Abin da ya sa na hana Gwamna shiga gidana don yin rigakafi – Usman Sani
A ranar Juma’ar da ta gabata ce wani magidanci mai shekara 46 mai suna Usman Sani Goron-Namaye ya shafa wa fuskarsa toka ya hana Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero shiga gidansa domin diga wa ’yarsa maganin cutar Foliyo.Wannan al’amari mai kama da majigi ya faru ne a Unguwar Rigasa lokacin da Gwamnan ya […]

A ranar Juma’ar da ta gabata ce wani magidanci mai shekara 46 mai suna Usman Sani Goron-Namaye ya shafa wa fuskarsa toka ya hana Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero shiga gidansa domin diga wa ’yarsa maganin cutar Foliyo.
Wannan al’amari mai kama da majigi ya faru ne a Unguwar Rigasa lokacin da Gwamnan ya je unguwar domin kaddamar da allurar rigakafin Foliyo a yankin. Bayanai sun nuna cewa an kaddamar da allurar ce a unguwar domin jama’ar yankin sun yi kaurin suna wajen kin yarda da ita. Kuma wannan magidanci an san shi da adawa da allurar Foliyo duk da kasancewarsa kusa da asibitin unguwar.
An ce Gwamna Yero ya je unguwar ne domin kara wa mazaunanta kwarin gwiwa cewa allurar ba ta da illa ga rayuwar ’ya’yansu. Saboda haka bayan ya gama jawabi sai aka nemi ya shiga makwabtan asibitin domin diga wa yara kanana maganin da kansa.
Cikin gidajen da aka zaba wa Gwamnan har da gidan Malam Sani, amma sai Malam Sani ya ki amincewa Gwamnan ya shiga gidansa. Wannan al’amari ya faru ne a gaban manyan baki da suka hada da kwamishinoni da ’yan sanda da sojoji da ’yan jarida da kuma mazauna unguwar wadanda suka yi dafifi a kofar gidan domin ganin yadda al’amarin zai kasance.
Duk irin bakin da Gwamnan ya ba mutumin domin ya bar shi ya shiga cikin gidan ya ci tura domin ya dage cewa shi ba za a diga wa ’yarsa allurar ba. “Abin da ya sa na ki yarda Gwamnan ya shiga gidana shi ne saboda ba na son allurar Foliyo kuma ban yarda a diga wa ’yata ba. Baya ga haka kuma babu wanda ya fada min cewa Gwamna zai shiga gidana. Da a ce jami’an asibitin sun shaida min batun shiga gidan sai in fito a mutuncina. Amma ba su yi haka ba kuma ga shi ni ba bakonsu ba ne domin kuwa a gidana ma’aikatan suke bayan gida da Sallah. Saboda haka duk matsayin Gwamnan ina ganin bai kai makwabcina ba, domin duk abin da ya same ni sai makwabcina ya kawo min dauki kafin Gwamnan,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Sannan maganar da wani soja da ke cikin tawagar Gwamnan ya yi ne ya kara bata min rai har na ce ba zai shiga gidan ba. In ba rainin hankali ba, ta yaya zai ce wai duk mazauna Rigasa bakin haure ne. Nan take na ce da shi to, ko Shugaban kasa Jonathan ne ya zo nan ba zai shiga gidana ba, sai dai idan sun kashe ni. Ni ban san da zuwansu gidana ba domin da gajeren wando na leko waje. Shi ya sa na ce ba zai shiga ba. Na kuma shaida wa sojan cewa da ba don yana cikin kayan sarki ba, da na ba shi mamaki. Da Gwamna ya ga muna cacan baki sai ya rike min hannu yana tambayata ko na san shi. Na ce kwarai kuwa na sanshi. Na kuma ce ni ba ni da wata matsala da shi. Domin bai min laifi ba. Amma dai ni ba zan bar shi ya shiga min gida ba saboda ban san da zuwansa ba.”
Ya ce da ya ga jami’an tsaron da ke wurin sun ce za su yi amfani da karfi wajen yi wa yarinyar rigakafin cutar sai ya wurga musu ita domin su diga mata. “Na ba su ita ne ba don ina so ba, sai don kawai na ji hukuma za ta yi amfani da karfinta dama kuma abin da nake jira inji ke nan,” inji shi.
Daga bisani Gwamna Yero ya karasa gidan makwabcin Malam Sani wanda ba tare da ja-in-ja ba ya amince aka diga wa daya daga cikin jikokinsa.
Malam Saidu Jibril dattijo ne dan kimanin shekara 90, ya shaida wa Gwamnan cewa shi ba ya adawa da rigakafin domin an jima ana ba jikokinsa. “Ni ba na adawa da rigakafin Foliyo. Shi ya sa da Gwamnan ya zo gidana na karbe shi hannu biyu-biyu. Na shiga da shi cikin gidan domin ya ga yadda ya lalace. Bayan ya gani sai ya ba da umarnin a gina min sabon gida.”