Abin da ya sa na rubuta littafi kan kiyaye hadura – Ibrahim Paul

Ibrahim Paul Yusha’u ma’aikacin Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa ne sannan a lokaci guda marubuci ne da ya yi wallafe-wallafe da dama. A cikin wannan tattaunawar da ya yi da Aminiya, ya bayyana irin aikace-aikacensa da abin da ya sanya shi yin rubuce-rubuce da kuma burinsa nan gaba. Ga cikakkiyar hirar:   A matsayinka na […]

Abin da ya sa na rubuta littafi kan kiyaye hadura – Ibrahim Paul

Ibrahim Paul Yusha’u ma’aikacin Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa ne sannan a lokaci guda marubuci ne da ya yi wallafe-wallafe da dama. A cikin wannan tattaunawar da ya yi da Aminiya, ya bayyana irin aikace-aikacensa da abin da ya sanya shi yin rubuce-rubuce da kuma burinsa nan gaba. Ga cikakkiyar hirar:

 

A matsayinka na ma’akaci mai sanya kayan sarki, me ya ja ra’ayinka zuw ga fara rubuce-rubuce?

To, da farko dai zan iya cewa wannan wata kyauta ce ko kuma baiwa daga Allah. Na biyu kuma shi ne, lura da irin aikin da nake yi (FRSC) sai na ga ya kamata a fito a rika wayar wa da jama’a kai ta hanyar rubuta littattafai. Wato abin da nake so in ce a nan, dukkanin littattafan da na rubuta, in ban da guda daya, duka suna sun shafi aikina ne.

Yawan hadurra da ake samu a hanyoyinmu wadanda suke janyo asarar rayuka da dukiyoyi kullum sai karuwa suke yi, wanda hakan yana matukar tayar min da hankali. To, a matsayina na ma’aikacin kiyaye hadari kuma ga shi Allah Ya yi min baiwar rubutu, sai na ce bari in dauki wannan fannin da ba kasafai ake samun haka ba don wayar da kan ’yan kasa.

 

Ko za ka bayyana mana kadan daga cikin dalilan da ke yawan janyo hadurra a manya da kananan titunanmu na Najeriya?

Dalilan na da yawa amma manya daga ciki sun hada da fashewar taya. Yawanci direbobinmu ba su kiyaye lokacin da taya za ta kare aikinta, ta yadda za a canza ta ko da ko a fuska suna ganinta kamar sabuwa. A ka’idar sabuwar taya shekara biyar ya kamata ta yi, daga lokacin da aka yi ta. To, direbobinmu ba su cika kiyaye wannan ba, idan ka yi musu magana sai su nuna maka ai rayuwar yanzu komai ana lallabawa ne. Kana lallaba kanka zuwa ga mutuwa ne ai in ba ka sani ba. Domin kana jefa rayuwarka da ta mutanen da ke cikin motarka ne ko da na fasinja ne ko ba na fasinja ba ne.

Matasala ta biyu ita ce, sai ka ga wasu suna tafiya ba tare da safiya taya ba ko kuma ka ga ita kanta safiyar ma ta tashi a aiki. Ka ga wannan shi ma hatsari ne babba. Kowane lokaci irin wadannan tayoyin na iya fashewa, musamman idan ana gudun wuce kima a lokacin zafi, tun da ka ga yanayinmu a nan kasar ya saba da yanayin kasashen da ke yin tayoyin. To wadannan da ma wasu dalilai da yawa suka sa na fara rubuta littattafai don wayar da kan direbobi da fasinjoji sanin abin da ya hau kansu.

 

Akalla zuwa yanzu ka rubuta littattafai kamar guda nawa?

Zuwa yanzu dai baya ga rubuce-rubuce da nake yi a jaridu daban-daban, na rubuta littattafai kamar guda shida wadanda aka wallafa su suka shiga hannun mutane kuma dukansu, in banda guda daya, a kan jigon da na ambata maka na yi su. Dukansu na rubuta su ne da Turanci, akwai ‘Importance of Automoblie behicles and Maintainance’ wanda irinsa ne na farko, wanda wani bakin fata ya rubuta ba tare da hada maudu’in da wani abu ba. Sai ‘Towards Sustainable Safe Dribing’ da ‘Recipe for Safe dribing’ da sauransu, sai kuma wanda ya fita daban a cikinsu wanda na ce maka a kan zaman lafiya na rubuta shi mai suna ‘Strategies for Tackling Insecurity in Nigeria.’ Sai kuma wasu da na ke kan rubutawa.

 

To, shi kuma wannan mai ya ja ra’ayinka zuwa ga rubuta littafin hanyoyin da za a bi don dakile ko magance rikice-rikice a Najeriya?

Ka san wannan kalubale ne da kusan ya zama ruwan dare ko’ina a duniya, wato kusan ko’ina da irin kalar rikicin da yake addabarsu. Mu a nan Najeriya kowa ya san muna fama da matsalar rashin tsaro da suka hada da na fashi da makami da satar mutane da kuma rikice-rikicen addini da na siyasa da kuma na kabilanci. Duka wadannan matsaloli ne da suka dade suna ci mana tuwo a kwarya, wanda kuma ya kamata a ce marubuta su rika bayar da gudummawarsu a wannan fannin wajen fito da hanyoyin da za su taimaka wajen samar da zaman lafiya da kuma dawwamarsa. Bai kamata shugabanni su rika kallon kansu a matsayin ‘ni dan Arewa ne, ni dan Kudu ne ko wani yanki ba.’ Kalli yadda makamai suka yi yawa a hannun jama’a, wanda hakan babbar barazana ce ga zaman lafiyar kasa. To, mece ce mafita dangane da ire-iren wadannan matsalolin? Shi ne abin da littafina mai suna ‘Strategies for Tackling Insecurity in Nigeria’ yake bayani a kai daidai gwargwadon fahimta.

 

Kasantuwar rubuce-rubucenka sun shafi hukumar da kake yi wa aiki kai tsaye, kai ne ke daukar nauyin wallafe-wallafen ko kana samun tallafi ne daga hukumarku ko wasu kungiyoyi?

Babu ko daya! Allah ne kawai yake dafa min. Wani lokaci ma idan na rubuta littafi na kira taron kaddamarwa sai ka ga mutane sun ki zuwa saboda gudun dan abin da za su bayar.

 

Wane kalubale marubuta ke fuskanta a Najeriya?

Maganar rashin kudi babban kalubale ne. Ya kamata gwamnati da kungiyoyi su rika taimakawa tun da muna da hazikan marubuta a Najeriya wadanda idan suna samun tallafi za su iya gogayya da sauran marubuta na duniya.

 

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume