Abin da ya sa na bude kofar jirgi yana da tsaka da gudu a sama – Fasinja

Fasinjan zai iya fuskantar daurin shekara 10

Abin da ya sa na bude kofar jirgi yana da tsaka da gudu a sama – Fasinja

Kofar jirgin da aka bude

’Yan sandan Koriya ta Kudu sun ce fama da matsalar numfashi ce ta saa mutumin nan da ake zargi ya bude kofar jirgin sama mallakin kamfanin Asiana Airlines yana tsaka da gudu a sararin samaniya inda ya bukaci fitar gaggawa.

Jirgin dai na dauke ne da fasinjoji kusan 200, lokacin da ya kusa titin da jirgi yake gudu kafin ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Daegu.

Birnin dai na da kimanin nisan kilomita 240 ne daga Kudu maso gabashin Seoul, babban birnin kasar.

’Yan sandan sun ce mutumin, wanda bai wuce shekara 30 ba, ya bude kofar ce lokacin da jirgin yake kimanin mita 200 ya taba kasa, ba tare da wani cikakken bayani ba.

Sai daga bisani ’yan sandan birnin na Daegu suka tsare suka titsiye shi inda ya shaida musu cewa yana fama da matsananciyar damuwa ce tun bayan da ya rasa aikinsa a ’yan kwanakin nan.

“Ya ji cewa jirgin yana bata lokaci kafin saukarsa, shi kuma nunfashinsa ya fara daddaukewa, inda ya bukaci ya fice kawai,” kamar yadda wani dan sanda mai bincike ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP).

Fasinjan dai zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara 10 saboda karya dokokin sufurin jiragen sama.

Bayan saukar jirgin dai, fasinjoji da dama sun rika sumewa, inda wasu daga cikinsu ke cewa sun zata mutuwa za su yi.

Wani jami’in Ma’aikatar Sufurin kasar ya shaida wa AFP cewa wannan ne karo na farko da hakan ta taba faruwa a tarihin sufurin jiragen sama a kasar.