Abin da ya sa na daina zagin kaina a fim —Mai Sana’a
Fitaccen jarumin barkwanci a fina-finan Hausa na Kannywood, Musa Mai Sana’a, ya ce yana matukar nadama a game da tsinewa ko la’antar kansa da yake yi a cikin wasu fina-finan da ya fito. A cikin wata tattaunawa da BBC ta yi da shi ta Instagram, Mai Sana’a ya ce a da ya yi hakan saboda […]
Fitaccen jarumin barkwanci a fina-finan Hausa na Kannywood, Musa Mai Sana’a, ya ce yana matukar nadama a game da tsinewa ko la’antar kansa da yake yi a cikin wasu fina-finan da ya fito.
A cikin wata tattaunawa da BBC ta yi da shi ta Instagram, Mai Sana’a ya ce a da ya yi hakan saboda rashin kwarewa.
Amma a hankali a hankali sai ya fahimci cewa wannan abu da yake fa ba abu ne mai kyau ba.
Ya ce, “da farko-farkon finafinaina na yi ta yin abubuwa wadanda ni a ganina daidai ne, amma daga bisani bayan da wasu mutane suka ja hankalina a kan abubuwan musamman zagi ko tsine wa kaina da nake, sai na fahimci cewa lallai ya kamata in
daina.”
Musa Mai Sana’a ya ce a yanzu ya kara fahimtar abubuwa a finafinan
Kannywood, kuma ga girma ma da ya zo.
“Don haka dole wasu abubuwa a jingine su a daina, musamman
da yake ga shi an fara tara iyali dole a daina wasu abubuwan a
cikin fina-finai”, inji jarumin.
Mai Sana’a ya ce, shi a finafinansa ana gani kamar yana
wuce gona da iri, to sam shi ba ya haka.
Ya ce, “ina yin fina-finaina ne domin nishadi da kuma
fadakarwa, kuma na fi yin finafinai ne ma a kan batun da ya
shafi iyaye da ’ya’yansu.
“Duk abin da aka na yi a cikn fim to fadakarwa nake domin
masu irin wannan hali da na yi a ciki fim su dauki darasi su daina”,
inji Mai Sana’a.