Abin da ya sa na fice daga PDP – Na’abba

Tsohon Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Ghali Umar Na’abba ya fice daga Jam’iyyar PDP, inda ya bayyana cewa jam’iyyar ta rasa alkiblarta. Ghali ya zama Shugaban Majalisar Tarayya na biyar da ya fice daga Jam’iyyar PDP. Shugaban Manalisar mai ci Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya fice daga jam’iyyar zuwa Jam’iyyar APC a watan Oktoban bara.Sauran shugabannin […]

Abin da ya sa na fice daga PDP – Na’abba
Abin da ya sa na fice daga PDP – Na’abba

Tsohon Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Ghali Umar Na’abba ya fice daga Jam’iyyar PDP, inda ya bayyana cewa jam’iyyar ta rasa alkiblarta.

Ghali ya zama Shugaban Majalisar Tarayya na biyar da ya fice daga Jam’iyyar PDP. Shugaban Manalisar mai ci Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya fice daga jam’iyyar zuwa Jam’iyyar APC a watan Oktoban bara.
Sauran shugabannin majalisar da suka fice daga Jam’iyyar PDP sun hada da Aminu Bello Masari da Patricia Etteh da Dimeji Bankole.
A ranar Lahadin da ta gabata ce Na’abba ya bayyana ficewarsa daga PDP cikin wata wasika mai taken: “Sanarwar ficewata daga PDP da dukkan kwamitocinta,” inda ya aika ga shugaban jam’iyyar na madabarsa ta Sharadda da ke karamar Hukumar Birnin Kano.
Kuma ya aika kwafen wasikar zuwa ga shugaban jam’iyyar na Jihar Kano da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Arewa maso Yamma da Shugaban Jam’iyyar ta kasa da kuma Shugaban Kwamitin Dattawan Jam’iyyar (BOT).
A cikin wasikar Ghali Na’abba ya ce a tarihin Najeriya ba a taba samun gwamnatin da take amfani da addini da kabilanci wajen raba kan ’yan Najeriya irin wannan gwamnati ta Shugaba Jonathan ba.
Ya ce, “Za ku amince da ni cewa wannan dabi’ar siyasa bai kamata ta kowace fuska mutum mai mutunci da hankali ya saurara mata ko ya amince da it aba.
Shugabannin bayan-fage ke juya Najeriya da PDP:
Ya kara da cewa: “Shugabannin bayan-fage ne ke juya akalar shugabancin kasar nan da na Jam’iyyar PDP, ta yadda ’yan Najeriya sun san suna da Shugaban kasa mai suna Dokta Goodluck Jonathan, a lokaci guda kuma sun kasa sanin wa yake shugabancin kasar nan. “Najeriya da PDP suna cikin dimuwa,” inji shi. “Don haka an bar mu a wani yanayi da mutane ba za samu nasara a rayuwa ba, sai in sun kasance marasa kunya ko marasa mutunci. Na lura PDP ta kama hanyar kashe kanta kuma ba yadda za a yi ta farfado.”
Alhaji Na’abba ya ce kafin ’yan Najeriya su samu tohon wata sabuwar rayuwa, wajibi ne “su fice daga wannan shugabanci da ya gaza, shugabancin da bai abin sha’awa ko abin karfafa gwiwa.”
Ya kara da cewa, “A madadinsa, ba wai ’yan Najeriya suna bukatar shugaban kirki da gwamnonin kirki da sauran masu rike da mukaman siyasa kawai ba ne, har ma suna bukatar cikakkun shugabanni ababen misali.”
Na’abba ya ce irin wadannan shugabanni wajibi ne su kasance suna da cancanta da karfin halin gudanar da mulki da kuma sananniyar manufa ga makomar kasar nan.
Ya ce, PDP “ta tsunduma kanta cikin cin hanci da rashawa da mulkin Gadara ta yadda ake dauki-dorar masu tsayawa takarar mukamai, inda kusan jihohi 20 suke fama da rikici kan zaben share-fage na ’yan takarar gwamnoni da sauran mukamai,” inji shi.
