Abin da ya sa na kekketa katin zama ta dan Jam’iyyar PDP – Obasanjo
A ranar Litinin ne tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar PDP, bayan da ya karbi bakuncin wakilan jam’iyyar na unguwa ta 11 da ke karamar Hukumar Abeokuta ta Arewa da ke Jihar Ogun, inda ya umarci shugaban jam’iyyar na mazabar Alhaji Surajudeen Oladunjoye ya kekketa katinsa na zama dan Jam’iyyar […]
A ranar Litinin ne tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar PDP, bayan da ya karbi bakuncin wakilan jam’iyyar na unguwa ta 11 da ke karamar Hukumar Abeokuta ta Arewa da ke Jihar Ogun, inda ya umarci shugaban jam’iyyar na mazabar Alhaji Surajudeen Oladunjoye ya kekketa katinsa na zama dan Jam’iyyar PDP.
Shugabannin PDP na mazabar sun ziyarci Obasanjo ne domin jin halin da ake ciki kan kasancewarsa dan jam’iyyar sakamakon yadda dangantaka ta yi tsami a tsakaninsa da Shugaba Jonathan.
Da yake mayar da jawabi Obasanjo ya ce kunnensa a bude yake, kuma ya samu labarin shirin shugabannin PDP na ladabtar da shi. Ya ce, “Kun yi min tambayoyi biyu, kuma zan amsa su yadda ya kamata,. Wannan Najeriya tamu ce duka, ba za mu bari a ruguza ta ba. Wannan shi ne Katina na zama dan Jam’iyyar PDP, akidata Najeriya ta kowa ce har da jarirai. Ba za mu bar wani ya ruguza ta ba, daga ko’ina ya fito, ko me yake da shi, domin idan suka ruguza ta alhakin ’ya’yanmu da masu zuwa a bayansu yana kanmu. Kuma tambayar a wace jam’iyya nake. Ina cikin rukunin mutanen da suka imanin cewa bai kamata a ruguza Najeriya ba. ’Yan kasuwa daga cikinku sun ga yadda farashi ke hauhawa. Masu canji kudade suna sayar da Dala daya kan Naira 150 a baya, yanzu ta tunkari Naira 250. Hakan yana nufin abin da kuke saye a Naira 150 zai koma Naira 250, wannan ba haka muke fata kasar nan ta kasance ba. Babu aikin yi, wasu mutane sun fara ruguza Najeriya kuma ba zan kasance cikin masu ruguza Najeriya. Sun kasa gane cewa saboda akwai Najeriya ne PDP ke raye, idan babu Najeriya ba za a samu PDP ba.”
A wasu bayanai da ya fitar a shafinsa na tiwita Obasanjo ya ce: “Zan gwammace keta katin zamata dan PDP maimakon in zauna ina gani Jonathan yana amfani da PDP da ci hanci yana kekketa kasata. Ina da martaba a ciki da wajen kasar nan da zan kare. Don haka zan gwammace in zauna ni kadai, maimakon in kasance a jam’iyya guda da Kashamu.”
Ya ce ya keta katin jam’iyyar ne a kokarinsa na kare martabar Najeriya, inda ya ce babu abin da ba zai yi ba don kare martabar kasar nan. Obasanjo ya ce duk da ya yayyaga katinsa na dan jam’iyyar ba zai bari wani ya hana shi magana ba, kuma a shirye yake ya tofa albarkacin bakinsa kan duk abin da yake bukatar sharhi ko bayyana ra’ayinsa.
Obasanjo ya zargi gwamnatin Jonathan da sanya siyasa a cikin duk wasu hukumomin Najeriya ciki har da sojoji wadanda ya ce sun zabi kasancewa wani bangare na PDP.
Bayanai sun nuna cewa, Obasanjo ya dauki wannan mataki ne domin kauce wa cin mutuncinsa ta hanyar dakatar da shi daga jam’iyyar da ake kokarin yi. Kuma tsohon Shugaban kasar ya ce, ba zai shiga wata jam’iyyar siyasa ba, sai dai zai ci gaba da zama dan Najeriya da zai yi aiki da kowa ba tare da lura da jam’iyyar da ya fito ba.
Lokacin da Pbasanjo ya mika katinsa na dan PDP ga shugaban mazabarsa kuma ya umarce shi da ya kekketa shi, magoya bayansa sun barke da murna inda suka rika yaba masa kan wannan mataki da ya dauka.
Kafin haka wasu daga cikin magoya bayansa da suka hada da korarren Oditan PDP na kasa Cif Bode Mustapha da tubabben Sakataren PDP na kasa, Yarima Olagunsoye Oyinlola da tsohon Gwamna Segun Oni da Dokta Femi Majekodunmi da Cif Jide Awosedo da sauransu sun fice daga PDP sun koma APC, bisa umarnin Obasanjon.
Sai dai kwana daya bayan keta katin zama dan PDP da Obasanjo ya yi, sai shugaban jam’iyyar a Jihar Ogun Adebayo Dayo ya ce jam’iyyar ta kori tsohon Shugaban kasar daga cikinta kan zargin yi wa jam’iyyar zagon kasa da kuma yadda yake caccakar jagoran jam’iyyar Shugaba Jonathan.
Matakin na Obasanjo yana samun goyon baya da suka daga magoya bayan PDP da abokan adawarta.