Abin da ya sa na shirya fim din Ekuestrian Elegance – Farfesa Abdalla Uba Adamu

A makonni biyu da suka gabata ne aka gudanar da wani gagarumin taron tunawa da Farfesa Muhammad Hambali Jinju a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, inda masana harsunan gida da marubuta da dimbin al’umma suka halarta. A yayin gudanar da taron ne Farfesa Abdalla Uba Adamu na Jami’ar Bayero Kano ya nuna shahararren fim dinsa […]

Abin da ya sa na shirya fim din Ekuestrian Elegance – Farfesa Abdalla Uba Adamu

A makonni biyu da suka gabata ne aka gudanar da wani gagarumin taron tunawa da Farfesa Muhammad Hambali Jinju a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, inda masana harsunan gida da marubuta da dimbin al’umma suka halarta. A yayin gudanar da taron ne Farfesa Abdalla Uba Adamu na Jami’ar Bayero Kano ya nuna shahararren fim dinsa mai suna ‘Ekuestrian Elegance.’ Fim din na tarihi ne wanda ke nuna zahirin yadda ake bukukuwan hawan Sallah a Kano. Wakilinmu ya gana da shi, inda ya yi bayani game da fim din da sauran muhimman bayanai da suka shafe shi shi kansa da sauran al’amura masu muhimmanci:

Wane ne Abdalla Uba Adamu?
An haife ni a garin Kano, a unguwar Daneji ranar Laraba 26 ga Afirilu, 1956. Watau a yanzu dai na shiga shekara ta 58 a duniya.
Na yi makarantun firamare na dandago, na koma Tudun Madatai, duk a Kano. Na shiga Makarantar Gwamnati ta Gwale a 1968, na gama 1973. Mu ne muka bude Kwalejin Sharar Fagen Shiga Jami’a ta Kano State College of Adbanced Studies, watau CAS, a Nuwamba 1973. Na shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a 1976 na gama 1979. Na karanta digirin horar da malaman kimiyya, inda na zabi ilimin kimiyyar halitta.
Bayan hidimar kasa a Imo, na fara aiki a Jami’ar Bayero a watan Agusta 1980, a tsangayar horon malamai. A shekarar 1997 na zama cikakken Farfesa a fannin ilimin manhajar kimiyya (Science Education and Curriculum Debelopment). A lokacin ina da shekaru 41, wanda ya sa na zama Farfesa mafi karancin shekaru daga rukunin Farfesoshi ’yan Kano.
Na yi aikin shekara guda a Jami’ar California da ke Berkeley daga 1991 zuwa 1992, sannan kuma na yi rasidan a wata cibiyar nazari a Bellagio da ke kasar Italy a 1993. Ragowar rayuwar kuma an cika ta da almajirci da halartar musabakokin ’yan zamani a kasashe kamar Amurka, Ingila, Jamus, Morocco, Senegal, Ghana, Nijar, Egypt, Ethiopia, Kenya da  France.
Amma duk da haka ban bar nazarin horon malamai ba, domin a yanzu haka ma ni ne shugaban sashen horon malaman kimiyya da fasaha na Jami’ar Bayero. Wani bangare kuma da nake da sha’awa a kai sosai, shi ne ilimin ajami da kuma yadda za a yi amfani da shi wajen ilimintar da ’yan uwana almajirai da gardawa da ke karatu a tsangayun kasar nan, a inda nan ma ina yin wani yunkurin.
Na samu goyon baya sosai daga abokan aiki, domin a yanzu ina daga cikin malaman da ke koyarwa a sashen ilimin sadarwa na Jami’ar Bayero.
A tsawon lokaci, ana damawa da kai ta bangaren harkokin fina-finai da kade-kaden Hausa, me ya ja ra’ayinka zuwa wannan fage, duk da cewa kai shahararren malamin jami’a ne?
Kada ka manta, malamin jami’a manazarci ne. Da na zama Farfesa a 1997, sai na ga in da tsawon rai, to ina da ragowar shekaru 24 kafin in yi ritaya. A gaskiya a lokacin sai na ga kamar na biya duk wani bashin horo da tsangayar horar da malamai ta yi min, saboda haka sai na ce bari in canza sheka, in kuma gwada ilimin binciken da na koya a wani fannin. Bayan nazari mai tsawo sai na kutsa kai cikin nazarin al’adun jama’a, wanda da Turanci ake kira ‘Cultural Studies.’ Dalilai biyu suka sa na yi wannan.
Na farko, ina da sha’awar abubuwan da suka shafi al’adu – daga rayuwar zamantakewa zuwa sarrafa tunani ta hanyar adabin zamani kamar labarai, fina-finai da kuma kade-kade. Ba kuma wai kawai na Hausawa ba, a’a, na kowacce al’ummar duniya. Na biyu shi ne, kutsowar Turawa cikin nazarin sarrafaffen adabin Hausa na zamani. Tun wajen 1997 suka fara lekowa domin su ga wacce irin wainar ake toyawa a sana’ar littattafan soyayya? Shi ya sa na yi wuf na shige lamarin domin ta haka za su zo, su yi tsokane-tsokanen su, sannan su ba abin da muke yi wata ma’ana ta daban. Ta haka in ma zagi ne, kushe ko yabo, gara mu mu yi da kanmu. Ta haka za mu gyaru, saboda za mu yi amfani da ma’aunanmu na kanmu wajen fitar da ra’ayi game da sarrafaffen adabin Hausa a wannan zamanin.
Ko za ka yi mana bayani game da fim din ‘Ekuestrian Elegance?’
Akwai wani yayana da ke zaune a Abuja, wanda ya labarta min sha’awarsa ta a yi fim a kan Hawan Daushe (watau hawan sarki na rana ta biyu da Sallah) na bikin Sallah na Kano, takamaimai saboda a tallata shi a kasar waje, inda yake da sana’o’insa. Ya ce ya lura babu wani cikakken fim da aka yi, ake kuma sayarwa game da Hawan Daushe. Kuma tun da ya ga ni ina mu’amala da sana’ar fim, to yana neman in yi masa fim din. Na yarda na tsara labarin. Sai na kira fim din da sunan ‘Ekuestrian Elegance – The Hawan Sallah Pageantry’ watau kasaitar Dawakai – Labarin Hawan Sallah.
Sai na tashi neman Darakta, wanda ya fi kwanta min a zuciya kuma na san zai fahimci abin da nake so shi ne Bala Anas Babinlata, domin muna da abubuwan ilimi da yawa da su ka hada mu tare. Sannan shi ba ya baragada a fina-finansa – hasali ma dai in bai yarda da labarinka ba, to ko nawa za ka ba shi ba zai yi maka daraktin ba, sai dai ka nemi wani. Na yi sa’a ya yarda da nawa labarin. Sannan ko da kayan aikin ma, ba mu yi kasa a gwiwa ba – wajen Wabes Studios a Kano muka je hayar kamarorin, wadan da ke amfani da nauyin High Definition (HD) – saboda kamar yadda na ce, duniya muke son nunawa, ba wai Kano ba.
Mataki na biyu shi ne samun albarkacin Mai Martaba, Sarkin Kano, wanda kuma muka bi ta hanyar daya daga cikin ’ya’yansa, Alhaji Amin Ado Bayero, Sarkin Dawakin Tsakar Gida, wanda shi ma ya yi sha’awar a yi fim din saboda dama can Mass Comm (aikin jarida) ya karanta, saboda haka ya san darajar adana hawan Sallah, don inganta tarihi. Mai Martaba Sarki ya karbe mu sosai, kuma a ranar da za mu je fada, Bala Anas Babinlata har doguwar riga da hula ya sa. Wannan sabanin yadda mutane suka san shi da shigar ‘kwamred’
Mai Martaba dai ya bayar da izinin mu yi fim din. Dalilan neman izinin guda biyu ne. Na farko, saboda girmamawa ga shi Mai Martaba din. Na biyu, saboda mu samu kusanci wajen daukar bidiyo din, saboda ba ma son mutane su shige gaban kyamara. Wannan ya taimaka kwarai, domin ba na jin akwai fim din Hawan Sallah da aka yi wanda kyamarar ta je dab-da-dab da Mai Martaba Sarki, sai a namu. Kuma gaskiya ma dai da sanayya, domin kusan dukkanin kansilolin sarki iyayena ne, ko kuma yayyena.
Da na tashi tsara fim din sai na wuce Hawan Daushe, na dauki duk haye-hayen na kwana biyar – watau hawan farko ana Hawan Idi, sai hawa na biyu, Hawan Daushe; sai hawa na uku, Hawan Nasarawa; sai hawa na hudu, Hawan dorayai (karamar Sallah), sai hawa na biyar, Hawan Fanisau (babbar Sallah). In ka duba za ka ga a kowacce Sallah, hawa hudu ake yi, musamman guda biyar ne in ka yi la’akari da bambanci tsakanin hawan dorayi da kuma hawan Fanisau. Dalili kuwa shi ne, wannan dama ce na a yi abin a lokacin guda.
In da aka so a samu matsala shi ne wajen mai bayar da labarin Hawan. Mun dauki wani mun je da shi sutudiyo domin a dauki muryar, kuma muka biya shi. Amma da Bala ya dada sauraron muryar da kuma yadda ya karanta labarin sai ya ce bai yi masa ba, saboda yawan tsayawa da kokarin fahimtar wadansu kalmomi da mutum yake yi. Bala ya ce sai dai a samo wani. Ana ta jimamin wa za a je a samo, sai Bala ya ce ni in yi. Da yake ba na jin dadin muryata sai na ki, amma ya nace; haka dai na hakura na yi. Dalilinsa shi ne, tunda ni na rubuta labarin, to ni zan fi iya karanta shi yadda nake so, kuma ko da gyara ne ma, zan iya yi kai tsaye a lokacin karantawar.
Saboda haka dalilan da suka sa na yi Ekuestrian Elegance, sun hada da niyyar adana wannan biki mai muhimmanci, nuna wa duniya kasaitar wannan bikin wanda babu irinsa a duk Afrikiyya (in kuma akwai, to a sanar da mu don mu je mu koyi wani abu), baiwa manazarta damar tono wadansu abubuwa game da biki, ilimintar da mutane a kan bikin da kuma tarihinsa.
Za mu ci gaba