Ghali Na’abba ya ce PDP da shugabannin kasar nan sun gaza wajen cin gajiyar dimokuradiyya kan gudanar da zabe daga wata gwamnati zuwa wata ta yadda sauran kasashen Afirka su yi koyi. “A karkashin wannan gwamnati, Najeriya tana fama da zubewar mutunci, inda muke dada komawa sahun baya a harkokin kasashen duniya. Abu mafi bata rai, shi ne damuwar da mafi yawan ’yan Najeriya suke ciki game da yadda gwamnati ke kwan-gaba-kwan baya game da zabe mai zuwa. Abu ne da babu shakka cewa wasu ’yan ba-ni-na-iya ne da miyagu ne suka fi samun tagomashi a harkokin tafiyar da Najeriya.”
Ba a mutunta masu kishin kasa:
Ya kara da cewa “Ya fito fili wadanda suke kan madafan iko sun fi jin dadin irin wadancan mutane marasa mutunci fiye da masu kishin kasa da kaunar Najeriya.
Na’abba wanda shi ne Shugaban Majalisar Tarayya a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003 ya nuna damuwa cewa yanzu ingancin shugabanci a Najeriya yana dada komawa baya, inda muhimman hukumomin da suka hade kasa tare da dinke ’yan Najeriya wuri guda an tsoma su a cikin harkokin siyasa, sabanin shawarwarin masu hankali da gyara siyasa. “Na yi ta kokarin matsawa a yi gyara a harkokin PDP ni da wasu a kungiyance ba tare da mun samu nasara ba. A fili yake ga kowa cewa dukkan muhimman ’ya’yan jam’iyyar an mayar da su gugar yasa,” inji shi.
Ya ce, ’ya’yan jam’iyyar masu halin rakumi da akala marasa mutunci da ba su da gudunmawar bayarwa su ne a kullum shugabanni ke gaskatawa wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar saboda ana cewa suna da ‘biyayya.’ Ya ce “Wannan biyayya, ba wani abu ba ne face hauragiyar mutanen da ba su da kowa ba su da komai.”
Dalilin da iyayen jam’iyya suke barin PDP:
Ya ce, suna cin zafin cewa galibin iyayen da suka kafa jam’iyyar da suka mutu kamar Cif S.M. Afolabi da Alhaji Muhammad Abubakar Rimi da Cif Solomon Lar da Fafesa Osammor da Cif Sunday B. Awoniyi da sauransu duk sun mutu ne cikin bakin ciki da jam’iyyar ko jam’iyyar ta sanya su.
Kuma ya ce koda iyayen PDP na farko da suke raye kamar Dokta Aled Ekwueme da Malam Adamu Ciroma da Dokta Shettima Mustapha da Alhaji Asheikh Jarma da Dokta bictor Odili da Mista Isaac Shaahu da sauransu da dama, “Suna rayuwa cike da irin wannan bakin ciki. Yayin da wasu irin su Alhaji Atiku Abubakar da Alhaji Isyaku Ibrahim da Alhaji Musa Gwadabe da tsofaffin shugabannin jam’iyyar ta kasa, Cif Audu Ogbe da Cif Barnabas Gemade da sauransu suka fice daga jam’iyyar. Jam’iyyar da gwamnati su nuna a fili ba su da tausayi ko mutuntawa.
“Ina fata zukatanku da na sauran masu kishin kasa za su koma ga gaskiya ta yadda za ku dauki matakin da ya dace.”
Da yake tattaunawa da Aminiya bayan aika takardar, Ghali Na’abba ya ce ya zame wajibi a kansa ya bar PDP saboda saboda ta rasa ruhinta kuma ta lalace ta yadda zai yi wahala jam’iyyar ta “gyaru.”
Tsohon Shugaban Majalisar ya ce ficbewarsa daga PDP mako biyu kafin a gudanar da zabe wata manuniya ce ga magoya bayansa da masoyansa a fadin kasar nan cewa kada su jefa wa PDP kuri’arsu.
Me yiwuwa in shiga wata jam’iyyar:
Game da ko zai shuga jam’iyyar adawa ta APC, wadda take kara karfi da masu komawa cikinta daga PDP, Na’abba ya ce “Mai yiwuwa in shiga wata jam’iyyar siyasa nan da ’yan kwanaki kadan, (ya shiga Jam’iyyar APC a ranar Talatar da ta gabata).
Ya yi zargin cewa PDP tana rarraba kudi ga ’ya’yan jam’iyyar da aka fusata kan kada su fice daga jam’iyyar zuwa wasu jam’iyyu, amma duk da haka “Ba su tunkare nib a, saboda sun san ba za su iya saye na ba.”
Tsohon Shugaban Majalisar ya ce, PDP “tana rasa ’ya’yanta maza da mata ciki har da iyayen da suka kafa ta da sauran ’ya’yanta a kullum inda ya ce, “Ba zan zauna ginita ya rushe a kaina ba,” inji shi.