Abin da ya sa na fice daga APC zuwa SDP – Jumbo

Alhaji Bashir Adamu Jumbo tsohon dan Majalissar Wakilai daga Mazabar Kazaure/Roni/Gwiwa da ‘Yankwashi a Jihar Jigawa, inda ya taba zama Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar . A zantawarsa da Aminiya ya bayyana dalilinsa na ficewa daga APC zuwa SDP, da kuma abin da ya sa zai nemi Gwamnan Jihar:    Wadansu na kallon kun kasa […]

Abin da ya sa na fice daga APC zuwa SDP – Jumbo
Abin da ya sa na fice daga APC zuwa SDP – Jumbo

Alhaji Bashir Adamu Jumbo tsohon dan Majalissar Wakilai daga Mazabar Kazaure/Roni/Gwiwa da ‘Yankwashi a Jihar Jigawa, inda ya taba zama Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar . A zantawarsa da Aminiya ya bayyana dalilinsa na ficewa daga APC zuwa SDP, da kuma abin da ya sa zai nemi Gwamnan Jihar: 

 

Wadansu na kallon kun kasa tsayawa wuri daya a siyasa saboda neman mukami, me za ka ce?

Ni ba na yin siyasa saboda mukami. Da kaina na bar PDP na koma APC saboda a ganina mun shigo APC domin mu ba da shawarwari don a ciyar da Jihar Jigawa gaba. Amma ban shigo APC don neman wani matsayi ko mukami ba. Na yi tsawon shekara biyu da rabi ina cikin APC kuma har na bar APC ban mallaki katin zama dan jam’iyyar ba. An hana mu, ana yi ta mana shagube ana fada mana kalamai marasa dadi ana cewa mu ’yan PDP ne. Ba a yin komai da mu, ba a daukar shawararmu, ba a yin taro da mu gaba daya, mun zama tamkar saniyar ware. 

Na sha fada musu ni ba ni da burin zama dan takara, ba na bukatar wani matsayi amma duk da haka ba a amince da mu ba.

Me ya sa ka koma SDP?

Na fice ne saboda matsa mana da aka yi a APC, ana ganin mun zo ne mu mamaye komai tamkar mun zama wata barazana a wajen ’ya’yan Jam’iyyar APC, kuma na bar APC ce saboda ana kyamar yin duk wata mu’amala ta siyasa da mu. Maimakon mu koma inda muka fito wato PDP, sai muka koma SDP. ballewarmu ta tayar musu da hankali matuka. Kafin mu fice daga tafiyar APC na sha bai wa Gwamna shawara amma babu wata shawara daya da aka dauka aka yi amfani da ita. Wannan ya sa muka tattara duk mutanenmu muka fice sai dai wadansu kalilan da suka makale a ciki.

Magana ta gaskiya a matsayina na shugaba da na jagoranci mutane muka koma APC, ba zan sa ido ina ji ina gani ana muzguna wa mutanena kuma in ja baki in yi shiru ba. Wannan ne ya sa kwanmu da kwarkwatarmu muka fice daga Jami’yyar APC muka koma sabuwar tafiya ta SDP domin fitar da jaki daga duma.

Ba ka ganin za a ce ka koma ne saboda kasuwar bukata?

Ba gaskiya ba ce, na koma SDP ne domin biya wa jama’a bukatarsu. Me nake nema? Allah Ya yi min komai, ni ba duniya ce a gabana ba, mutuncina da martabata su ne gaba da komai. Shi ya sa nake fada wa mutane duk mai son Jihar Jigawa ta ci gaba ya shigo SDP ya ba da gudunmawarsa domin ganin an ceto jihar.

Kuma batun in fito a hada baki da ni don a sauya tunanin jama’a ba gaskiya ba ne, kuma Allah Ya san Shi nake tsoro ba mutum ba. Ba maganar yaudara a wajena, na fito zan yi takara tsakani da Allah kuma a wajen Allah nake nema domin mulki naSa ne.

Ba ka ganin za a ce ka yi wa APC da Gwamna Badaru butulci?

Babu maganar butulci a cikin tafiyata domin sai da na fada musu kafin in fice daga APC. Haka a lokacin da nake PDP kafin in shigo sai da na fada musu ina shawara da na gama kuma na shigo, kafin in fice sai da na fada wa Gwamna Lamido cewa ni fa zan fice daga PDP. Ni ba sabon yanka ba ne kuma ba wanda ya yi min alfarma. Ina alfahari da haka har gobe a cikin tafiyar APC kafin in fice an sha yi min tayin mukamai amma ban karba ba saboda ba su ne a gabana ba. Na shigo ne domin mu ciyar da jam’iyyar gaba mu taimaka wa gwamnatin a samu sauyin da ake cewa. Mun dauka canjin ne da gaske, ashe duk ba haka ba ne.

Me ya sa ba ka yi kokari ka mallaki katin Jam’iyyar APC ba har ka fice?

Maganar cewa me ya sa ban mallaki katin jam’iyya ba har na fice wannan sai dai ka tambayi shugabannin Jam’iyyar APC saboda su ne suka hana mu katin, kuma sun amso katin domin su raba mana mu da muka dawo cikin tafiyar amma me ya sa suka hana mu katin suka ajiye ban sani ba. 

Ka taba bai wa Gwamna shawara kan yadda za a gyara matsalar bai gyara ba?

Na sha zama da Gwamna Badaru ina ba shi shawara a kan yadda za a gyara matsalar har sau biyar, amma bai taba dauka ba, saboda ni ba munafiki ba ne, ko da zan fice daga PDP kamar yadda na fada a baya sai da na fada wa Alhaji Sule Lamido cewa zan fice haka da zan fice daga APC sai da na fada wa Gwamna Badaru cewar zan fice zuwa SDP domin kada Badaru ya kalle ni a matsayin munafiki. 

In ka samu damar zama Gwamnan Jigawa a 2019 ta ina za ka fara?

Zan fara ne ta wajen inganta ilimin firamare da na sakandare kuma zan inganta aikin gona in sama wa manoma kasuwa inda za su rika sayar da kayan da suka noma a farashi mai daraja. Haka zan sama wa manoma kayan noma na zamani wanda zai taimaka wa rayuwar manoman, kuma gwamnatina za ta bai wa noma muhimmanci domin Jihar Jigawa jiha ce ta manoma. 

Kuma zan yi bakin kokarina wajen gina rayuwar dan Adam domin babu abin da ya fi gina rayuwar dan Adam,  shi ne gaba da komai a rayuwa kasancewar jiha ce da aka dogara da gwamnati sosai. 

Yanzu haka na sanya masu bincike kwararru a kan matsalolin Jihar Jigawa kuma da su zan yi amfani wajen bayanan da suka ba ni wajen tafiyar da tsarin mulkina.

Kuma ina tabbatar maka idan na samu damar darewa kan kujerar mulkin Jihar Jigawa ba zan wuce shekara hudu ba, da zarar na sanya komai a kan tafarkin da ya dace zan kauce wani ya zo ya dora. Ban dauki mulki a yi ko a mutu ba, a kullum ina rokon Allah Ya zaba mana mafi alheri.