Abin da ya sa na nada Nadada Sakataren Gwamnati – Gwamnan Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar ya ce ya nada Alhaji Muhammadu Nadada Umar a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi ne saboda kwazo da gogewarsa wajen sanin ayyuka da tsare-tsaren gwamnati domin kyautata rayuwar jama’ar jihar. Abubakar ya fadi haka ne lokacin da yake rantsar da sabon sakataren gwamnatin jihar ta Bauchi, yana mai […]

Abin da ya sa na nada Nadada Sakataren Gwamnati – Gwamnan Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar ya ce ya nada Alhaji Muhammadu Nadada Umar a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi ne saboda kwazo da gogewarsa wajen sanin ayyuka da tsare-tsaren gwamnati domin kyautata rayuwar jama’ar jihar.

Abubakar ya fadi haka ne lokacin da yake rantsar da sabon sakataren gwamnatin jihar ta Bauchi, yana mai cewa nadin nasa ya biyo bayan wadansu sauye-sauye ne da aka yi a baya-bayan nan, bisa wani yunkuri na sake fasalin gwamnati da nufin inganta ayyukan kyautata rayuwar jama’a.

Gwamna Abubakar ya ce nadin sabon sakataren Gwamnati wata hanya ce na daidaita al’amuran raya kasa, “Kafin ka ba mutum ya rike wannan ofishi tilas sai ka sami mutumin da yakware ya goge wajen sanin hada-hadar ayyukan gwamnati da yadda ake gudanar da su, saboda kwarewarsa ne yasa na nada shi akan wannan mukami”

 

Ya ce ofishin sakataren gwamnati ne ofis na kololuwa wajen gudanar da aikace-aikacen gwamnatin jihar, musamman ma lura da irin yadda ofishin ke kula da dukkan hidimomi da aikace-aikacen hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jiha, sai ya bada tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da bin matakan da suka dace domin gudanar da al’amura cikin inganci.