Abin da ya sa na rungumi aikin gyaran mota – Gloria
Oke Gloria Ogechi mace ce ’yar kabilar Ibo da ta kwashe shekaru tana aikin gyarar mota a garurruwan Legas da Abuja. Ta zanta da Aminiya kamar haka: Aminiya: Mene ne tarihinnki?Sunana Oke Ogechi Gloria, bayan na kammala karatun a matakin Difloma a fannin na’ura mai kwakwalwa, sai aka ce min ko zan iya koyon aikin […]

Oke Gloria Ogechi mace ce ’yar kabilar Ibo da ta kwashe shekaru tana aikin gyarar mota a garurruwan Legas da Abuja. Ta zanta da Aminiya kamar haka:
Aminiya: Mene ne tarihinnki?
Sunana Oke Ogechi Gloria, bayan na kammala karatun a matakin Difloma a fannin na’ura mai kwakwalwa, sai aka ce min ko zan iya koyon aikin gyaran mota, idan na kammala za a rika biyana, sai na ga ai abin nema ya samu, don maimakon in rika yawon neman aiki a ofis ai gara in yi rungumi abin da ya zo min.
Aminiya: Wane irin aikin gyaran mota kike yi?
Ana kiran wannan aiki da suna “Sabis,” wanda yawanci a manyan gidajen sayar da man fetir ake samunmu. Watau ya hada da juyen bakin mai da canja taya ko yin faci da setin taya don kar ta yi rawa (Balansi) da kuma alayimen, watau daidaita sitiyari don kar ya rika jan matuki zuwa gefe.
Aminiya: Wane irin kaya ake sawa yayin da mutum zai fara aiki?
An fi so mutum ya sa wandon aiki, watau jins, da riga jacket mai aljihu da yawa da takalmi mai kauri maganin santsi da kuma tsumma don goge hannu idan an taba bakin mai ko giris, maganin hadari ko jin ciwo. Kuma tun da ni na yi karatu na san amfanin rigakafi, shi ya sa nake sa madubi don kare idanuna.
Aminiya: Iyayenki sun so ki yi wannan aiki?
Ba su so ba, amma da na dage sai suka hakura, don na ce ni fa ba zan taba raina aikin yi don in rufa wa kaina asiri ba. Tun da akwai wata mace da ta yi suna, don ita ce makanike ta farko a Legas, shi ya sa na ce ni ma zan yi aikin sabis. Kuma a yanzu na riga na iya.
Aminiya: Wane aikin kika fi son yi?
Duk ayyukan da mai mota ya zo da shi ina yi, ko juyen bakin mai ko a canza tsohon taya da sabuwa ko balansi ko kuma daidaita sitiyari.
Aminiya: Yaya kike yi da maza abokan aiki masu tsangwama?
Aikina na sa a gaba, don ban tsaya ina kula da masu tsokalata ba, na yi watsi da su, shi ya sa na kama hanya ta, su kuma suka suka raina kansu. Don na dage shi ya sa na yi saurin fahimtar aikin da a da ake ganin sai namiji kadai zai iya yinsa.
Aminiya: Kin iya amfani da duk wadannnan kayan da suke aiki da na’ura mai kwakwalwa?
kwarai kuwa, don aikin ba shi da wahalar da yake da shi a da, don kayan yanzu suna da maganadishu na na’ura mai kwakwalwa. Wannan ya saukaka aikin kwarai da gaske. Kuma kayan suna amfani ne da wutar lantarki.
Aminiya: Ko kina samun masu cewa mace ba za ta yi musu sabis ba?
kwarai, lokacin ina koyon aiki wadansu suna cewa ba zan yi musu sabis ko wani aiki ba, don wai kila ba zan iya kwancewa da daura notin ko taya da karfi kamar namiji ba. Amma daga baya har yau, akwai wadanda suke cewa idan ba ni ba babu wanda zai yi musu gyara, don ba abin da ya gagare ni.
Aminiya: Ko kin taba samun hadarin ko jin ciwon a wannan aiki?
kwarai ai aikin sana’ar hannu sai a hankali, domin sai an koka. Dalili shi ne, lokacin da zan yi wa wata mota sabis, sai notin ya ki kwantuwa, watau ya yi tauri, sai na sanya karfi, amma sai na buge hannuna, ganin haka sai na fito daga ramin karkashin kasa ina rike da hannuna, amma abin mamaki sai manajana ya ce in koma karkashin mota in kwance, ya ce aikin ya gaji-haka. Abin ya ba ni mamak,i don na yi tsammanin za a ce in tafi gida sai gobe. (Dariya), tun lokacin sai na kara kiyayewa.
Aminiya: Yanzu wace mota kike yi wa sabis?
Wannan motar sunanta Toyota Tundra, kuma sabis za a yi mata na gaba daya: Watau canza taya da yin balansi da juyen bakin mai da kuma daidaita sitiyari. Kuma na kwance tayoyinta na baya, sannan abokin aikina ya kwance na gaba.
Aminiya: Wane kira kike da shi ga na baya masu cewa su aikin ofis kadai za su yi?
To ina aikin yake? Wanda ma suke yin aikin da yaya ake biyansu? Amma aikin hannu ai yanzu shi ne mafita, kana kammalawa a biya ka.
Aminiya: Mene ne burinki?
Burina shi ne in samu wurina, sannan in koyar da matasa, musamman ma mata. Kuma kamar yadda manajana Mista Adedeji Adeola ya ce, suna iya koya wa mace ko namiji wannan aiki.