Abin da ya sa na musulunta – Direban Bishop Abioye

Wani tsohon direban Shugaban cocin Libing Faith Church, Bishop Dabid Abioye mai suna Nicholas Martins ya bayyana dalilin da ya sa ya bar addinin Kirista  ya rungumi Musulunci.Nicholas Martins wanda yanzu sunansa Isma’il Haruna, ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da yake murnar yin Juma’arsa ta 13 a matsayin Musulmi.Isma’il Haruna, ya ce ya […]

Abin da ya sa na musulunta – Direban Bishop Abioye
Abin da ya sa na musulunta – Direban Bishop Abioye

Wani tsohon direban Shugaban cocin Libing Faith Church, Bishop Dabid Abioye mai suna Nicholas Martins ya bayyana dalilin da ya sa ya bar addinin Kirista  ya rungumi Musulunci.
Nicholas Martins wanda yanzu sunansa Isma’il Haruna, ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da yake murnar yin Juma’arsa ta 13 a matsayin Musulmi.
Isma’il Haruna, ya ce ya fi jin dadi a cikin Musulunci fiye da zamansa a addinin Kirista. “Sunana a da Nicholas Martins amma na tuba na rungumi Musulunci. Kuma na musulunta ne a unguwar Games billage da ke Abuja. Ina cike da farin cikin kasancewa Musulmi,” ya fadi cikin murmushi.
Ya ce ya yanke shawarar barin addinin Kirista ne bayan aukuwar wani lamari da ya shafi badakalar kudi a cocin Libing Faith, Garden of Faith Church da ke Kaduna a Jihar Kaduna. Kuma duk da bai bayyana yadda badakalar ta auku ba, Isma’il ya shaida wa kafar labarai ta NAIJ.com cewa ya gamsu kan ya karbi addinin Musulunci ne bayan an kore shi daga aiki saboda ya amince an yi ba daidai ba. “Ni direban Bishop Abioye a Winners, kuma na fara aiki ne da cocin Canaan Land a shekarar 2001 inda na shekara biyar. Sai wani abu ya faru suka ce idan ka fadi gaskiya, wannan gaskiyar ce za ta kubutar da kai. Amma sai ya zamo ni kadai ne na tashi na fadi gaskiyar abin da ya faru kuma shi ne gaskiya,” inji Isma’il.
Ya ce, amma abin da ya ba shi mamaki bayan ya fadi gaskiya -wacce yake fata ta kubutar da shi- sai aka sallame shi daga aiki shi da abokan aikinsa biyu da suka fadi gaskiyar.
“Sun sallame mu, suka ce mu daina aiki da cocin. Sai na fahimci cewa ashe in na fada maka gaskiya amma ba za ka kubutar da ni ba,” inji shi.
 Ya ce sauran wadanda suka aikata wancan laifi an bar su sun ci gaba da aikinsu bayan sun yi rantsuwa da Baibul cewa ba su yi wannan laifi ba. “Ko a yau na san suna can; sun kyale su a can, amma mu da muka fadi gaskiya sun ki amincewa mu ci gaba da aikinmu,” inji shi.
Isma’il ya ce, wannan ne ya sanya ya dawo Abuja, kuma ya ce ya shafe shekara kusan tara kafin ya sake samun wani aikin.  Ya ce “Yanzu na musulunta saboda abin da ya faru. Kuma tun daga shekarar 2004  na daina zuwa coci har zuwa bana, na daina zuwa coci ne saboda na kebe kaina ina ta tunani.”
Ya ce an kunyata shi da ya zamo gaskiya ta kasa ceto shi. Ya ce a lokacin da ya fara sabon aikinsa ne ya fara yaba dabi’un wanda ya dauke shi a aiki. “Lokacin da na gan shi, na fahimci cewa wannan mutum hakika yana yin abin da Allah Yake so mu yi,” inji shi.
 Ya kara da cewa: “Akwai dimbin abubuwa da yake gani a yanzu da a baya bai ganinsu kuma bai ma sansu ba. An haife ni kuma na girma a Arewa. Na kai kamar shekara 28 a can, kuma da na dawo Abuja ne na fara sha’awar Musulunci a karshe na musulunta.”
Game da sabon addininsa, Isma’il ya ce yana cike da farin cikin kasancewa cikin Musulmi a Abuja, kuma game da azuminsa na farko a matsayin Musulmi ya ce:  “Wannan ne karo na farko da na yi azumi a matsayin Musulmi, kuma wannan ne karo na farko da nake Idi a matsayin Musulmi a wannan fili mai tsarki.” Ya ce ya gamsu cewa a yanzu ne yake wurin da ya dace, inda ya yi kira ga jama’a musamman Kiristoci su rika taka-tsantsan da mutanen da suke da’awar su masu gaskiya ne fiye da saura alhali suna aikata miyagun ayyuka.