Abin da ya sa na shirya fim da din Ekuestrian Elegance – Farfesa Abdalla Uba Adamu 01

A makon jiya ne muka kawo muku kashi na daya na tattaunawar da muka yi da Farfesa Abdalla Uba Adamu dangane da fim dinsa na Ekuestrian Elegance. A yau kuma za mu karkare da amsoshin wadannan tambayoyin: Ko akwai wani biki na musamman da ka shirya don kaddamarwa ko gabatar da fim din ga al’umma?A’a, […]

Abin da ya sa na shirya fim da din Ekuestrian Elegance – Farfesa Abdalla Uba Adamu 01

A makon jiya ne muka kawo muku kashi na daya na tattaunawar da muka yi da Farfesa Abdalla Uba Adamu dangane da fim dinsa na Ekuestrian Elegance. A yau kuma za mu karkare da amsoshin wadannan tambayoyin:

Ko akwai wani biki na musamman da ka shirya don kaddamarwa ko gabatar da fim din ga al’umma?
A’a, babu. Babu maganar gabatarwa ko kaddamar da shit a hanyar biki a gaban jama’a. Amma kamar yadda na ce, na rarraba shi wurare da dama a duniya a matsayin ma’adanin tarihin rayuwar Hausawa, kuma ana amfani da shi a koyarwa. daya daga cikin mutanen da na bai wa fim din wacce ta ke koyarwa a Jami’ar Calinfornia da ke Los Angeles, ta aiko mini da wata wasika, wadda ke nuna yadda ta gamsu da fim din, har ma take cewa za ta yi amfani da shi wajen koyarwa a jami’arsu.
Bayan wannan, da ma ni ba abokin kaddamar da abubuwa ba ne, saboda haka ko da babu wannan takunkumin, to ba zan kaddamar da fim din ba. Amma in da zan samu yadda na ke so, da sai a fitar da fim din a kan farashi mai rahusa ta yadda kowa zai iya mallakarsa – domin don a ilimintar aka yi, ba don a yi riba ba.
Amma akwai madadin fim din, wanda shi ma na taimaka wajen yinsa. Wannan kuwa shi ne wanda Ibrahim Ado Kurawa, Babban Jami’in Bincike na Gwamnatin Ibrahim Shekarau ya sa aka yi, kuma aka watsa a intanet domin duk duniya ta gani, kyauta.
Me ya sanya ka zabi ka shirya fim din nan da Turanci, maimakon Hausa, yaren da mafi yawan al’ummar Kano ke amfani da shi?
Dalili shi ne, ban yi fim din da niyyar ya makale a Bata ko kofar Wambai ba. Hasali ma dai ban saki fim din ba, kuma ba zan sake shi ba, domin dama can ba don kudi aka yi shi ba. Amma na rarraba shi a wurare da dama a duniya, takamaimai Amurka, Ingila, Jamus, Faransa, Senegal da South Africa. Idan aka yi da Hausa, wadannan mutanen ba za su fahimce shi ba, duk da cewa an yi shi ta yadda ko da ba ka jin abin da ake fada, za ka iya bin abin da ke faruwa, domin na bi salon yin fim da ake kira ‘Cinema berite’ watau fim din da ya nuna gaskiyar lamarin abu.
Idan za mu waiwayi harkar fina-finan Hausa jiya da yau, yaya kake ganin ci gaba ko akasin haka ga harkar?
Na sha karanta hirarraki da aka yi da ’yan fim inda suke fadin irin ci gaban da aka samu a sana’ar. Ni kuwa ban ga wani ci gaba ba. Kyamarori da sauran na’urorin sarrafa abubuwan ba su samu ba saboda fina-finan Hausa. Dama can suna nan, saboda haka ba fina-finan Hausa ne suka kawo su ba ballantana a ce an samu ci gaba. Misali, sai da kyamara mai daukar hoto mai nauyin HD ta jima a kasuwa kafin a fara amfani da ita a fina-finanmu. Kusan duk wani nau’i na fasahar ci gaba da sana’ar dama yana can – samun damar budaddun hanyoyin sadarwa ne ya sa ake amfani da wadansu a fina-finanmu, sannan ake ganin kamar ci gaba ne.
