Abin da ya sa na shiga kera injin casa – Dandago
Alhaji Wada Shehu Dandago fitacce ne a sana’ar walda da kera injinan casar kayan amfanin gona, inda ya kafa masana’antar kera injinan aikin gona mai suna; ‘Dandago Agricultural Machinery Co.’ a Jihar Kano. Aminiya ta tattauna da shi kan dalilin da ya sa yake kera injinan casa da na gyara amfanin gonar: Mene ne takaitaccen […]
Alhaji Wada Shehu Dandago fitacce ne a sana’ar walda da kera injinan casar kayan amfanin gona, inda ya kafa masana’antar kera injinan aikin gona mai suna; ‘Dandago Agricultural Machinery Co.’ a Jihar Kano. Aminiya ta tattauna da shi kan dalilin da ya sa yake kera injinan casa da na gyara amfanin gonar:
Mene ne takaitaccen tarihinka?
Sunana Alhaji Wada Shehu Dandago, an haife ni a Unguwar Dandago a cikin birnin Kano, kuma a nan na rayu har zuwa girmana. Bangaren karatu kuma, na fi karfi wajen karatun addini, na yi makarantar Aliya da ke birnin Kano, sannan da mu aka bude makarantar Aliyu bin Abu Dalib da ke hanyar Zariya, sai karatun da na yi a wajen manyan malaman addini wadansu Allah Ya yi musu rasuwa, Allah Ya jikansu. Ban yi karatun zamani sosai ba, amma Allah Ya yi min baiwa mai yawa.
Bangaren sana’a na taso na samu gidanmu ana kasuwanci da noma don haka na koyi kasuwanci da noma tun ina karami. Sana’ar walda na koye ta a wajen yayana daga baya na je na koyi gyaran mota da girmana sai kuma wacce ake ciki yanzu wanda ta samu ne ta hanyar jajircewa da mai da hankali.
Me ya ja hankalinka ka bude masana’antar kera injinan aikin gona?
Babban abin da ya ja hankalina na fara kera injinan aikin gona shi ne; lokacin tsohon Shugaban Kasa Janar Ibrahim Babangida, na yi noman alkama kuma mun samu amfani sosai, amma abin da ya ba mu matsala a wancan lokaci shi ne injin cashe alkamar. Sai ka yi kwana 14 kana bin layi a injin da zai cashe maka alkamar, wani lokaci ma sai ka tura wani ya kwana yana jiran layi ya zo kansa kada wani ya tafi da injin zuwa gonarsa. Wannan ya sa na fara tunanin mafita. Tunda Allah Ya ba ni basira kuma ga shi na iya sana’o’i iri-iri musamman kanikanci da walda, sai na fara tunanin in kera wani inji da zai taimaka min wajen aikin gona.
Akwai wani inji da aka kawo daga kasar Indiya mai suna ‘Suwaraj’ tun lokacin sai na fara nazari yadda zan kera irin wannan inji, daga baya sai na kera wani karamin injin cashe masara da gero da sauransu a matsayin gwaji kuma Allah Ya taimake ni injin ya yi aikin da ya kamata. Daga baya na yi babba wanda na sayar wa wata kungiyar manoma da ke garin Karaye.
Yaushe ka fara sayar da injinan?
Kamar yadda na shaida maka akwai Kungiyar Manoma ta Karaye wadda marigayi Farfesa Falaki, ya hada ni da su, su ne suka fara saye. Daga nan sai wani mutumin Gombe mai suna Benjamin Adam da wani Danladi Muhammad da suke karatu a kasar Ghana, Benjamin zai yi bincike a kan masara, Danladi kuma a kan alkama, sai na kera musu injinan da suka yi bincikensu.
Kawo yanzu injina iri nawa kuka kera?
Daga baya mun sake fasalin injin farko muka mai da shi “fibe in one” mai sarrafa amfanin gona biyar kamar; injin casar hatsi irin su gero da masara da dawa da waken-suya da alkama “Multi crop Thesher” da injin nika kara “Crop Residue Crushing Machines” da injin abincin kaji “Feed mills/mider crusher” da injin man gyada da injin gyaran shinkafa kamar zazzabe “Rice parboile” da na busar da ita “Drier” da na goge ta ta fita tsaf “Rice cleaner” da sauransu.
