Abin da ya sa na fara aikin DJ a Kano — Kyauta Dillaliya

Aikina na farko na yi shi ne a taron bikin sunan Safiya Musa ’yar fim lokacin da ta haihu.

Abin da ya sa na fara aikin DJ a Kano — Kyauta Dillaliya

Fati Nayo Fulani wacce aka fi sani da Kyauta Dillaliya a fim mai dogon zango na tashar Arewa 24 wato Dadin Kowa, a yanzu ta koma DJ Kyauta Dillalliya.

Duk da cewa ba ta bar fitowa a finafinai ba, amma ta tsunduma harkar yin sankira da aka fi sani a Turanci da MC da kuma harkar sanya kida a wuraren tarurruka wato DJ.

A tattaunawarta da Aminiya DJ Kyauta Dillaliya ta ce ta shiga harkar ce don yin aiki a bukukuwan mata zalla:

Mutane sun saba ganinki a finafinai sai kuma aka ji kin shiga harkar gabatarwa (MC) da DJ. Yaya aka yi hakan ya faru?

Abin da ya ja hankalina na fara harkar DJ kawai ina lalluben sana’ar da zan rika yi don in tallafi rayuwata ce sai wannan tunani ya zo min.

Na lura cewa idan mata suna gudanar da tarurrukansu sai dai su kira DJ namiji ya zo ya yi musu aiki.

Sai na yi tunanni me zai hana in shiga wannan sana’ar don in rika yin aiki a tarurrukan ’yan uwana mata.

Na kula cewa, mata da yawa suna so su samu mace da za ta rika yi musu harkar kida da MC a bukukuwansu da suke yi a gida.

Bayan na yanke shawarar shiga harkar DJ sai na samu wani telana sunansa Mansur na nemi shawararsa a kan haka, inda ya karfafa min gwiwa cewa babu matsala.

Sai na nemi ya raka ni Sabon Gari in sayo kayayyaki, amma ya ce min kamata ya yi in fara neman masu sana’ar sai in hada gwiwa da su don su koya min yadda harkar take sannan kuma ia rika amfani da kayayyakinsu.

Idan ya so duk lokacin da na je aiki, sai a raba kudin tare. Na nuna masa ni ban san kowa ba a harkar ballantana in je in neme su.

Sai ya fada min cewa shi ma ya fara yana ma da kayayyakin aikin. Shi ke nan muka yarda a kan wannan yarjejeniya.

Zan iya tunawa aikina na farko na yi shi ne a taron bikin sunan Safiya Musa ’yar fim lokacin da ta haihu.

Ni na je na hayo kayayyakin na dauki mota har gidanta a Zariya na yi mata DJ a ranar suna. Baya ga DJ ina yin MC.

Shin a matsayinki na mace da take wannan sana’a kina samun aiki kamar maza?

Gaskiya ana gayyata ta aiki sosai domin a lokuta da dama abin yawa yake yi min, duba da cewa a iya sanina kusan ni kadai ce mace da take wannan sana’a.

Duk da cewa akwai mata da yawa da ke yin aikin MC. Amma ni duka biyun nake hadawa a lokaci guda.

Ana gayyata ta bukukuwa daban-daban biki ne ko suna, amma fa sharadina sai harkar ta kasance ta mata zalla.

Da na je wajen taro na yi aiki sai ki ga an zo wurinmu ana amsar lambar waya cewa ana so za mu je wasu bukukuwan, musamamn irin mutan da ba su son hadakar maza da mata.

Haka kuma ina da yara da muke gudanar da aikinmu tare wadanda su ma dukkansu mata ne babu namiji ko daya a cikinsu.

Muna kuma zuwa duk inda za a yi bikin a gida ne ko a wuraren gudanar da bukukuwa na zamani (Event Centers).

Sai dai na fi son yin aiki a Event Centers saboda sun fi fili da sauransu.

Duk da cewa komai kankantar gida nakan je in yi aikina sai dai gaskiya ba na yarda in yi a kofar gida domin idan za a yi a kofar gida, to, maza za su zo kallo su ga matan mutane suna rawa.

Wadanne nasarori kika samu a wannan harka?

Alhamdulillahi duk da cewa ba zan ce ga wani abu ko wata babbar kyauta da aka taba ba ni ba, amma dai na san idan na je aiki ina dan samun abin rufin asiri.

Mene ne kalubalen wannan sana’a?

Na farko rashin isassun kayan aiki domin a yanzu kayan sun yi tsada. Ina so a ce a yanzu ina da wasu manyan amsa kuwwa, amma abin bai yiwu ba saboda tsadarsu. Kin ga a yanzu kowace daya ta kai Naira dubu 400.

Abu na biyu shi ne muna haduwa da bata kayan aiki daga wurin yara. Za ki ga idan ba ki tsaya tsayin daka ba sai yaran nan sun lalata miki kaya. A bar ki da gyara.

Wani kalubalen da nake samu shi ne yadda idan aka fito da amarya fili don yin rawa sai ki ga mutane sun zo sun cika wurin da sunan daukar hoto.

Mutum zai ta yi musu magana, amma su ki barin filin. Wannan abu ba karamin bata min rai yake yi ba.

A kwanan nan Hukumar Hisba ta yi taro da ku yaya taron ya gudana?

A gaskiya ban ma san Hisba ta yi wannan taro ba, sai daga baya na ji an ce ga matakin da ake kai, wanda kuma na yi maraba da shi.

Duba da cewa ita hukuma ce da take kokarin yin umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna, to, duk abin da za ta zo da shi zai zama na gyara kayanka ne wanda kuma Bahaushe ya ce ba ya zama sauke mu raba.

Kowa ya san haramcin da ke cikin hada mata da maza a wurin biki, musamman irin yanayin da ake samu ana rawa, kin ga wannan babu kyau.

A ganina abu ne mai kyau mata su rika yin taronsu daban da na maza. Haka idan za su dauki DJ ko MC ya kasance mata ne za su yi musu wannan aiki.

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba