Abin da ya sa na jingine kasuwanci na shiga siyasa – Alhaji Sadik

Alhaji Abubakar Sadik Muhammad sanannen dan kasuwa ne da ke harkar man fetur da gas daga Jihar Sakkwato, wanda bayan kammala karatunsa na jami’a ya fara aiki da wani kamfanin hada-hadar jiragen ruwa mai suna Firmsmerge Group da ke Legas. Daga nan ya koma ofishin matar Shugaban kasa marigayiya StellaObasanjo da aiki inda ya shekara […]

Abin da ya sa na jingine kasuwanci na shiga siyasa – Alhaji Sadik

Alhaji Abubakar Sadik Muhammad sanannen dan kasuwa ne da ke harkar man fetur da gas daga Jihar Sakkwato, wanda bayan kammala karatunsa na jami’a ya fara aiki da wani kamfanin hada-hadar jiragen ruwa mai suna Firmsmerge Group da ke Legas. Daga nan ya koma ofishin matar Shugaban kasa marigayiya StellaObasanjo da aiki inda ya shekara hudu. Kuma ya kafa kamfaninsa mai suna Westlake Engineering kuma shi ya shigo da wani kamfanin tsaro daga Landan mai suna Saladin. Wakili  a wasu kamfanoni, ya taba rike mukamai a Jam’iyyar PDP da CPC, kafin ya tsunduma APC a yanzu. Aminiya ta zanta da shi kan dalilan da suka sa yake neman takarar dan Majlisar Wakilai daga kananan hukumomin Kware da Wamakko a Jam’iyar APC:

Aminiya: A matsayinka na dan kasuwa me ya jawo ra’ayinka ka shiga siyasa?
Sadik: Gaskiya abin da ya jawo ra’ayina ga shiga siyasa shi ne neman kawo gyara, domin a can inda aka fito muna tare da ’yan siyasa mukan taimaka musu su samu nasara amma duk abin da muka nemi su yi na ci gaban al’ummarmu sai su ki aiwatar da shi. Kan haka na ga ya dace na fito don kawo sauyi mai alfanu ga jama’ata musamman mutanen Kware da Wamakko, zan bugi kirjina da karfi in gaya wa al’umma shirin da na yi don kawo masu ci gaba ba wani dan majalisar wakillai a Jihar Sakkwato da ya yi wannan shirin. Akwai wani tsari da na yi da muke kira da ‘Tsarin Ayukkana ga Al’ummata,’ da farko na dauki tsaro da kare rayukkan al’umma da muhallinsu wanda in na samu nasara akwai kamfanin da zan gayyato daga kasar waje domin taimaka min da shawarwari a samu hanyoyin kare al’umma ta magance matsalolin da ke sa a aikata laifi da amfani dabarun zamani don hana aikata laifi da shigo da harkokin shari’a. Na biyu akwai tsarin dawo da kimar ilimi da samar da hanyoyin ci gaba ga matasanmu, shi wannan ban jira wai sai na samu kujerar siyasa ba sannan zan yi wani hobbasa ba, a yanzu haka na sanya a duk mazabar a tattaro min sunayen matasa da ke bukatar karo ilimi tun daga jami’a har kasa amma ba su da halin yi domin in taimaka musu su cimma burinsu. Kuma ba zan kyale su ba har sai sun ci gajiyar karatunsu, kuma yanzu haka ina gina makarantar Islamiyya a garin Gidan Tudu kuma ina da kudirin gina wasu a sassan mazabuna. Kuma akwai wata makaranta da zan fara gyara ta kwanan nan, duk dai domin in farfado da ilimi a kananan hukumomin Kware da Wamakko. Na uku na samar da wani tsarin tattalin arziki da zai samar da aikin yi ga jama’ata da fito da kasuwanci na bai-daya a tsakanin kananan hukumomin da zai sa arzikinmu ya dada bunkasa. Ina mamakin yadda ’yan majalisarmu suka bar Gwamna shi kadai da aikin jama’a su kuma sun je suna kwana da dumama kujeru a zauren majalisa. Akwai bashin da hukuma ke bayarwa domin taimaka wa mata da kananan ’yan kasuwa da masu kananan sana’o’i, ban taba jin wani dan majalisa ya karbo wadannan kudade ba don agaza wa jama’arsa, kullum sai bukatarsu su zo garinsu talakawa su rika zuwa suna yi musu maula.
Na hudu farfado da aikin gona don samar da abinci mai inganci da kawar da hamada a yankunanmu. Na biyar sha’anin lafiya a yankinmu zai kasance bai-daya don za mu inganta asibitocinmu da kayan aiki na zamani. Na shida zan yi kokarin samar musu da yanayi mai kyau da ruwan sha mai tsabta, na yi alkawarin gina gidaje masu sauki ga jama’armu don raba musu a bashi ko kyauta da samar musu da kayan zirga-zirga da sauransu. Na bakwai na lura da ’yan aslin jiharmu da suka tafi ci-rani a Abuja da sauran wurare a kasar nan suna shiga halin kunci da wahala in suka fada hannun hukuma kan haka na bukaci samun sunayen kowane dan Kware da Wamakko da ya tafi yin kasuwanci a wani gari don in rika waiwayar yanayin da suke ciki domin ba su agajin gaggawa da sauransu. In har na samu nasara ba wata mazaba a kasar nan da za ta fi mu ci gaba da yardar Allah.
Aminiya: Duk lokacin da wani dan siyasa ya fito takara da wanda ke kan kujera a jam’iyyarsu, akan yi zargin yana da daurin gindin a sama, yaya abin yake a wurinka?
Sadik: Gaskiya ba wani daurin gindi da nake da shi, sai dai kawai abin da ya ja ni ga fitowa takara shi ne samar wa jama’ata mafita. Don na tabbata Mai girma Gwamna yana bukatar duk wanda zai kawo ci gaba, kuma gaskiya wanda ke kai ya kasa don haka ne nake shawartarsa ya bar wadanda ke iya yi su rika. Domin yana dan uwana ya sa na zo in taimake shi ga abin da ya kasa aiwatar wa jama’armu, saboda kada wani ya kawo maganar ki ko wani abu daban.
Aminiya: Kwanan nan aka soma taron kasa yaya kake kallonsa?
Sadik: Jam’iyyata ta dade da daukar matsaya wadda nake kanta wato taron shirme ne kawai da bata kudi har Naira biliyan bakwai da gwamnati za ta yi. Da wasu ayyuka muhimmai ta yi da kudin da ya fi kyau. Kuma kai ka san da aka ce akwai wasu fannoni da ba za a kutsa cikinsu ba, kuma ka san maganar banza ce wannan, dole a yi maganar hadin kan kasa da sauran abubuwa masu rikitarwa hakan kuwa jayayya kawai zai haifar da bata lokaci. Ra’ayina wannan taron bai da amfani kuma ba a yi wa Musulmi da Arewa adalci ba, ya kamata a gyara ba don muna kin kowa ba, sai don a bi cancanta da gaskiya da adalci.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno