. Babu koda soja daya da ya cutar da ni da hannunsa.” 

Yanzu haka mahukunan Najeriya suna yi wa Bana Umar bayani kan yadda suke yi da ’yan Boko Haram da suka bar kungiyar a kashin kansu. Kuma idan suka kammala za a yi kokarin sake maido shi cikin jama’a sai dai kuma ba zuwa garinsa na Banki ba. Za a dauke shi ne zuwa wani garin da ba a san shi ba, domin ya sake sabuwar rayuwa.