Abin da ya sa na ce a raba Najeriya – Farfesa Ango Abdullahi

daya daga cikin jiga-jigan kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya ce raba Najeriaya shi ya fi zama alheri saboda yawan shakiyancin da dattawan Kudu ke furtawa a ’yan kwanakin nan. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake karin haske ga wakilinmu a Zariya, kan kiran da ya yi a raba Najeriya kuma ya […]

Abin da ya sa na ce a raba Najeriya – Farfesa Ango Abdullahi
Abin da ya sa na ce a raba Najeriya – Farfesa Ango Abdullahi

daya daga cikin jiga-jigan kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya ce raba Najeriaya shi ya fi zama alheri saboda yawan shakiyancin da dattawan Kudu ke furtawa a ’yan kwanakin nan. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake karin haske ga wakilinmu a Zariya, kan kiran da ya yi a raba Najeriya kuma ya tabo wasu batutuwa da suka shafi kasa kamar haka:

Aminiya: Farfesa an ruwaito ka kana cewa a raba Najeriya, sakamakon kiraye-kirayen da wadansu ke yi cewa a raba ko a sake fasalin Najeriya, me ya jawo haka?
Farfesa Ango Abdullahi: Eh, to abin da na hanga tantagaryar shakiyanci ne kawai da wadansu mutane daga Kudu suke yi don babu wani abu daga ciki sai shakiyanci da kuma neman wulakanci da kuma neman muzanta jama’a a kan zamantakewar da ake da ita a nan Najeriya. Yau dai Bature da ya zo ya gwama mu waje daya a kan ma ba mu san juna ba wajen shekara dari ke nan har da biyu, ya yi shekaru yana mulki kafin mu karbi mulki. Daga lokacinsa zuwa lokacin da aka karbi mulkin kai, an yi ta neman hanyar da mu mutanen Najeriya aka yamutsa mu yadda za mu zauna da juna mu yarda cewa wannan kasar guda daya ce kuma kowa yana da wani abu wanda zai iya amfana da shi a cikinta. To amma kullum muna ganin manyan mutanen da ake tsammanin hankalinsu ya wuce a ce jahilci ya sa suke yin maganganu na a zo a sake tsarin Najeriya wai Bature Mista Lugard ya yi kuskure da sauransu. To ni abin da yake ba ni mamaki wani lokaci sai mu mutanen Arewa mu dauka cewa kasar nan mu ne kadai muke cin alherinta wadansu da suke kukan nan ba sa ci, kuma suna ganin mu mutanen Arewa muna kwararsu ne. In ba rashin tunani ba da rashin karanta tarihin kasar nan ba, ba wanda zai tashi daga Kudu ya ce Arewa ta kware shi a zamantakewar da muke yi. In da mu masu kishin kanmu ne masu duba tarihin kasar nan ne da kyau, in da wanda zai ce ana kwararsa a zamantakewar kasar nan, to mu mutanen Arewa ne. Muna da cikakken bayani a kan Arewa ita ta gina Najeriya bayan Bature ya hada mu waje daya. A wancan lokaci ya kasa Najeriya hudu, a lokacin ya nuna babu shakka kuma tabbataccen abu ne wanda an bincika kuma a rubuce yake cewa Arewa ita ta rike Najeriya, ita ta rike kasar nan. Jama’arta da jibinsu da aikinsu da tsarin mulkinsu da Bature ya zo ya iske su da shi, mu muka gina kasar nan duk wanda yake cikin kasar nan ba wanda ba za mu nuna kabilarsa ba cewa yana cin albarkacin Arewa ne. Saboda haka cewa har yanzu zamantakewar kasar nan bai yi musu ba, to, shi ne ran nan na ce mu ma ba ya yi mana dadi, saboda haka duk wanda ya ji zaman bai yi masa dadi ba, ya kama gabansa abin da na ce ke nan.
Aminiya: To, idan aka ji wannan magana ta fito daga bakinka za a dauka ka yi ne a madadin Dattawan Arewa, ko ka yi ne a kashin kanka?
