Abin da ya sa na hada aikin koyarwa da sarauta – Sarkin garin Sabon Kawu

Malam Adamu Yohana shi ne Sarkin garin Sabon Kawu da ke cikin yankin gundumar Bwari a birnin tarayya Abuja. A tattaunawar da ya yi da Aminiya ya bayyana dalilan da suka sanya ya koma yake koyarwa a makarantar firamaren gwamnati ta Sabon Kawu da kuma kalubalen da yake fuskanta wajen hada aikin koyarwa da harkokin […]

Abin da ya sa na hada aikin koyarwa da sarauta – Sarkin garin Sabon Kawu
Abin da ya sa na hada aikin koyarwa da sarauta – Sarkin garin Sabon Kawu

Malam Adamu Yohana shi ne Sarkin garin Sabon Kawu da ke cikin yankin gundumar Bwari a birnin tarayya Abuja. A tattaunawar da ya yi da Aminiya ya bayyana dalilan da suka sanya ya koma yake koyarwa a makarantar firamaren gwamnati ta Sabon Kawu da kuma kalubalen da yake fuskanta wajen hada aikin koyarwa da harkokin mulki:

Aminiya: Yaya aka yi kana sarkin garin Sabon Kawu kuma kake koyarwa a wannan makaranta?
Sarki: Abin da ya faru shi ne, gwamnati ta yi mana alkawarin za ta turo mana da malamai amma har yanzu ba ta turo ba. Duk kokarin da muka yi na ganin mun samu isassun malamai ya ci tura. Ni kuma a matsayina na shugaban al’ummar Sabon Kawu kuma a matsayina na wanda yake ya karanta ilimin lissafi, sai na ga ya dace in rika shiga aji ina koyarwa.
Aminiya: To kai da ma ka yi karatun zamani?
Sarki: Na yi karatun firamare da na sakandire har zuwa gaba da sakandire, inda na yi karatun malanta na NCE a fannin lissafi, kuma na kammala da sakamako mai kyau. Don lokacin da nake karatu ba wasa na yi ba kuma ban shagala da wadansu aubuwan banza ba.
Aminiya: Ta yaya aka yi ka samu aikin malanta a makarantar Sabon Kawu?
Sarki: Kamar yadda na gaya maka a baya, muna da karancin malamai, bayan duk kokarin da muka yi na ganin gwamnati ta turo mana malamai ya ci tura sai na rubuta wa sakataren gundumar Bwari wasika na gaya masa cewa ni na karanta lissafi kuma ina da takardar shaidar malanta ta NCE kuma na dade ina shiga ajijuwan makarantar ina koyarwa. Sai ya tambaye ni cewa ko idan sun dauke ni aiki zan ci gaba da koyarwa a makarantar ? sai na ce masa zan ci gaba da koyarwa. Shi ke nan sai suka dauke ni aiki a matsayin malami.
Aminiya: Wane kalubale kake fuskanta wajen hada aikin koyarwa da harkokin mulki?
Sarki: Yadda nake yi shi ne, kowanne na ware masa lokacinsa, ta yadda daya ba zai yi karo da daya ba. Aikin koyarwa ina yin sa ne da safe, shi kuma harkar tafiyar da mulki ina yi ne idan mun tashi daga makaranta. Mutanena ma sun san haka. Saboda haka idan da wata matsala sai su jira sai mun tashi daga makaranta idan na shiga fada sannan su zo gare ni. Sai dai kuma wani lokaci a kan samu matsala ta taso gadan-gadan, yadda nake yi sai in tura wakili wurin. Sai dai kuma wani babban kalubalen da muke fuskanta shi ne, akwai wasu mutane da idan abu ya faru nan da nan suke so in yanke hukunci, kuma a gaskiya abin ba haka yake ba. Wani lokaci idan ka yanke hukunci cikin gaggawa to babu shakka za a yi da-na-sani, amma idan aka yi bincike sosai aka tabbatar da mai gaskiya da marar gaskiya, to sai ka ga an yi hukuncin da ya dace.
Aminiya: Wane alfanu ko darasi ka samu wajen hada koyarwa da harkokin mulki?
Sarki: Gaskiya na ga alfanu mai yawa kuma na koyi darasi da dama. Saboda ka san shi ilimin lissafi ilimi ne na tunani da auna abu da kuma kirdado. Wannan ya ba ni damar samun kwarewa a harkokin mulkin da nake yi. Domin idan aka kawo mani wata matsala mai sarkakiya idan na yi amfani da ilimin lissafin da nake da shi sai ka ga na warware ta ba tare da wahala ba. Hatta ita kanta magana lissafi ce, saboda sai ka hada tunin abin da za ka fada a zuciyarka sannan ka furta shi har mutane masu sauroronka su fahince ka. Shi ya sa wannan ilimin lissafi ba karamin amfani ne da shi ba.
Aminiya: Wane kira za ka yi ga masu sarauta irinka wadanda suke ganin sun fi karfin su yi taimako irin naka?
Sarki: Ni kira da zan yi a gare su shi ne, tun da Allah ya dora musu nauyin al’umma, su duba su ga irin baiwar da Allah ya ba su su taimaka wa mutanensu. Saboda ilimi shi ne gishirin zaman duniya. Idan masu mulki za su rika yin haka to babu shakka za a samu fahimtar juna a tsakaninsu da mabiyansu.