Abin da ya sa na ki amfani da adireshin intanet din gwamnati – Hillary Clinton

Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka Hillary Clinton wadda kuma ita ce matar tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton, ta fito ta bayyana dalilin da ya sa ta yi amfani da adireshin intanet na kanta domin gudanar da ayyukan gwamnati maimakon na gwamnati. Hillary ta bayyyan hakan ne bayan cece-kucen da wasu Amurkawa ke yi […]

Abin da ya sa na ki amfani da adireshin intanet din gwamnati – Hillary Clinton
Abin da ya sa na ki amfani da adireshin intanet din gwamnati – Hillary Clinton

Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka Hillary Clinton wadda kuma ita ce matar tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton, ta fito ta bayyana dalilin da ya sa ta yi amfani da adireshin intanet na kanta domin gudanar da ayyukan gwamnati maimakon na gwamnati.

Hillary ta bayyyan hakan ne bayan cece-kucen da wasu Amurkawa ke yi game da amfani da adireshin.
Ta ce: “Ba shakka ta goge dubban bayanai da ke cikin adireshinta na e-mail domin tasan ba su da amfani a gare ni. Wannan ne ya sa ban ga dalilin da zai sa na ci gaba da ajiye su ba domin nawa ne ba na gwamnati ba,” inji ta.
Tshowar sakatariyar ta kara da cewa masu cewa ta sa gwamnati ta yi hasarar bayanai masu amfani domin ko duk wani jami’in gwamnati yana amfani ne da adireshin e-mail mallakar gwamnati, “amma cikin wadanda ta yi amfani da su da kuma wadanda ta share ba daya da yake na gwamnati ne. Duka bayanai da suka shafe ta ne, ko kuma iyalan ta amma ba gwamnati ba,” inji ta.
Misis Clinton ta ce daga lokacin data rike mukamin har zuwa lokacin data sauka ta yi mu’amulla ne da sakonnin intanet har guda dubu 60 wadanda rabi daga cikin su na kashin kanta ne kuma ta share wadanda ita kanta ba su da muhimmaci a gare ta.
Masu fashin baki a harkokin siyasar kasar na ganin wannan na iya zame wa Hilary din matsala a kokarin da take yi na ganin a watan gobe ta bayyana aniyyarta ta tsayawa takarar Shugabancin kasar Amurka domin ko a halin yanzu ana ganin ita ce ’yar takarar da ke gaba-gaba wajen neman tsayawa a zaben fidda gwani na jam’iyyar su ta Democrat.