Farfesa Ango Abdullahi: Eh, da farko na yi magana ne amadadin kaina. Na biyu ina tabbatar maka cewa kyakkyawan zaton da nake da shi a kan mutanen da na sani muna aiki tare kuma muna kishin Arewa, kusan in ce ra’ayin wannan kungiya tamu ta Northern Elders Forum zai yi wuya ya bambanta da nawa cewa lokaci ya yi idan ’yan Najeriya sun ji zaman bai yi musu dadi ba, kowa ya kama gabansa. Ai kwanan nan Malam Adamu Ciroma abin da ya ce ke nan, kuma ba ya cikin kungiyar Northern Elders Forum, yana cikin ACF ne, amma kwanan nan ya ce duk wanda yake so ya bar Najeriya a bar shi ya kama haya ya bar Najeriya. Ku san in ce dai mutane sun tuke sun suke a kan wadannan maganganun banza na wadanda ake ganin dattawa ne masu sani ba jahilai ba suke yi daga Kudu. Da wadansu jahilai suke irin wadannan maganganu sai a hakura, amma maganganun suna ta fitowa ne daga wadanda da su aka yi gwagwarmaya ko da iyayensu aka yi amma har yanzu suna cewa Arewa tana kwararsu a zaman da ake yi yanzu. Kuma wanda a baya muka yi kiri-kiri da shi a kan wannan batu shi ne Farfesa Ben Nwabueze wanda shi ne Sakatare Janar na kungiyar Ohaneze Ndigbo ta ’yan kabilar Ibo. Ya ce shi abin da ya sani Najeriya ba za ta zauna da kyau ba in dai ba wani abu aka yi a kan yawan Arewa ba. To ni ban gane abin da yake nufi ba, so yake a zo a karkashe mu mu rage yawa domin yawanmu ya zo daidai da su ko kuwa me yake nufi? Ko so yake a debi kasar a ce an ba su don su samu karin kasa kamar yadda muke da shi yanzu? Iyaka abubuwan da suka dame su ke nan domin wannan kasa a wurina babu wanda yake cin arzikinta kamar Ibo. Saboda haka in ya ga ba ya ci a shirye muke duk wanda ya ga zai tafi ya tafi, ni ba na shakkar komai in don an raba kasar nan kila ma shi ne zai fi mana zama alheri kuma zai fi wa ’ya’ya da jikokinmu zama alheri, amma wannan zaman gamin-gambiza a wurina ba zai yiwu ba.
Aminiya: Farfesa ba ka ganin kamar matsi ne ya sa kuka fara cewa a raba kasar, su kuma suna ganin sun riga sun kai ku kasa ba ku da hadin kai ko wata madafa don haka suke ta yawan mita cewa a raba?
 Farfesa Ango Abdullahi: kasa dama mu muka kai kanmu ai da mu ’yan Arewa a sama muke kuma ba wanda zai iya dauke wannan abin inda mun tsaya a kan wannan abin iyayenmu suka dora mu a kai, amma saboda lalacewar shugabanci musamman shugabanni wadanda za a ce ’yan Arewa ne lalacewarsu ya kawo ake takalar hancinmu a kan zamantakewa a kasar nan. Saboda haka ko gobe aka raba kasar nan ba ni shakka cewa Arewa za ta rayu fiye da kowane shiyya a kasar nan, domin abin da muke da shi, ba su da shi, kuma ba za su taba samu ba, wannan tarkacen abin da ake kira mai ba mu girma a cikin mai ba, a cikin gyada da auduga muka girma kuma muka rayu kuma ko’ina a kasar nan gyada da auduga da koko su suka gina shi ba man fetur ba. To yanzu ina man fetur din yake kasar take cikin fitinar talauci da ba a tsammani.
Aminiya: To yanzu da za a ce ka ba da mafita, me za ka ce?
Farfesa Ango Abdulahi: A ba da mafita a kan wadanda suke cewa zaman kasar nan bai yi musu daidai ba? In haka ne a raba, kuma idan har an yarda a zauna, to sai an koma an yi sabon lale. Sabon lalen nan shi ne wannan tsari da Bature ya bar mu da shi na tsarin gwamnati irin na Ingila (Parliamentary System of Gobernment) in dai ba shi za a koma ba, to sai dai a raba kasar nan.
Aminiya: A baya tsohon Shugaban kasa Jonathan ya kafa kwamitin da zai ba da shawara kan yadda kasar nan za ta kasance. Kana ganin sakamakon da za a fito da shi, ba za ku gamsu da shi ba?
