Abin da ya sa na kafa makarantar kimiyya – Bello Kirfi

A ranar Asabar din da ta gabata ce Makarantar Kimiyya ta Giwo Science Academy wadda Wazirin Bauchi Alhaji Muhammadu Bello Kirfi ya kafa ta yaye dalibai 73 a karo na farko bayan kafa ta a shekara ta 2013.Da yake zantawa da wakilinmu a wajen taron wanda aka gudanar a harabar makarantar da ke kan hanyar […]

Abin da ya sa na kafa makarantar kimiyya – Bello Kirfi
Abin da ya sa na kafa makarantar kimiyya – Bello Kirfi

A ranar Asabar din da ta gabata ce Makarantar Kimiyya ta Giwo Science Academy wadda Wazirin Bauchi Alhaji Muhammadu Bello Kirfi ya kafa ta yaye dalibai 73 a karo na farko bayan kafa ta a shekara ta 2013.
Da yake zantawa da wakilinmu a wajen taron wanda aka gudanar a harabar makarantar da ke kan hanyar Ningi Alhaji Muhammadu Bello Kirfi, ya bayyana cewa ya kafa makarantar ce saboda ya lura babu wata kasa a duniya da za ta bunkasa sai da masu ilimin addini da na zamani, ya ce ilimi shi ne babban sinadrin da ke jawo ci gaba cikin hanzari a tsakanin al’umma.
“Na kafa makarantar ce da kudin aljihuna, kuma nan da lokaci kadan makarantar za ta zamo jami’a mai zaman kanta, saboda ilimi shi ne babban abin da ya kamata iyaye su ba ’ya’yansu a wannan lokaci. A matsayina na Wazirin Bauchi zan ci gaba da ba da dukkan gudunmawar da ta kamata domin ganin al’umma sun samu ilimi, domin yanzu duniya tana alfahari ne da masu ilimi,” inji shi.
Daga bisani ya mika godiyarsa ga gwamnatin Jihar Bauchi da sauran dimbin wadanda suka ba da kyaututtuka ga daliban da aka yaye a lokacin bikin. “Ina fata za su dage sosai a lokacin da suka shiga makarantun gaba da sakandare,” inji Wazirin.
Da yawa daga cikin daliban sun samu sakamakon jarrabawa mai inganci da za ta ba su dama su ci gaba da karatu a makarantun gaba da sakandare.
Da yake amsa tambayoyin wakilinmu a ofishinsa shugaban makarantar Alhaji Idris Yusuf Anchau ya bayyana godiyarsa ga daukacin daliban makarantar bisa kokari sosai da suka nuna a lokutan karatu.