Abin da ya sa na janye daga takarar Shugaban kasa – Tambuwal
Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana janyewarsa daga neman tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa. Maimakon haka, Aminu Tambuwal zai nemi tsayawa takarar gwamnan jiharsa ta Sakkwato ne kamar yadda Aminiya ta samu labari a ranar Talata da daddare.A wata sanarwa da ya fitar a ranar […]
Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana janyewarsa daga neman tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
Maimakon haka, Aminu Tambuwal zai nemi tsayawa takarar gwamnan jiharsa ta Sakkwato ne kamar yadda Aminiya ta samu labari a ranar Talata da daddare.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata da daddare mai taken: “Makomar Siyata” Aminu Tambuwal ya ce yanke wannan shawara ya biyo bayan tunutubar sassa da dama, kuma jingine kudirinsa na neman shugabancin kasa a karkashin Jam’iyyar APC ya yi ne domin amfanin jam’iyyar.
Tun bara aka fara rade-radin Tambuwal zai tsaya takarar shugabancin kasa tun kafin ya fice daga Jam’iyyar PDP wanda ya yi a ranar 28 ga Oktoban da ya gabata.
A ranar Alhamis din makon jiya ne wasu ’yan majalisa da abokan Tambuwal suka saya masa takardar nuna sha’awar tsayawa takarar domin yah ade da su Janar Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma Sam Nda-Isaiah don fafata neman tikitin jam’iyyar a zaben mai zuwa.
Washegari Juma’a a wajen wani bikin mika masa fom din, ’yan majalisar sun gamsu cewa Tambuwal yana da kwarewar da zai iya shugabancin Najeriya yadda ya kamata lura da gagarumar nasarar da ya samu a harkokin majalisar tun shekara ta 2003.
An ce Tambuwal yana samun goyon bayan Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko don tsayawa takarar Gwamnan, kujerar da Jam’iyyar APC ta riga ta tura shiyyar Sakkwato ta Kudu da Tambuwal ya fito.
Aminu Tambuwal ya ce, “Na jingine shiga takarar Shugaban kasa a yanzu ne saboda dama can ba na da wata sha’awa ta tsayawa takarar kowane mukami. Najeriya babbar kasa ce da za a iya sadaukar mata da duk wata bukata ta kashin kai ko siyasa. Duk abin da mutum zai zama a duniya yana hannun Allah ne kawai. Kuma Allah ne kawai Yake bayar da mulki ga wanda Ya so.”
Ya kara da cewa, “Na shiga APC ne don ingantata ta da gina ta. Don haka saboda amfanin jam’iyyarmu APC da kuma amfanin kasar nan, ina kira ga dukkan abokaina da abokan aikina na majalisa da magoya baya da masoya a fadin kasar nan su nuna min fahimta. Ba abu ne mai sauki ba daukar wannan mataki, kuma ina sane da damuwar da wadanda suka bayar da gagarumar gudunmawa da sadaukarwa ta jiki da dukiya da kwarewa don ganin na tsaya wannan takara a 2015.”
Aminu Tambuwal ya kara da cewa: “Na yi alkawarin yin biyayya ga jam’iyyarmu ta APC, kuma zan hada kai da kawunnaina da suke takarar shugabancin kasa: Ina nufin Janar Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Rochas Okorocha da kuma Mista Sam Ndah- Isaiah. Babu shakka dukkansu sun cancanta tare da dacewa da wannan kujera.”
Ya yi alkawarin sadaukar da kai da bayar da dukkan gudunmawa wajen ceto kasar nan daga mugun mulkin da ya lamunci almundahana da tsabagen gazawa da son kai da rarraba kan jama’a da take ciki a yanzu.
Lokacin da daya daga cikin ’yan majalisar da suka hada kudi suka saya wa Tambuwal fom din takarar, dan majalisa Zakari Mohammed ya ce za su mutunta shawarar shugaban nasu.
Sai dai magoya bayan Tambuwal da dama, musamman wadanda suka fito daga yankin Kudu maso Yamma ba za su ji dadin wannan shawara ba, sai dai shugaban majalisar ya ce a shirye yake ya yi wa kasa aiki a duk lokacin da bukatar haka ta taso.