Farfesa Ango Abdullahi:Wannan  ya kira  taro ne na kansa, nasa na Jonathan ba taron kasa ba, ai na kira wannan taron da sunan na Jonathan ba na kasa ba, domin akwai bambanci a tsakanin taron kasa da kuma taron Jonathan. Kuma wannan taro karya ne aka shirya, misali yaya za a ce Arewa wadda take da kusan kashi 60 da wani abu cikin 100 na jama’ar kasar nan a ce wai a taron tana da wakilci da kashi 30. Kuma yaya za a ce Musulmi muna da kashi 33 na wakilan da suka je wannan taro a kasa, alhali mu ke da jama’a fiye da kowa, wannan ai karya ce wannan tsari ne wanda Jonathan ya yi tare da makiya Arewa kuma koda yana Arewa ne, su Farfesa Nwabuezi su suka sa shi ya yi wannan taro.
Aminiya: Farfesa ba ka ganin wadannan rabe-rabe za su sa mu shiga hali na rashin yawa da fitunu daban-daban?
Farfesa Ango Abdullahi: Mutanen da suke cewa ba a za iya raba Najeriya ba muna da tsarin mulki Najeriya sai in buga misali da kasashen Turai kamar Ingila wanda ta yi mulkinmu, shekararta dubu da mulkin dimokuradiyya, to amma su ma suna da sassa. Kuma baran can Scotland wadda take tare da Ingila shekara 300, mutanenta suka ce suna so su fice daga Hadaddiyar kasar Ingila, (UK), aka yi kuri’ar raba-gardama da ba su ci ba suka hakura. Ka ga a ce yadda muke kabilu daban-daban a ce kai ne Sarkin Makera ka mulmula karfe kamar yadda za a ce za a iya fashewa da sauransu wannan ba zai taba yiwu ba. Sannan ga kasar Indiya lokacin da ta samu ’yanci cikin shekara daya ta fashe Pakistan ta fita sannan cikin shekara daya Bangaladesh ta fita kwana-kwanan nan Tarayyar Sobiyet wadda ake yi mata kirari da babbar kasa ta fashe ta zama kasa 13. Saboda haka mene ne a Najeriya da ake cewa ba za ta iya fashewa ba? Kuma ga Ingila kwanan nan ta fita daga Tarayyar Turai, don haka duk wanda yake ganin zamanmu a matsayin kasa daya ba ya yi masa dadi ba a raba, mu zo mu watse kowa ya kama gabansa.
Aminiya: To a karshe mene ne sakonka ga ’yan Najeriya?
Farfesa Ango Abdullahi:  Abin da ya fi damunmu yanzu ba ya ga wadannan surutai da ake ta yi cewa a zo a yi gyaran kasa da sauransu akwai wasu matakai da gwamnatin nan ta dauka wadanda a wurinmu ba su da kyau, kuma wajibi ne mu yi magana a kai. Babban kuskuren da gwamnatin nan ta yi a wurinmu shi ne kashe darajar kudin kasar nan wato Naira. Alhali Shugaban kasa tun kafin a zabe shi ya sha karfafa cewa ba zai rage darajar Naira ba, koda yake ya iske ta a halin da ba ya so, zai hakura a wannan halin da ba ya so amma ba zai rage darajarta ba, ta yadda za ta kara lalacewa idan aka hada ta da kudaden kasashen waje. Yau in kana neman Dala guda sai ka nemo Naira 420 kafin ka sayi Dala daya. Lokacin da nake Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello in na ba da Naira biyu sai a kawo min Dala uku, ka san kuma irin wannan matsayin idan ka dauke su ba ka iya komawa baya.
Aminiya: Ai ya ce har yanzu kwararu ba su gamsar da shi ba kan karya darajar Nairar?
Farfesa Ango Abdullahi: Mun san wadanda suka matsa masa, Hukumar Lamuni ta Duniya (IMF) da Bankin Duniya ne. A nan Najeriya ’yan Najeriya su ne IMF kuma su ne Bankin Duniya, domin su ke rike da arzikin kasar nan. Abin da IMF da Bankin Duniya suke so shi suke yi kuma kusan mulkin kasar yana hannunsu ne shi ya haifar mana da wannan. A cikin kamfen din Shugaba Buhari ya ce bai kamata talaka ya sayi lita fetur ta wuce Naira 50 ba, ko ba haka ya fadi ba, to amma yanzu nawa ake sayarwa? Naira145. Maganar aikin gona kuma da ya ce shi zai gaji man fetur yana cikin kuskure wanda ni a ganina ake yi a cikin kasafin kudi bana, abin da aka bai wa aikin gona kashi daya ne da da digo biyu (1.2) cikin 100 kuma aikin gonar nan shi ke kawo mana kashi 40 cikin 100 na tattalin arzikin kasar nan. Don haka wadannan manyan kura-kurai ne da ake tafkawa.