Amma fim labari ne – ba na’ura ba, ba wani siddabaru ba. A wannan ma’aunin, babu wani ci gaba da aka samu. Fim din Hausa na bidiyo da ya fara shiga kasuwa shi ne Turmin Danya (Daraka: Salisu Galadanci), a watan Maris 1990. Labarin soyayya ne. Zuwa yanzu, 2011, labaran soyayya ne ke jagorancin fina-finan Hausa – wane ci gaba ke nan aka samu? Labaran duk iri daya ne – babu yadda za ka kalli fim din Hausa ka ma gane ko wane fim ne, domin jaruman su ke nan dai ake ta juya su, labarin daya ne ake ta dumama shi. Har yanzu an kasa shiga wadansu fannonin yin fim. In kuma ka ce a shiga, ’yan fim sai su ce su kasuwa suke yi ma wa, saboda haka wanda duk zai yi wani abu wanda ba shi kasuwa take so ba, to ya zuba nasa jarin ya yi, ko kuma ya yi shiru. Shi ya sa muka zuba namu jarin muka yi fim din Ekuestrian Elegance – domin bai wa mutane misalin irin abin da ya kamata a dinga sirkawa da shi.
A yanzu haka Adamu Muhammad Kwabon Masoyi shi ma ya yi fina-finan talabijin guda bakwai a kan abubuwa masu amfani, wadanda za a nuna nan ba da dadewa ba. Wannan shi ne ci gaba, amma ba soyayya da rawa da wakokin nanaye ba, wadanda ba ma za ka iya tuna ko guda dubu nawa aka yi ba.
Daga fim din Ekuestrian Elegance sai kuma wanne za ka shirya?
Har ma na shirya, na gama. Wannan kuwa shi ne fim game da wakokin yara na gargajiya, kamar irin su kadangare Da Linzami, Najajjeni Gidan Gauro, belingo, da sauransu. Mun yi makonni uku muna atisaye a wata makaranta a Kano da Dutse tare da malaman yara guda 18, sannan muka je situdiyo muka dauki wakoki guda 27, na bidiyo da kuma na sauraro. Sunan fim din Hausa Children’s Songs from Northern Nigeria. A Dutse, a sarari muka dauki wakokin. Amma saboda ni makararren Bafulatani ne (watau Bafillace gaba da baya, amma ba na jin yaren) sai na hada da wakokin Fulani guda takwas. Wadanda suka dauki nauyin wannan fim din su ne Abu Dhabi Authority for Culture and Heritage, a kasar United Arab Emirates. Shi ma fim din ba a yi shi don a sake shi a Najeriya ba – har yanzu ma ba wanda ya taba ganin fim din. A kasar Faransa zai fita a matsayin DbD, wanda zai hada da wakokin wadansu yaran daga wadansu sassan na duniya.
Sannan daga ranar 4 ga watan Maris na 2013, na yi koyawarwa ta wata uku a Jami’ar Warsaw da ke kasar Poland. daya daga cikin abin da na koyar ya hada da wani fim wanda na fara dauka wanda na kira Al-Hausawi Al-Hindawi – Hausa Translinguistic Phenomena. Fim din a kan Nazeer Magoga ne wanda ke gabatar da shiri a Radio Kano FM da Indiyanci, kuma yana yin wakoki da yaren Indiyanci. Ina nazari a kan yadda ya koyi yaren ta hanyar kallon fina-finan Indiya kawai, kuma har ya zama gwani.
Ko wace shawara za ka ba ‘yan fim din Hausa domin ganin sun samu nasara a harkar?
Ai nasara sai dai su dada gode wa Allah, domin an samu kuma ana samu iya gwargwado. Sana’ar ta yi wa da yawansu komai da komai. Sai su ci gaba a kan tafarkin da suka saka gaba, domin wannan shi ne hanyar samun nasarar duniya.
Ko akwai shawarar da za ka ba Gwamnati da ’yan kasuwa dangane da harkar fim?
Babu. Duk wata shawara an bayar a baya. Daga gwamnatin har ’yan fim din ba wanda ke bukatar wata shawara. Kamar yadda na ce, su dai ’yan fim sai godiya ga Allah. Gwamnati kuma na iya kokarinta, to amma ba ’yan fim ne kadai a gabanta ba – akwai abubuwa da dama da suka addabi rayuwa.