Abin da ya sa na karbi belin Abdulrashid Maina —Ndume

Sanata Ali Ndume ya bayyana yadda ya shafe wata shida yana tunanin karbar belin Abdulrashid Maina, tsohon Shugaban Kwamitin Aiki Da Cikawa na Gyaran Fansho (PRT), wanda ke fuskantar zargin ta’ammuli da haramtattun kudade a gaban kotu. A watan Nuwamban 2019 Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da belin Maina amma […]

Abin da ya sa na karbi belin Abdulrashid Maina —Ndume

Sanata Ali Ndume

Sanata Ali Ndume ya bayyana yadda ya shafe wata shida yana tunanin karbar belin Abdulrashid Maina, tsohon Shugaban Kwamitin Aiki Da Cikawa na Gyaran Fansho (PRT), wanda ke fuskantar zargin ta’ammuli da haramtattun kudade a gaban kotu.

A watan Nuwamban 2019 Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da belin Maina amma ya shafe wata shida a tsare saboda gaza cika sharuddan belin da kotun ta gindaya masa.

Karbar belin Abdulrashid Maina da Sanata Ndume ya yi daga baya ya jawo cece-ku-ce. Ndume shi ne Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu, inda Maina ya fito.

Ndume wanda shi ne Shugaban Kwamitin Rundunar Sojin Kasa a Majalisar Dattawa ya bayyana wa ‘yan jarida yadda ya shafe wata shida kafin ya amcince ya karbi belin Maina.

Da yake bayyana dalilansa na karbar belin, Ndume ya ce, “Na farko ana bukatar ya kawo Sanata mai ci ya tsaya masa, kuma ni Sanata ne mai ci.

“Na biyu rashin lafiyarsa na kara tsanananta kuma yana bukatar kulawa.

“Na uku shi ne za a iya bayar da belin sa a kan zargin.

“Na karshe, ban ce kotu ta wanke shi ta sallame shi ba idan ya yi laifi. Idan an same shi da laifi a yanke masa hukunci.

Ya kara da cewa, “matsayi ne mai wuyar dauka. Hakki ne a kaina in wakilci na gari da mugu a Borno ta Kudu. Allah Ya shiryar da mu hanya madaidaiciya. Amin”.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna