Abin da ya sa na shiga kama ’yan fashi – Shehu Aljan

Shehu Musa Aljan jagoran wata kungiyar banga ce da ke  kama barayi musamman ’yan fashi da makami da barayin shanu. A makon shekaranjiya ya kama wasu mutum shida a wasu yankunan Jihar Filato, inda ya mika su ga jami’an tsaron musamman (STF) a Jos. Wakilinmu ya  zanta da shi don jin inda ya kamo wadannan […]

Abin da ya sa na shiga kama ’yan fashi – Shehu Aljan

Shehu Musa Aljan jagoran wata kungiyar banga ce da ke  kama barayi musamman ’yan fashi da makami da barayin shanu. A makon shekaranjiya ya kama wasu mutum shida a wasu yankunan Jihar Filato, inda ya mika su ga jami’an tsaron musamman (STF) a Jos. Wakilinmu ya  zanta da shi don jin inda ya kamo wadannan mafasa da yadda yake gudanar da aikinsa.

Daga wane wuri ka kamo wadannan mutane da ake zargi da satar shanu?
Na kamo wadannan mutane a yankin Shendam da Kurgui kuma cikinsu akwai kabilu uku, wato Tarok (Yargam) da Bafullace da kuma Bahaushe daya. Kuma na kama su ne lokacin da biyu daga cikinsu suka tsare hanya za su fara karbar dukiyar jama’a, sai muka diro suka fara da mu muka yi arangama, muka ci karfinsu muka kama su da hannu, wasu kuma suka gudu. Saura kuma mun bi ta hikima ne dama ina nemansu sai na bi kasuwar da suke ci, na samu nasarar kama su da taimakon wasu.
Da wadanne irin makamai kuka kama su?
Makami duk makami ne, amma mun kama su da bindigogi kirar gidane masu aiki da harsashin bindigogin G3 da sauransu. Kuma akwai wasu makaman da suka bisne sun ce za mu je mu tono su, saboda suna da tsari iri-iri kafin su fita aiki, don gujew a abin da zai iya zuwa ya dawo.
Ko kana samun tallafin gwamnati ko al’umma wurin da kake gudanar da wannan aiki?
Ra’ayi ne kurum ya sa muke wannan abu, don ni gwamnatin Najeriya ba ta taba ba ni kwabo ba, kuma ba na kama masu laifi na dauke su don za ga kan wasu saboda a ba ni taimako. Ni da yarana ra’ayi ne kurum ya sa muke wannan aiki, kamar yadda mafarauci ke yi, mukan shirya kanmu da gidajenmu, sai mu fita aikin kuma mu samu nasara, idan mun gama sai kowa ya fita wurin neman abincinsa.  Yawancimu ’yan kasuwa ne, wasu kuma masu sana’ar hannu. Sha’awa ce tasa muke wannan aikin saboda ganin za mu iya da kuma ganin yadda haka siddan mutane suna zaune lafiya, sai bata gari su auka musu ko su tsare hanya su kwace dukiya, wani lokaci har su lahanta mutane ko su kashe saboda rashin imani da kwadayin kayan mutane. Da farko ba irin sharrin da masu laifi ba su hada kai da bata gari an bi ni da shi ba, amma da aka ga gaskiyar lamari ne yanzu hukuma ke hada kai da ni kuma ake samun nasarar a fannoni da dama.
Yaya kuka yi da jami’an STF da kuka mika musu wadanda ake zargin a nan Jos?
Dama muna aiki tare da su, akwai wadanda ke cikin kungiyata muna tare kullum, kuma ba mu gama aiki ba sai da na tabbatar da cewa sun fito da duk makamansu. Kuma sai na sa ido wurin tabbatar da ganin an kai su kotu, saboda ni ba na kashe mutum kuma ba na so na kama a kashe ba a kai kotu ba. Saboda gudun kuskure ko daukar hakkin wanda bai ji ba bai gani ba. Kuma ba ni da matsala da jami’an tsaro a yanzu, matsalata daya ba a agaza min don bunkasa aikin. Idan da a ce Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya zai san wannan aiki da nake yi na san zai taimaka na samu tallafi da duk kariyar da ta dace. Saboda akwai mutane marasa kishi a cikin aikin tsaro a wannan lokaci, wasu zuciyarsu ke gaba ba son ci gaban jama’a da kasa ba. Wannan ya sa a kullum ake samun cikas a fuskar tsaro. Gwamanati na kashe kudi marasa kishi na zagon kasa suna arzurta kansu. Kai akwai wadanda wannan aiki da muke yi bai dame su ba, ji suke yi kamar su hana mu ko kamar su yi mana sharri kamar yadda ya yi ta faruwa a baya, amma Allah Ya tserar damu aka fahimci gaskiyarmu, saboda an lura muna da kishin kasa da tausayin jama’a. Ina aiki kamar tsuntsu, yau ina Kaduna, gobe ina Filato, jibi ina Bauchi, yanzu ina nan gobe na yi can, shi y asa ake ce min aljan. Kuma ba abin da ya dame ni kowane addini kake ko kowace kabila kake idan dai kana aikata laifi, muka hadu zan kama ka in ba hukumar da ta dace. Ni mai laifi nake magana dan fashi da makami. Kuma rashin kunyar masu aikata laifi tasa na shiga wannan aiki saboda yadda a baya suka damu yankinmu, da na fara aiki ta Bauchi na fara a karamar hukumata ta Toro. Da na fara sai da aka yi wata biyar ba wanda ya tare hanya kafin na shigo Jihar Filato da Gombe ina bin hanyoyi.
A cikin ayarina ba irin kabilar da babu, kuma sai mu yini mu kwana muna aiki ba abin da muka ci har sai mun kai ga nasara. Kuma ta’addancin da ake yi a kasar nan wani lokaci hada kai ake yi tsakanin kabilu daban-daban a gwara kan mutane inda ake yi musu sata sannan a dawo a hada kai da su a gwara kan al’umma su yi ta yakar juna suna sace dukiyar jama’a.
Musamman a Jihar Filato hada kai masu laifin ke yi su dawo su haifar da gaba a yi ta yakar juna ana ganin kamar kabilanci ne ko addini, alhali akwai masu ci da ceto da fitina, ya kamata gwamnati ta rika aiki da jami’anta na ciki da tsarkake kowane aiki don yi wa tukar da ta cukuikuye harkar tsaro a kasar nan hanci. Idan ba an yi nazari ba, kullum za a yi ta asarar kayan aiki da jami’an tsaro da talakawa ba tare da fahimtar komai ba.
Shawarata a gyara fasalin tsaro a bar kowane jami’i ya yi aikinsa yadda ya dace, kuma a sa ido a yi waje da batagari don kada alhakin na kirki ya bata niyyar gwamnati ta alheri wajen kare jama’arta da dukiyarsu.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno