Abin da ya sa na fallasa magudin zaben da mu ka yi – Sanata Mantu

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Nasiru Ibrahim Mantu ya bayyana cewa yana da hannu a cikin magudin zaben da aka yi a baya, inda ya ce ya sha bai wa jami’an zabe da na tsaro kudi su sauya sakamakon zabe. Sanata Nasiru Mantu ya ce “Ba dole ne sai na je rumfar zabe in […]

Abin da ya sa na fallasa magudin zaben da mu ka yi – Sanata Mantu

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Nasiru Ibrahim Mantu ya bayyana cewa yana da hannu a cikin magudin zaben da aka yi a baya, inda ya ce ya sha bai wa jami’an zabe da na tsaro kudi su sauya sakamakon zabe.

Sanata Nasiru Mantu ya ce “Ba dole ne sai na je rumfar zabe in sauya alkaluman zaben ba, amma mun bai wa jami’an hukumar zabe da jami’an tsaro kudi ta yadda idan suka ga wata dama da za su sauya sakamaon zaben su sauya don ya taimaki jam’iyyarmu, to sai su yi hakan.”

A wata tattaunawa da Sanata Mantu ya yi da gidan talabijin na Channels, ya ce a lokacin mulkin PDP, sukan shirya magudi ne sosai inda suke ware kudade na musamman domin bai wa jami’an tsaro cin hanci, “jami’an hukumar zabe har ma da wakilan jam’iyyun adawa ma mukan ware musu nasu, domin su amince da sakamakon zabe a inda muka ga abin zai ba mu wahala. Wannan abu mukan shirya shi ne domin ’yan takararmu su samu nasara a zabubbukan da ake yi. Na gaji da ganin irin haka yana faruwa a kasar nan. Lokaci ya yi da za mu mai da hankali wajen ganin an gyara wadannan abubuwa da ake yi a da. Kuma na gaji da ganin yadda kasashen ketare ke kallon dan Najeriya a matsayin mai laifi a duk inda ya shiga a duniya,” inji Mantu.

“Sannan kuma talauci ya yi wa al’ummarmu ta Najeriya katutu. Allah Ya wadata kasar nan da arziki, amma maimakon a yi amfani da dukiyar yadda ya kamata kowa ya samu abin yi, sai aka bar su kara- zube, kullum sai ka ga wani na yi maka sallama yana neman ka taimake shi, ko dai gidansa babu abinci ko an yi masa haihuwa babu yadda zai yi. Sannan duk inda muka tafi a fadin duniya ana nuna mu kamar marasa gaskiya. Idan ba fadin haka aka yi ba domin a gyara za, to za mu ci gaba da zama cikin rudani ne kawai da karya,” inji shi.

Sanata Ibrahim Mantu, ya ce ya tuba daga aikata irin wadannan abubuwa, yana mai cewa ya sanar wa duniya yadda Jam’iyyar PDP take murde zabubbuka a fadin kasar nan ne saboda ganin cewa lokaci ya yi da za a dawo daga rakiyar hakan a gyara domin ci gaban kasa.

Sai dai Jam’iyyar PDP ta nesanta kanta daga kalaman Sanata Mantu, inda ta ce batun bai shafi jam’iyyar ba, kuma ba ta taba sa wani dan PDP ya yi magudin zabe ba. Don haka Sanata Mantu ya yi hakan ne bisa radin kansa, ba bisa umarnin jam’iyyar ba kamar yadda Sakataren Jam’iyyar ya bayyana.