Abin da ya sa na fadi zaben Jihar Bauchi – Gwamna Abubakar
Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar shi ne dan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC kuma ya sha kaye a hannun dan takarar Jam’iyyar PDP Sanata Bala Muhammad. A zantawarsa da BBC a fadi matsayinsa kan yadda ya fadi a zabe: Me za ka ce game da yadda ta kaya a zaben Gwamnan Jihar Bauchi? Da farko dai […]
Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar shi ne dan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC kuma ya sha kaye a hannun dan takarar Jam’iyyar PDP Sanata Bala Muhammad. A zantawarsa da BBC a fadi matsayinsa kan yadda ya fadi a zabe:
Me za ka ce game da yadda ta kaya a zaben Gwamnan Jihar Bauchi?
Da farko dai ina godiya ga Allah da Ya ba da iko aka yi wannan zabe lafiya ba a samu wani tashin hankali ba musamman a Jihar Bauchi. Mun dauki matakai da dama domin a samu zama lafiya kuma a yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana, shi ya sa ma tun daga farko na ja kunnen hukumomin tsaro da magoya bayana cewa a tabbatar da an yi zabubukan nan lami lafiya. Ga yadda zabe ya kaya kamar yadda na taba yin hira a baya a kan yadda zan karbi sakamakon zabe, abin da na fada a wancan lokaci shi ne Allah ke ba da mulki ga wanda Yake so kuma a lokacin da Yake so, kuma Yake karba daga hannun wanda Yake so a lokacin da Yake so, to Allah Ya riga ya ida nufinSa. A dalilin haka ne ma ya sa tuni na riga na yi jawabi na yi murna ga wanda ya ci zabe, na kuma yi kira gare shi ya ja hankalin magoya bayansa wajen yin murnar cin zabe kada a ta da hankalin kowa.
Ta yaya ka taya shi murna, ta sanarwa ce ko kun yi magana ce da shi ta waya?
Na bayar ta sanarwa ce saboda ina Abuja shi kuma ina kyautata zaton yana Bauchi, amma duk da haka zan bi ta wadancan kafofi idan na same shi a waya ma zan dora a kan haka insha Allahu.
Ko wannan yana nufin ba za ka kalubalanci sakamakon zaben a kotu ko wani mataki makamancin haka ba?
To ni dai a zuciyata haka ne, to amma da yake ni dan jam’iyya ce kuma jam’iyya ce ke tsayawa zabe, dan takara a karkashin inuwarta yake, na shirya zan hadu da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa baki daya, bayan haka kuma zan hadu da Mataimakin Shugaban Kasa. To duk irin umarnin da suka bayar shi za a bi tunda ni cikakken dan jam’iyya ne, amma ni a ra’ayin kaina ina tsaye ne kan wannan murna da na taya dan takarar da ya ci zabe.
A taka fahimtar mene ne dalilin da ya sa ka fadi wannan zabe?
Ai dalili na ga Allahu (SWT) kamar yadda na fada da farko, Allah ke ba da mulki ga wanda Ya so kuma Ya karbe a lokacin da Ya so, mu dai za mu yi furuci a kan wasu abubuwa da muka gani amma Allah ne Ya san daidai.
Bisa yadda sakamakon zabe ya nuna za a iya cewa wannan kamar wani hukunci ne kan jagorancinka?
A’a, ba haka ba ne ai kamar yadda na fada maka idan ka dubi sakamakon zaben, mafi yawan kananan hukumomin Jihar Bauchi mu suka zaba, biyu ne kawai aka je aka yi aringizo, saboda haka wannan ba alama ba ce ta cewa al’ummar Jihar Bauchi ba sa sonmu ba, ai mun yi abin so a Jihar Bauchi. In ka shiga kowane lungu da sako dole za ka ga wani aiki da Gwamnatin Jihar Bauchi ta APC ta yi.
Amma ka taba tunanin za ka fadi zaben nan?
Ban taba tunanin haka ba, ba don komai ba sai saboda idan ka dubi sakamakon zaben ka dubi fadin Jihar Bauchi baki daya, mafi yawan kananan hukumom mu suke yi, Kananan hukumomi biyu ne kawai suka kawo abubuwan da hankalin mutum ba zai dauka ba. Kamar Karamar Hukumar Bauchi misali an yi zabe a akwati 493 amma babu kuskure ko guda daya, ka ga wannan ba harka ce da hankalin dan Adam zai kama ba don ya saba wa dabi’ar dan Adam. A Karamar Hukumar Tafawa Balewa ma in ka dubi sakamakon zaben mafi yawan gundumomi, mu muka ci amma gunduma uku ne aka rike aka yi aringizon kuri’a.
Kana zargin cewa an yi aringizon kuri’a ko akwai hujja?
Kwarai da gaske akwai hujjoji a wadannan kananan hukumomi.