Manoma suna samun saukin gyaran amfanin gonarsu a farashi mai rahusa ta wadannan injina.Sannan mun samar musu injin nika kara, don a baya ana zubar da kara ne, amma yanzu ya zama kayan kudi monama suna nika shi su sayar da shi ga masu kiwo.Idan mai kiwo zai ciyar da saniya a kan Naira dubu, to yanzu bai wuce ya kashe Naira 180 kacal ba, ka ga sauki ya samu ga masu kiwo, ga riba ga manoma.
Ta wacce hanya sana’arka take samar da aikin yi?
Idan muka dauki injin nika kara kawai akalla mutum biyar za su yi aiki a karkashinsa, shi kansa karan kasuwarsa ta bude ana samun dilallansa wanda a baya a banza ake kona shi. Sannan masu kiwon shanu sun samu karin riba da sauki, don idan za ka iya ciyar da shanu biyar ne, to yanzu za ka iya ciyar da sama da 10 domin bai wuce saniya ta ci karan Naira 180 ba. Sannan mun hada kai da kungiyoyin sa-kai masu taimakon al’umma wajen yi musu ragi a kan farashin kasuwa, domin su taimaka wa matasa wajen koyar da su sana’o’i da ba su kayan aikin da muke kerawa.
Akwai manyan makarantu da kuke hadin gwiwa da su wajen bincike?
Akwai makarantun da suke turo dalibansu suke samun horo (IT) na tsawon shekara guda, su tafi wadansu su zo. Daga cikin makarantun akwai Jami’ar Bayero da ta Ahmadu Bello da Jami’ar Kimiyya da Kere-Kere da ke Wudil da wasu kwalejojin ilimi. Kuma a shirye muke mu yi hulda da duk wata cibiyar bincike ko hukuma domin samar da ci gaban kasa.
Kawo yanzu wadanne nasarori kuka samu?
Alhamdulillahi mun samu nasarori domin mun fara daga gwaji ga shi yanzu muna da masana’anta ta kashin kanmu. Kuma ’ya ’yana sun taso, duk abin da nake yi suna yi, yanzu ina da mataimaka.
Amma babbar nasarata ita ce idan na tuna tun 1976 nake koyar da mutane sana’a, wannan yana sa ni farin ciki. Nasara ta gaba ita ce kayan da muke kerawa suna isa har kasashen ketare kamar Jamhuriyar Nijar da sauransu, ba iya Kano ko jihohin Najeriya ba a’a har waje ana saye ko a sa mu yi wasu injina na musamman.
Shin akwai matsalolin da kuke fuskanta a sana’ar?
Babbar matsalarmu ba ta wuce ta wutar karancin lantarki ba.
kO kuna tallata kayayyakinku a kafafen watsa labarai?
Gaskiya ba mu taba tallata hajarmu, dalili shi ne a yanzu ma wadanda muke mu’amala da su suna da yawa, kuma harka ce ta kira sai kana da kayan aiki a wadace sannan za ka iya biya wa abokan hulda bukatarsu. Da zarar muka fara talla to za mu gayyato mutanen da ba za mu iya biya musu bukata ba, ka ga sai ya kasance mun lalata harkarmu. Muna bi a hankali idan lokaci ya yi za mu shigo cikin al’umma gadan-gadan. Shi ya sa za ka ga masu sana’ar hannu suna saba alkawari saboda rashin tsari da hadama. Amma idan kana da tsari komai naka zai tafi daidai don haka muke bi a hankali.
Kana da shawara ga jama’a?
To shawarata ba ta wuce mutane su tashi tsaye a kan tarbiyyar ’ya’yansu ba, kuma su yarda su kai su su koyi sana’a. Idan ba mu yi haka ba, to zai yi wahala mu fita daga cikin halin da muke ciki na rashin tsaro da talauci da suke addabarmu a Arewa.